ZABEN TUMU 18

380 69 8
                                    


ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 18*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE.

Gareki M. ALI, yaba kyauta group, Allah barmu tare. Ina cigiyar dukkan yan wattpadians, kode kuma kunajin tuƙin baba ne? Allah sa de mu sauka lafiya😁😁😁😁

Iyatu ce zaune gaban mal tana rafasa kukan baƙin ciki, ta sharce hanci tace " yoooo malam hanunka na ruɓewa ne ka yanke ka yar? Tsinuwar batada da wata fa'eeda, shiru yayi yana nazari gaskiyar iyatu ta wani gurin, tsinuwar ɗiya batada faeeda, hakuri yakamata ariƙayi da duk abinda aka haifa, wai ance ciki mai haife haife sai yasa ka haifo har ɓarawo, toh amma , shi yanaga ko bai tsinewa ramlatu ba, toh Allah ma kadai ya isa ya tsine matan tare da mummunan fushinsa gareta, ta kashe rai har lahira, ta tsaya gaban kotu idanunta cikin nasa ta masa ƙazafi, ƙungiyar karewa ɗan adam haƙƙinsa suka shiga sukayi kane kane cikin zancen, ƙawarta data biyewa ita ta zafafa abin har ƙungiyar suka shigo cikin zancen, akaci tararsa wanda tace ta yafe masa, aka ɗora diyyar man ladan bisa wuyansa, badon yan uwansa kaf sun yafe ba da ina zai shiga? , Bayan kayan abin kunya data ɗebo masa, Allah ya taimakeshi halin sa na gari ya ceceshi a idanun mutane unguwa, shiyasa ma ya kasa zaman unguwar, idan ya tuna idanun matar man ladan da tashin hankalin dayake cikinsa abin yana sanyashi yaji ya tsani kansa shi dayayi sanadiyar zuwan ramlatun duniya ma gaba ɗaya.

Yana tuna ranan da aka fito daga kotun , ta tsaya agurinsu. Idanunta cikin na ramlatun tace da ita " babu abinda zance dake sede ina rokon Allah ya miki duk abinda kika mana, duk wani ɗaci na baƙin ciki da kika ɗisa mana a makoshinmu toh Allah ya ninka miki, mun barki da fitowar rana da faɗuwarta"

Ta juya tabar gurin idanunta cike da wani abu mai bantsoro, irin abinda baka gani a idanun kowa sai idanun wanda aka zalunta, wanda akaci zarafi, wanda Allah zai gaugawar amsa musu aduoinsu ko wane iri saboda an zaluncesu zalunci mafi muni!

Juyawa tayi zatabi baban, ya dubeta

Idanunsa da wani abu wanda bata taɓa gani ba acikin idanunsa duk iya tudun laifukanta da taɓa yi a da can baya, na yau ɗin dabanne, batayi gigin ƙara cewa komi ba har saida yace mata

" Hanyar jirgi daban data mota, ramla kike ko wa? Daga rana mai kamar tayau ban sanki ba baki sanni ba, ni tawa ɗiyar ramlatu dana haifa, ta mutu agurina na bnneta"

Ya dubi iyatu yace " idan kinason aurenki toh ki wuce muje, idan kuma kin zabi waanan gawar toh ki tsaya gurinta ku je ku nemi duk inda zakuje na yafe ku"

Kuka ramla d aiyatu suka sanya, sun san ƙarshen yazo sede ko wani ikon Allah, man liman mutum ne mai magana ƙwalli daya baya canzata, musamman idan yayi dagiya acikin fushi toh fa abin baya kyau, gaba yayi ya barsu yanajin jamila tana cewa kuyi ku bar baba ransa ne a ɓace zai huce"

Yayi wani murmushin takaici, yana ayyana wa da zai iya kisa jamila zai kashe farko sanan ya haɗa da ramlatun dukka su bar duniya, dn yasan shi da iyayen yarinyar basuyi sa'ar samun ɗiaya nagari ba, dama ba yawan haihuwa ko neman haihuwa ba, aduar samun nagari ɗin tafi komi daɗi, ɗiya sukan zamo fitina ga iyayensu musamman acikin wnaan zamani da muke ciki, ya Allah ka azurtamu da haihuwar ɗiya nagari wanda zasu zamewa alummar musulmi abin alfahari ameen.

Daga nan bai ƙara sanya ramlatun a idanu ba, kai ko zancenta bai taɓayi ba sai yau da iyatu ta nace da maganar har ya zauna ya saurareta, miƙewa yayi yana ce wa " wnaan damuwarki ne zaki iya zuwa duk inda take amma ni kam namata iyaka da duk inda nake, zan baki hakkinki na uwa, amma kisani akwai iyaka"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now