ZAƁEN TUMU 16

348 69 10
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 16*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

  AURE IBADA NE

Jamsy tadubeta tace, " yo meye abin damuwa wai?

Ramlat duk. Hankalinta a tashe, ta kuma duban jamilar a karo na barka tai ,tace " meyasa hankalina ba zai tashi ba , nida mukayi rabuwar baran baram da baba, tun a kotu? Kin tuna yace na nemi wani uban? Kin tuna ban ma san inda yake ba, ban da iyatu da muke waya a ɓoye da ita? Duk kinsan da wnaan zakice kada na damu?

Guntun lemon wine ɗin dake riƙe hanun jamsy ta kurɓe, sanan ta dubeta tace " zamu samu iyaye na bogi muce sune iyayenki zmau biyasu, yaya kin gamsu da wnaan?

Wani murmushi ya kubce mata, wato jamsy ta wuce tunaninta tanada fikira ta tunani da kawo abubuwa masu kan gado, setaji bata buƙatar damuwa indai har tana tare da jamila, tayi imani itace rufin asirin rayuwarta gaba ɗaya kuma masoyiyarta ta asali..... Cikin rashin sanin masoyi kan iya komawa babban maƙiyinka na har abada! Wanda zai dauki wuƙa ya daɓa maka ta baya lokacin da ka sakankance ka miƙa masa rayuwa.

Hakan kuwa akayi jamila ta shirya komi daki daki, yadda ta tsara kuwa hakane ya tafi dallah dallah, sun samo dattijai masu ƙima maza suka gayyato ƙawayensu dn yin abincin fita kunya. Hajiyar tofa ta tura abban kano da kawun sumaila, da wasu yan uwa akaje aka kai sadaki, aka kai nagani inaso, da duk wani abinda al'ada ta tanadar, aka sanya biki bayan sallar azumi.

Zunzurutun kuɗi da aka zube musu ya tsoratasu, jamsy ta ce " mahaukaciyar banza da wanan kikeso ki mana hasara akan wani ɗan iskan ƙadangaren bariki"

Ta dakatar da ita " um um dn Allah karmuje nan gurin"

Cikin masifa tace " naji naji an taɓo ɗan gwal, mu bar wanan, yanzu hajiyar nijar zamuje gunta tamiki gyara, da ta sokoto, daganan kuma mugama da ta borno sonake mulkin the tofa's ya dawo hanunmu da gaggawa , as soon as possible"

Suka bushe da wata irin dariya da shaiɗanci!

************************************

" Yanzu de ku faɗa mana me dame kuke buƙata lubabatu"

Cewar kamis wanda shine babban abokin ango

Luba tace " kuɗin gyaran jiki mukeso, da lalle, da kuma na alibidinnkawayen amarya"

Kamis ya kwashe da dariya yace " meye kuma alibidi ni kamisu ɗan muntari"

" Au na mance kai ɗan birni ne ashe bakasan alibidi bako?

Ya girgiza kansa alamar bai sani ɗin ba

Tace " kudin entertainment na freinds"

" Au au haka nan kuke kiransa a yobe"?

Ta harareshi " ehhh meyene toh"

Ya kaɗa kai kafin yace " mu mutan zaria ba haka muke cewa ba"

Ta katseshi " banda shan fate fate me kuka iya?

Yanzu kam dariya yakeyi sosai dn yadda luba tayi maganar a ƙule

Affan ya katsesu " toh sarakunan faɗa , dn Allah ku bar faɗan nan haka, mugama abinda yake gabanmu idan nasamu aka kawomin matata saiku je kuyi ta faɗan ku dn Allah, we dont have time, bamuda lokaci"

" Toh mai mata munji"

Cewar luba.

Kamis yace " zumuɗi lale maraba ba"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now