ZABEN TUMU 3

516 124 8
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 3*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Daga karb'an sak'on gida suka nufa, umma da abban suna tamgamemen falon, umman na ansa waya

" Ke mamana dagaske?

Umma tace tana riƙe da kan tsadaddar wayar samsung, hanunta yasha k'unshi irin na larabawan nan abinka da farar mace sai ya haskata tar!

Fuska cike da murmushi tace " ah gaskiya a barni nayi karatun likita cin tunda ina so"

Ta sake murmushi irin nasu na manya tana sauraron me ake fad'a mata , murmushi da jin dadinta ya kasa gushewa, har ta ajiye wayar, ta dubi abban nasa tace " mamanka fa taci jarabawar, harda jamb, tacike buk da Abuja University, nace a kawota nan kawai"

Shima murmushin

Sanan yace mata " gwara tazo nan d'in ko zata saba da 'yan uwanta ai, amma sun kunshe min uwa a d'aka ko d'uriyarta banaji"

Shigowar su KABEER dinne ya katse musu zan cen nasu, abban ya dubesu bayan ya kurb'i hadadden shayin ganawa da umman ta natashi dashi, har yakance akwai wani sirri cikinsa.

" Har kun dawo?

Cewar abban

" Ehh Abba mundawo ga sak'on'

Affan ya mika masa wata takarda da aka sata a wata leda mai kyau, umm komi na masu hannu da shuni dabanne wato?

Bud'e takardar abban yayi yanata murmushi da alama wani abune mai muhimmanci agareshi.

Dubansu yayi ya ce " sannunku da k'okari, kuje kuci abinci ku huta, zuwa gobe ku shirya karbar wani babban nauyi,  i want to see how responsible you guys are"

Umma ta D'an tab'e Baki tace " ina responsible kuwa , ko budurwar hira babu bare matar aure"

Cikin yar dariya Abba yace " umman yara ki bari na dora musu nauyin Nan zakiga yadda boys d'ina zasu dawo, inaga applications sekin ture"

Ta hararesu tace " wand'an nan d'in? Hummm toh baride mugani, kada mu yanke musu tsammani"

Affan kunya duk ta rufeshi, shikam gogan se murmushi yakeyi, lokacin yazo ya fada cikin zuciyarsa

" Umma ki gyara zama zakisha mamaki"

Tayi galala da baki

" Ba gwara kowa da kai ba babana, kai mai shegen tsirfar tsiya, d'iyan k'awayena nawa na kawo cikin gidan nan? Daga kace wanan tayi gajera, a'a wanan siririya, waccan tayi k'iba dayawa, se waccan tacika yanga, wanan ta maka rashin kunya, wanan tanada girman kai da izza, ba ahaka aka kare ba, yarinyar nan saudat mai hankali 'yar haj uwani, ka tsefe ido kace wai mummunace, kamar ka iya halitta"

Ta k'are maganar cikin b'acin rai saboda gajiyawa da halin d'annata tilo wanda suka dauki son duniya suka d'ora masa

Abbane ya raba fadan yana tausarta, yasan halinta sarai da fushi musamman akan zancen auren kabeeru d'in, shi shaida ne na irin matsayin datake kawowa wai ya aura, amma ya ce mata ta barshi ya samo wacce yakeso, taka yi k'orafin ya d'aure masa gindi, dn wanan ba hujja bane, su ba auren had'in gida akayi musu ba, dukkansu da ita da k'anwarta su suna 'ya'yan maza su suna 'ya'yan mata shi da k'aninsa kuma sun zauna lafiya.

Yakance da ita " duniya ta canza umma yanzu ba da bane, tsirfar d'iyan zamani ta wuce tunaninki"

Hakan ne kuwa dan iyayin samari da yan matan zamani sai a hankali gurin zab'in abokin rayuwar aure, suna mance zaɓin Allah shine zaɓi, ba zaɓin kanka ba, dn d dama suna karewa cikin nadamar ZAƁEN TUMUN DARE da sukeyi, ga dai kabeeru ya dauko wata hanyar ta daban.

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now