Maza ne kimanin su ashirin, duk sanye da suits suna zaune shuru a boardroom. Jefi Jefi suna dan kuskus da juna. Can kamar after minti goma sai ji suka yi an buda kofar boardroom din. Maza ne kosassu guda biyu suka fara shigowa kamun wani namiji sanye da suit na alfarma, da gani kasan ba karamin mutum ne zai iya affording wannan kalar suit din ba, domin limited edition designer suit ne na Giorgio Armani. Tsam duka mazan nan suka miqe ganin ya shigo ana ta gaida sa, wani bature ne dan dattijo ya fara nufo sa cike da fara'a.
"Welcome sir". Ya gaida shi "I'm glad to have finally met you. I'm the new managing director of khalif constructions, the Amsterdam branch actually". Ya fadi. Murmushi kawai ya mai suka sha hannu kamun ya wuce ya zauna a kujerar sa ta alfarma, kujerar CEO. Sai da aka gama setting din smart board inda ke dakin, sannan duk mutanen da suke zama aka miqa musu wani file aka kuma umurci kowa da ya kunna computer dinsa tukun ya buda baki don yayi magana.
"Where's Al-Mubaraq?". Yayi maganar cikin wata sanyayyyar murya gami da kallon kujerar da ke facing dinsa directly, kujerar overall director din khalif airlines and group of companies. "Tariq? You heard me I believe".
"Ye.yes... yes si.. sir". P.A dinsa me ansa suna Tariq ya ansa cikin inina. "I sent an email to everyone you asked me to". Ya ansa.
"Then why is Al-Mubaraq not here?". Ya kuma tambaya amma kowa yayi shuru "Find out what's wrong". Ya umurci P.A dinsa.
"Yes sir".
"Now!". Ya kuma fadi wannan karan cikin murya me dan karfi. "Gentlemen I greet you all". Ya fadi, huskar sa a hade ba alamun dariya koh murmushi. "As you all know I meet with all managing directors of this mighty group of companies every 6 months but I had to set this meeting up 3 months to the initial time for the meeting". Ya fadi kamun ya tsaya gyaran murya sannan ya gama kallon faces din duk wanda suke gun.
"Embezzlement of this company's money has been going on and the culprit or culprits i'm sure are here amongst us. A great chunk of money has been stolen and we don't know how, when, where or by who". Ya fadi. Ji kake mutanen da ke gun suna dan kananun surutu tsakaninsu.
"How much precisely are we talking about here?". Khalid Shuraim, managing director din branch in Saudi Arabia ya tambaya.
"50,000 U.S Dollars. About 67,500,000,000 Saudi Riyals. That's 18 billion naira in Nigeria's currency". Be gama fadi ba kowa ya buda baki cikin mamaki. Hakika kudi da aka sace ba kudade bane kananu. Dole a dau mataki. A nan meeting dai ya dau zafi, kowa na presenting progress din branch inda yike, ana nuna profit and loss chart na businesses din company din. Bayan kaman awa uku, aka gama meeting.
"We all meet in 3 months time insha Allah. I'll have my P.A send the venue of the meeting to you all. Gentlemen, have a nice day". Ya miqe yayi waje, bodyguards nasa suna biye dashi a baya. Wani tsararran office ya nufa, da isowarsu kofar daya daga cikin bodyguards nasa ya buda mai kofa ya shiga su kuma suka tsaya a wajen kofar. A hankula ya dinga takawa har zuwa kujerarsa ya zauna. Sai da ya sama ýan mintoci kadan ya na dan nazari kan ya buda computer inda ke gaban sa amma duk da haka ya sama kansa da rashin concentrating akan aikin da ke gaban sa, duk tunani ne iri iri suke ta yawo a kansa. Dago kai yayi ya qura idanunsa a kan qaton enlargement inda ke ije a office dinsa. Wata ýar murmushi ya saki tare ta miqewa ya nufi inda wannan enlargement yike.
Ya dauki lokaci yana kallon hoton kan ya dan shafa Jikin hoto. "I'm the man you've always dreamt for your son to become right? Na mijin zaki, a man like you... Mohammed Mumtaz Al-Haydar". Wanda ke hoton nan dai ba kowa bane fa ce mahaifin sa wanda ya rasu kusan shekaru goma da suka wuce. Shekarar nan ta kasance me tsananin wuya a garesa kasancewar koh shekara mahaifin sa be yi ba da rasuwa ya rasa Fatima, matar sa wacca ta mutu a gun haihuwa.
Tuno wa yayi da Fatima da irin rayuwar auren da suka yi. Duk da auran su ba aure bane wanda akayi sa akan so, sun zauna cikin haquri da juna da kuma kwanciyar hankali. A lokacin da son Fatima ya fara shiga zuciyarsa, lokacin mutuwa ta raba shi da ita. Har yau ba ya iya mance randa ya rasa Fatima 8 years ago........
"Mace ce".
"Na ce maka namiji ne!".
"Mace".
"Na miji!". Ta fadi cikin bacin rai "Cikin ba a jikina yike ba. Ni nasan na miji zan haifa".
"Haba habibty.,... i'm sorry. We're having a boy insha Allah. Daina hushi". Ya rarrashe ta.
"Yawwa habibi na, ko kai fa". Ta saki wata murmushi, irin wanda ke sanyaya zuciyarsa, wanda a duk lokacin da aka basa haushi a office da ya dawo gida ya kalli wannan murmushi a huskar ta sai yaji duk wannan bacin ran nasa ya tafi. A Kullum gode wa Allah yike yi da kuma Abban sa da yayi arranging auran sa da Fatima.
"We'll name our son muhammad Fadeel insha Allah" ta katse mai tunani. Murmushi yayi ya jawo ta kusa da jikinsa.
"I thank Allah each blessed morning for making you mine". Ya fadi tare da sumbatar goshin ta.
"So now it's settled, isn't it?".
"What?".
"We're gonna have a boy and he'll be Muhammad Fadeel".
"Such a party pooper, ko Kice mun you love me too".
"Toh fa kai kace na daina karya ba kyau". Ta fadi cikin tsokana.
"Kenan baki so na?".
"Yo ehma....". Ba ta gama magana ba ta ga ya miqe cikin hushi ya wuce bedroom ya barta. Ýar dariya tayi kan ta miqe ta nufi bedroom din ita ma "Habibi" Ta kira shi cikin muryar ta me sanyi amma sai yaqi kula ta. Ta matso kusa dashi ta zauna amma sai ya share ta ya juya yayi kwanciyar sa.
"Haba habibi... qalbi na, kaima ka san duk duniya ba irin ka a gu na. Sanyin idanu na, tauraro me haske zuciya ta, abun alfahari na a ko da yaushe, uban ýaýa.....". Bata kai ga gama magana ba taji ya janyo ta jikinsa.
"You're killing me with your words" Ta ji ya fadi hawaye masu dumi suna sauko wa daga idanunsa.
"Why are you crying?".
"I've never felt love like this before. Never leave me please zahra".
"Shhh mutu ka raba nida kai insha Allah". Gyara kwanciya tayi a jikinsa suka dade a haka kan can tace mai su fita.
"Please please please let's go do some shopping and stop by the new ice cream place".
"Amma fa doctor yace ki rage shan kayan sanyi fa. Can't we just stay like this, I enjoy cuddling with you".
"Pleaseeeeeeee mana, Kaga I promised Aryaman zan siya mai birthday present kuma gobe ne. Kaima ka san I won't breathe in ban siya mai abu ba. Kaji habibi".
"Toh ya na iya dake. Ni kawai jikina yana mun wani iri ne, i'm having a bad feeling".
"Kayi ta azkhar, Allah na tare da mu insha Allah".
"Toh bara na watsa ruwa na zo". Yana shiga bandaki ita ma ta miqe ta sanja kaya zuwa wata doguwar riga mai kyau wadda tayi matukar mata kyau dama kuma gashi ciki ya an she ta. Cikin ta ya fito dan madaidaici dashi dan in mutum ya gani ma bazai taba zaton ya kai wata bakwai ba.
Shima yana fitowa ya sa ýar tshirt da wando ýar three quater suka fito yana riqe da hannunta. Sun shiga mota kenan zaya tayar da motar ta dakatar dashi.
"Me nene kuma yanzu?". Hugging dinsa kawai yaji tayi tare da fadi mai "I love you, in all situations. Come what may always know that I love you, with my whole being". Ji yayi ta kashe mai jiki da kalaman ta.
"Why is my wifey being sweet all of sudden?", ya tsokane ta kan ya yi starting mota, Idi me gadi ya buda musu kofa, nan ma kansu fita ta ce ya tsaya tana so ta dan zanta da Idi. Kwarai da gaske Fatima ta daure me kai yadda take ta abubuwa a ranar.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Hmmmmm koh me ke samun Fatima, Allah a'alam. Duk me son sani ya biyo ni a next chapter. Thanks for reading. Like I always say, bazaku taba da na sanin karanta Jirwaye ba!
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...