MACE MUTUM WRITTERs ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 27*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Shashancin da ramlat ta sanya agaba baa cewa komi, yanzu kam tagama zama tantirayar kanta, ta tsunduma kanta cikin harkoki marasa kyau, saboda yadda samun kuɗaɗe ya ragu agun kb, sai ya zamo itakuma bazata iya rayuwa haka ba tunda na sama take hangowa bana ƙasa da ita ba tama manta talaucinsu na da tunda yanzu ko babanta ma bawani mutuncinsa take gani ba tunda bazai gaya mata abu ta ɗauka ba, ita kuwa iyatu yar abi yareema asha kiɗa ce, wanan ya sanya malam liman yin wani babban tunani game da rayuwarsa, can gida ya koma ya nemi gafarar yan uwansa da wanda suka rage masa, har ya samu kayan gadonsa yake nomarsa, ya kuma nemi aure cikin yan uwansa, mata mai hankali da addini, wata bazawa da mijinta ya mutu, ya ajiyeta nan ƙauye abinsa duk iyatu suna haukarsu suna facaka da kuɗaɗensu, sede yana tausayin kabeeru yari mai hankali da sanin ya kamata, ya shiga tarko irin nasa, duk da ramlat ɗiyarsa ce amma ya sa'lameta, yana mata adua in mai shiryuwace ta shiryu in ba haka ba Allah shi yasan yadda zaiyi da ita, yasha son sanar da kabeer abubuwan da bai sani ba game da iyalansa amma yana tsoron kada mutuncinsa ya ida zubewa a idanun kabeerun.amma ajuri zuwa rafi, wataran ko baa bakinsa ba zaijiwo shikuwa zai sanar dashi gaskiya in har ya nemi jin hakan,, wanan shine alƙawarinsa.
Wanan abubuwan data saka agaba yasa yanzu mijin ma baya gabanta sha'aninta takeyi, takoma ruwa tsundum da taimakon jamila,( wnaan fa sune ƙawayen zamani mata kuyi hattara wasu ƙawayen sun rantse se kun shiga wuta tare).
Zuwa gun boka kam yazama kamar wasan yara agunta, duk da ayar da Allah yake nuna mata akan kabeer ɗin yaƙi ya dawo tafin hanunta, amma fir taki tagani da taimakon zugar jamila.
Mal kabeeru fa ya fara raba ɗayan biyu, abubuwan da ramlat takeyi sun kai masa har wuya, yana sonta har yanzu amma halayenta da ɗabiunta sune suka fita daga kansa, wani abin mamaki shine dukkan abinda ya keson yaga mace dashi agurin maman affan yakecin karo dasu, ko da ɗin mai yasa bai gansu ba sai yanzu? Ya kasa gane wnaan sauyi dake kawo sumame a zuciyarsa, abin yana bashi tsoro, baya iya wuni fa baije ya ganta ba koda kuwa a ɓoye yakan fa ke da yaro affan amma yanzu abin yanaso yafi ƙarfin hakan soyayyar dayake yima affan din tana ƙara ƙara karuwa saboda mahaifiyarsa, ita kuwa baa magana dn ko sunanta yaji sai yayi murmushi, zuciyarsa na ɗaɗa tambayarsa wai shin menene hakan??
Yau de ya yanke hukuncin tafiya can tofa gun abokiyar hirarsa dn yaji meke faruwa da shi da kuma neman wasu shawarwari akan matarsa ya tabbata haj tofa zatayi adalci akan kowane hukunci.
Tsaraba yayi musu kamar me, baibi jirgi ba mota ya hau da kansa yana tuƙi yana nishadi, idan ya iso wasu garurwan yayi murmushi harda ƙwallah dn tuna abbansa da abbansa da ɗanuwansa, yana tuna yarintarsu da samartakarsu, abba zai sasu a mota ya tukosu har tofa yana basu labaran garuruwa, a sanadin hakan yasan su tarihin bayajidda, su sarauniya amina, da sauransu, dama haka lokaci ke shuɗewa ya tafi da duk wasu abababe da ɗan adam yayi su, seya barshi da tunani da zanen majigin duk abinda ya faru a wnana zamanin.
Gab da la'asariya mai sanyi ya isa, yaje fada yayi gaisuwa, dags nan yayi sallaah, ya shiga gida,
A dai matattarar ya iskesu, su hajiyar tofa anata cafta itada affan, umman khulsum da wata yar uwarsu lanto sunata kwasar dariya.
Ganinsa ya sanya affan kwasa da gudu yana cewa abban yaro affan oyoyo"
Shima ya rungune yaron cikin jikinsa yanajin ɗuminsa da kaunarsa suna shiga zuciyarsa , har lumshi idanu yakeyi, ya ɗaga ya daukeshi duk girmansa baya gani.
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...