MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 43*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Wanan shine karon farko da jikinta ya sanyaya takejin anya kuwa ta kyauta?
Ramlat kenan ta na zaune falo ta rafka tagumi, duk abinda takeso a duniya ta mallakeshi,. Dukiya , matsayi, mijin da takeso, irin rayuwar datake mafarki, sede batada kwanciyar hankali, ko kadan damuwa tayi mata yawa, a yau kuma take ƙarajin damuwar ta sake yi mata yawa, ganin. Fuskar kb datayi ya taɓa mata zuciya ƙwarai matuka, tanajin wata yar nadama tana taso mata.
Faɗowar jammy gidan ya sanyata dawowa daga dogon tunanen data faɗa
Ɗan dafa kafaɗarta tayi tace " lafiya kuwa?
Hmmmmmm
Taja numfashi
" Ki bari kawai jamcy yau jikina ya sanyaya danaga yadda kb ya koma"
Wata dariya jammyn ta saka, har seda ta ƙusan ƙular da ita
" Yau kece da batun imani? Lallai shiriyata Allah"
Tsuka taja tace " toh meye abun dariyar anan kike tawani ƙyaƙyatawa haka nan"
Jammy ta cigaba da dariya ciki ciki tana cewa " ai abbinne da mamaki, mu bar wanan maganar zancen filaye da gidajen nan nazo mu ƙarasa tunda naga shariar nan komi zai iya faruwa gwara ki lalabi abinda kika san zai fissheki"
Se anan ta ɗan washe, ta saki ranta suka soma zancen makudan miliyoyin kuɗaɗe, wanda jamilan ne zatayi jagaba gurin gabatar da komi....
Wai rashin sani yafi dare duhu...
Cikin ikon Allah dukkanin contact ɗinta sun dawo, ƙawayenta datayi hulda dasu a makaranta, da kuma ƙawayenta da sukayi rayuwa nan cikin kano, kamar wasa TOFA's DELIGHT yayi fice abin ya bunƙasa, ta sanya kb ya ajiye aikin dayakeyi dn abinda take samu ya wadace su bar su bayar ma, sun canzawa yaransu makaranta ma, tsananin da suka shiga ya gushe, yanzu har ma'aikatanta ta ɗiba masu mata aikace aikace, kawayenta sun taimaka ƙwarai wajen habaka abin tunda ɗiyan masu hannu da shuni ne sai ya zamo duk wani bikin bazday, ko suna ko aure ko annivasary, ko bridal shower toh kamfaninta ne zaiyi abincin nan.
Hakan yasa tayi fice, a hankali su ka sauya gidan da suke inda suka ƙawata shi, ta gyara wsni bangare dn koyarwa ga duk wsnda suke son koyan abinciccika kafin kace kwabo kusan sunfi karfin komi.
Shikam kb ya ƙara tsoron Allah akan wanda yake dashi, yau wai shine yake ci, ya ke saye da tufafi, diyansa suke ci , suke saye da tufafin da gumin matarsa kuma yar uwarsa ya samar masu, bsijin akwai mata irin su khulsum da suka rage a duniya, lallai da Allah ya barshi da zabin sa da bai san a wacce makoma yake ba ƙila da yanzu baƙin ciki ya kasheshi har an mance dashi , se Allah ya nuna yana ƙaunarsa cikin halittunsa ya rufa masa asiri ya sanyo khulsum cikin rayuwarsa, wanan kaɗai ya isheshi ishara, bashi bama ga duk wsni namiji mai canki canki akan matar aure, da mazan da matan zasu gane su nemi zaɓin Allah, da shawarar iyaye akan abokan rayuwarsu ba son zuciyarsu ba ko wani zabin nasu, duk da wasu lokutan ka kanyi zaɓin kuma ka dace in har babu son zuciyar ...
Da waɗanan tunane yake kwana yake tashi.
Hanunta riƙe da waya ta shigio tanata murna
Kansa ta faɗa ya soma cewa
" Wayyo bayin Allah kuzo zaayi mani fyaɗe"
Cikin zolaya ta dada ɗarewa kansa tana kici kicin cire masa riga kamar de wadda zatayima fyaɗen.
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...