ZAƁEN TUMU 33

263 50 4
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 33*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Ganin ɗanta ya sanya ta kwantar da hankalinta ta share komi, da matar gidan , da maigidan basu ko isheta kallo ba hakan ya ƙarawa ramlat kaimi wurin cusa kai da aiwatar da abubuwan da take so tacinma gaci.

Wasu kuɗade ne yanzu yake samu kamar babu gobe, cikkn ƙanƙanin lokaci ya sake wa matansa bakin aljihu, ya siyawa mahaifan ramlat gida acan garinsu wanda hakan burin malam dinne, tare da danƙawa masa  kudi masu yawa dn yayi jari, badon iyatu ta so ba tabar abuja, taje kuma ta gamu da tashin hankali acan garinsu, ganin wata mace harda ciki tana gab da haifeshi, ranan iyatu tayi kuka tayi hauka, man liman kuwa yace ta tafi idan taga bazata zauna ba, shi fa yanzu babu dole, kada kuma tayi zaton duk abinda ta masa a baya zata sakeyi yanzu, ya tattara kanin ramlat ya miƙashi makaranta can jihar sokoto, ba zai ƙara yarda iyatu ta lalata mata ɗiya ba sai inda ƙarfinsa ya ƙare!

" Waya take amsawa cikin taku a falon tana cewa " toh wai iyatu ke da kin ɗauka maza ba tsinannu bane?

Daga dining ta ɗago idanunta tana kallonta,

Taci gaba " harda baban fa shi ba namijin bane? Har yayi aure shekaru bamu sani ba, dana san hakane wallahi tallahi da bazan bari babban mutum ya bashi komi ba da ke aka danƙawa,"

Ta ɗanyi shiru da wayar tana furzar da numfashi mai zafi

Ko me aka ce mata daga ɗaya. Ɓangaren seta sheƙe da dariya tace

" Shima munafikin yana nan ya auro wata yar uwarsa wai kamar ki hure ta faɗi, in ba maza ba ma ko me yagani anan, ace namiji yanada kamar ni kuma wai yaje kalen mace?

Hmmmm kodayake ai wanan yar iskar kakar tashi ce ta haɗasu"

Batayi aune ba sai ganin khulsum tayi a gabanta, harsaida taji kamar ta zura da gudu duk iskancinta yarinyar ta tsoratata,

Yatsa khulsum ta nunata dashi tace

" Ke tsohuwar yar bariki idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, wallahi ki ƙare iskancinki a ko ina banda kan iyayenmu da kakanninmu in ba haka ba zakisha mamaki. Dn zama zai gagareki anan gidan"

Wani ihu ramlat ta kwalla kamar wanda aka harbeta, ta tsuguna tana cewa

" Haba khulsum kiyi hakuri mana daga tambaya seki hau min zagi da cin mutunci me namiki ne haka, naji iyayena talakawa ne amma ai na ja ragamar mutunci na, ba kwaɗayi bane ya kawoni gidan ɗan uwanki"

A hankali ya soma tattakowa, fuskarsa a murtuke, ya riƙo hanun ramlat ya na dagota

"Tashi dn Allah karki zubda darajarki a inda ba'a santa ba, sorry"

Ya soma goge mata idanu

Ta dada narkewa acikikin jikinsa, tana kukan kissa.

Khulsum ya tsurawa idanu yana nazarinta,

Khulsum tagama rainashi, kuma batajin magana, dole ya taka mata birki,

Wucewa yayi da matarsa can sashensa

Yana lallashe , zuciyarsa na Allah Allah ya sauko ya samu khulsum yayi mata cin mutunci.

A dakinta ya sameta tana bitar karatun ta na hadda dayake neman kubce mata.

A kanta ya tsaya yana cewa " ashe baki da kunya khulsum?

Yanzu ko baki gurmama ramlat a matsayin uwargida ba bazaki girmamata a matsayin wacce ta baki shekaru masu yawa ba?

ZABEN TUMUN DARETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon