MACE MUTUM WRITTERS ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 25*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Ganin wayarta da sassafe yasa jamila yin wata dariya tasan ruwa na neman ƙarewa ɗan kada ne, ta ɗaga wayar nemanta tayi da gaggawa,
Ta isa gidan tana mai jimami, jamilan ta dubeta tace " ya duk naganki a firgice ne RB"
Ta kirata da tsohon sunandata san da tayi tashensa,
Numfashi ramlat tayi tace " uhumm jamila tawa ta ƙare"
" Meya kaiki faɗan haka yar uwa"
" Ina ƙawata ɗinan matar minista da ranan kika ganmu tare?
Jammy ta gyaɗa kai tace " ehh meya sameta?
Ta ɗan muskuta tace " dama akwia wata ƙungiya damuke ciki, da bulaliyar tsumagiyar zender , bokan shi yake yi mana aiki mai kyau, yanzu kuma wai ya mutu"
Jammy ta tattara fuska tayi tsaki
" Toh meye abin damuwa"?
Sororo ramlat ɗin tayi tana duban jamila, yaya jamilar zatace meyasa zata damu? Ita kuwa ai itace me damuwa, damuwa ma kuwa ta sosai, tunda tasan nan ne kanta ya dawa
" Ke dena dmauwa akwai sabbin bokaye da suka wuce wani banza waishi zender, gasunan kala kala, zan kaiki gunsu"
Ta rungume jamilar tanaa cewa " nagode yar uwa da babu ke ya zanyi?
Jamilan tace " karki damu duk lokacin da kika shirya zan kaiki da daɗa rungumarta fuskarta cike da wani murmushi me ma'anoni iri iri....
Yayama zaayi jamila ta manta matar minista hambali, wacce akanta ramlatu ta rufe idanu tayi mata cin mutunci na ban mamaki, ta zageta da cewa ita zalamammiya ce kuma mai yi mata bakin ciki daga bata shawara, shine take so ta gwada mata bariki ba ta yara bane irinta, bariki tasu ce tsinannu wanda daman daga gida ma a tsine suka taho, ita har a gwada mata iskanci da cin amana, ita da ta kwana da mijin yayarta yamata ciki har sau biyu, ta kwana da mijin uwarta ta haife masa ɗa, ta girgiza kai tana tunanin ko ina yaran nata suke oho! Ta kwana da mazajen ƙawayenta da samarinsu bila adadin ta nemesu da bokaye da yan tsibbu kuma ta samu, kawai de ramlatu sa'a zata gwada mata a rayuwa badai iskancinda barikanci ba wnaan ƙaryanta, tayi alkawari zata yaga ramlatu irin yagawar da ɗan koyon tela ke yiwa atamfa sabuwa!( Ko wane irin yagu ne wnaan?🙄🙄🙄🙄
*************
************
Oyoyo abbana oyoyo abban yaro affan!Wani ɗan karamin yaro kyakkyawa dayake saye da fararen kaya ya nufeshi da gudu, shima da gudunsa ya taho suka haɗe sunata kyalkyale dariya, ya rungumeshi cikin jikinsa, yanajin ɗumin yaron har cikin ransa , yamajin ƙaunarsa na mamayarsa, kb yayi ittifaƙin ba zai taɓa son ɗiyansa na cikinsa dayake ta jira ba kamar yaro affan yana sonsa so mafi tsanani, yanajin yafi uwar data haifeshi sonsa, nace toh!
Ya na riƙe a hanunsa, sunata hirarsu suka shiga har gida
" Abba yaushe zamuje wonder land nida kai da ummana?
Kabeer yaja kumatun yaro affan yace " um um yarona kanason yawo dayawa fa ba last week munhe ba"
Yaro affan ya taɓe baki kamar zaiyi kuka yace " munje last week bt it was so boring ba ummana"
Kabeer ya zaro idanu " au nine boring din ko?
Yaro affan yayi saurin sanya yan hannayensa duka biyu kan kumatun kabeer ya juyo da fuskar tasa daya juyar wai shi ala dole yayi fushi ance boring
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...