Babi Na Sha Hudu (14).

2.5K 264 0
                                    

Abdulmalik na juya wa ya duba amma be ga Laylah ba. Dama all through the party his eyes were on her, dan fita da yayi ya ansa call din Begum shine ya dawo be ganta ba. Duk sai yaji ba dadi, ya qosa a gama party din ya wuce ya huta.

Suna zaune da Nawfal a bayan mota driver na jan su, zasu koma gida kawai Nawfal ya fara tambayar sa.

"Khalifa you love the girl, don't you?".

"What girl?".

"Laylah".

"Nawfal so nawa zan fadi maka I don't love her, ni kawai I don't know why I feel ina da connection da ita. Ni ba kowace mace a zuciya ta in ba zahra ba".

"Hmmm khalifa kenan". Nawfal ya fadi kan ya dan yi shuru "I'm not talking about Laylah yanzu, i'm talking generally. Haka zaka mutu ba aure? Ya kamata ka gane fa zahra ta mutu, ta zama tarihi, ba zata dawo ba, it's not the end of the world. Fadeel Kuma fa? Baka tunanin yana buqatar so da kulawa na uwa".

"Duk yana samu a gun Hajjo".

"Haba khalifa, ai duk kulawan da Fadeel zai samu in ba love and care of a family wallahi it's nothing, he needs a family, he needs a mother, he needs you. Ya kamata ka sama wa yaron nan uwa, koh ita marugayiya zata so haka". Ya fadi kan yayi shuru.

Shi dai Abdulmalik bai kuma cewa komi ba, rufe idanunsa kawai yayi ya jingina kansa da headrest din kujeran motar yana ta nazari akan maganar. Imagining rayuwa yike da wata mace wadda ba zahra ba, ta ya ma zai fara. Har suka isa gida tunani yike tayi. Yana shiga gida ya wuce dakinsa straight, ya tube ya shiga wanka, a gun wankan ma tunani yayi ta yi. A karshe ya fito ya shirya cikin kayan barci ya dauko wayar sa kamar yadda ya saba. Samun kansa yayi da strolling down to sunan Laylah "Buddy" kamar yadda yayi saving number din amma to his disappointment she was offline. Ranar dai kasa barci yayi, yana ta tunani, duk abunda ya faru a gun party din ya dinga replaying a mind dinsa har zuwa maganar da suka yi da Nawfal.

Ita kam Laylah ta dade a zaune a bathroom din kan ta tashi ta cire kayan Jikin ta ta sanya rigar sanyi saboda wani irin wawan sanyi da taji na damunta. Combing hair dinta tayi kan tayi drying dinsa. Tana cikin combing hair din ne ta tuno da comb inda khalifa Al-Haydar ya bata. Miqewa tayi ta dauko ta fara taje kan dashi kawai sai ta saki wata ýar murmushi. Tuno childhood days dinta take sanda take cewa abokan wasan ta in ta girma zata yi kudi ta bar garin, dan sarki zata aura koh kuma me kudi sosai. Da ta fadi haka sai suta mata dariya ana tsokanar ta. Haka lokacin da ta fara dating Mahmoud wanda Babansa malamin boko ne, shine headmaster din primary school din garinsu, aka ta mata dariya ana tsokanarta amma ita a lokacin koh a jikinta saboda so ya riga ya gama rufe mata idanu. Dariya kawai tayi da ta tuno da abubuwan nan, gashi har yau bata yi auran ba amma kuma ga kudi masu tarin yawa ta samu. Toh me ma amfanin kudin bayan ta hanyar banza ta same su? A question she asks herself everyday.

"Khalifa Al-Haydar is my last mission". Ta qara tuna wa kanta.

Tsayawa tayi tana qarewa comb din kallo me kyau kawai sai ta fara tuno da da incidence inda suka auku a party din. Toh ta ya khalifa Al-Haydar yayi noticing dinta? Ita har ajin ta da kyaun ta ya kai ya jawo hankalinsa? Tayi ta nazari, Hakika ya saukaka mata aikin ta. Can kuma sabon abokin ta tuna, da sauri ta miqe ta dau wayarta ta fara scrolling through contacts dinta to his number. Dubawa tayi amma taga he's offline dun haka kawai ta ije wayar ta kwanta amma duk ta kasa barci. Tunanin khalifa Al-Haydar kawai take ta yi, ita dai Tabbas she has a feeling ta sansa a wani gu, Amma a ina? Kuma meyasa take jin wani abu a zuciyarta, da tana tare dashi wani dadi ta dinga ji, kamar kar su rabu.

'What's happening to me?' Ta fadi a ran ta 'first it was Abdulmalik and now khalifa Al-Haydar'.

Washe gari bata tashi da wuri ba sai can wuraren 11 ta tashi, tana tashi breakfast ta fara kan tayi wanka. Fitowan ta wanka ke da wuya sai ga daya daga cikin masu aikin gidan tazo mata da bouquet din flowers da dan note a jiki. Ije flowers din tayi bayan ta gama sunsuna su ta kuma yaba da kyaun su.

*Rise and shine, it's a new day. Don't let the sorrows of yesterday ruin the beauty of today, morning sunshine. Khalifa Al-Haydar #Xx*

Tana murmushi ta gama karanta note din, cike da mamaki. Shikenan daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaqi, Lallaima khalifa Al-Haydar. Mamaki sosai ta dinga. Tana cikin shiri taji text ya shiga wayarta, tana dubawa taga daga Abdulmalik ne.

*Lunch at 2, don't say no please*.

Murmushin ta ya qara fadada da ta gama karanta text din. Ta rasa meyasa Abdulmalik ke da irin wannan effect din on her. Kwanan nan bata da aiki wanda ya wuce na tunanin sa, yanzu kuma ga khalifa. Ita duk ta ma rasa wani irin wasa da hankali zuciyarta ke mata ba.

*Sounds fun*. Tayi typing me reply.

*perfecto! I'll pick you up. Xx*. Ya kuma turo da wani text din.

Nan da nan Laylah ta rasa zama, tunanin kayan da zata sa ta fara. A haka ta cinye time dinta tunanin what to wear har sai around 1:30pm tukun tayi making up mind dinta ta sa wani gown din atamfa me kyau sosai, ta dora wani dan blazer a sama, kan ta kuma ta rufe da dan sheilah. Tsaf ta gama shirin ta tayi kyau, bata dade da kammala shiri ba aka shigo dan fadi mata baqon ta ya iso.

Tana saukowa ta gansa yayi kyau cikin wani sweatpant da ya sa da navy blue v-neck shirt. Sajen sa ya sha gyara, koh kama baya yi da driver.

'Wannan da me kudi ne da an ga namiji me kyau'. Ta fadi a zuciyar ta. Ita ta gama yarda Abdulmalik ba wani me kudi bane saboda impression inda ya bata kenan and yanayin kayan da yike sa wa da wayar da yike riqe wa and wasu ýan abubuwa da tayi noticing ya sa ta yarda sosai da sosai shi talaka ne. Gaisawa suka yi kan suka nufi hanyar waje.

"Nidai talaka ne, bani da mota". Ya fadi yana dan sosa kansa "hope you don't mind taking a bus". Ya tambaye ta.

"It's been a while since I did that, it sounds fun". Ta fadi fuskar ta a sake. A hankula suka taka har zuwa bus station suna ta taba hira. Suna shiga bus kuwa suka sama seat daya ne kawai vacant sai yace mata ta zauna shi kuma ya kama railing din sama ya tsaya. Ita ma miqewa tayi ta tsaya dashi. Kallon ta yayi yayi mata murmushi. Fashewa da dariya sukayi sanda bus din ya dan fada porthole suka ci karo.

"kutt! Wai ke kanki sai kace kwakwa. Na Biyu kenan muke cin karo". Ya fadi suka fashe da dariya. Fito da sleek iPhone 7 dinta tayi ta fara daukan su hoto. Suna ta making funny faces suna dariya abunsu. A haka har suka isa park inda suka fara haduwa bayan isowarsu Australia. Eatery din cikin park din suka shiga suka zauna aka kawo masu menu suka yi placing order. Cin abincin suke suna dan taba hira.

Laylah ta sha mamaki yadda taga yana cin abinci cikin nutsuwa, with poise and class. A gaskia da ace bata san sa ba da bazata taba yarda shi ba mai kudi bane, he's too good to be a driver.

"So, naga you look educated amma kuma kake aikin driving".

Sai da ya kurbi ruwa kan ya bata ansa "I have a degree in Software engineering". Ya fadi ba tare da fadi mata har masters garesa da PhD.

"Forreal! Shine kake aikin driving".

"Toh ya muka iya, rashin aikin yi a qasar mu". Ya fadi mata "ke fah? You look rich, or should I say you're wealthy, da an ganki an ga ýar gidan naira".

Dariya tayi kan ta basa ansa "Ni ba ýar kowa bace. I paved way for myself. I have a degree in business administration, last 2 years kuma nayi wani special course in events planning and management. I'm an events planner".

"Ohhh you told me, Amma what business proposal do you have for Mr Al-Haydar if I may ask". Ya tambaya. Rasa abun cewa tayi kawai dai ta kirkiro tarin karya kamar ta kware. Sai da ta gama tarin ta basa ansa. Lokacin ta samo karyar da zata mai.

"He's a business man, so na ke yayi signing agency dina, mu dinga mai planning events a duk lokacin da yike da sha'ani koh wani abu". Kai ya gyada mata alamun ya gane suka cigaba da cin abinci.

"Ya ban ganka ba a dinner din jiya?".

"Ni a wa? Ina ni ina zuwa taron manyan mutane". Ya fadi cikin dariya. Daga nan shuru suka yi suka cigaba da cin abincin su.

"Yawwa! Please waye Al-Mubaraq Bala a gun khalifa Al-Haydar, what's the relationship between them". Ta tambaya.

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Toh toh toh..... things are slowly progressing. Mun kusa komawa Nigeria very soon and the real fun begins there💃💃💃 keep reading jirwaye. Xx

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now