Sai da tazo fita da nufi zuwa sightseeing tukun ta tuno da ipad dinta. Nema take ta yi cikin kaya kan can after some minutes ta tuna ai ta mance sa a jirgi.
"Damn!" Ta fadi gami da jan ýar tsaki dun takaici. Akwai abubuwa da yawa masu muhimmanci a gun ta da suke cikin wannan ipad din. Cigaba da shirin ta tayi ta saka wata jacket baqa me kyau da wando wanda ya dan matse ta sannan ta sa wasu boots masu kyau, ta dauko dan karamin veil baqi ta rufe baqin gashin ta wanda sai kyalli yike ta yi saboda tsananin kula da kashe kudi da ake yi a kan shi.
Waya ta dauka ta kirawo Simon dun yazo ya kai ta ganin gari tunda dama shine driver dinta wanda zai dinga tuqa ta iya zaman ta a Australia wanda be wuci na 2 weeks ba. Baa yi 15 minutes ba ya kira ta cewa ya iso harabar hotel din. Ta katse wayar ta saka a cikin wata ýar suspender tare da wallet dinta da sauran necessities dinta sannan ta jawo babban box inda tazo dashi saboda daga ganin gari ba zata dawo hotel ba. Special guest house din Senator zaa kai ta. Tana gamawa ta dan fesa turare sannan ta fita tana taku a tsanake kamar me tausayin qasa.
Mr Yates na hango ta ya nufo ya ansa box din ya cigaba da ja har zuwa inda yayi parking mota.wata mota ce hadaddiya, ta taka wadda ya dauko ta daga airport dashi.
'Lallaima, senator babban mutum ne. Na ko yi babban kamu' ta fadi a cikin zuciyar ta gami da sakin wata ýar murmushi a fili.
Laylah dai ýar budurwa ce me tashe, wadda bata wuci shekara 24 ba da haihuwa. Tsayawa kwantata irin kyau da figure inda Allah ya mata bata lokaci ne, ga muryar ta wata sanyayyya da ita, irin muryar nan me sa me gida lattin office, ga manya idanu Masha Allah. Gashi kam har gadon baya, ga skin din ta irin wanda bature kan kira flawless, ba spot koh daya gashi da laushin tsiya wane fur din mage, tana da dan haske iya gwargwado ga farin jini a gun samari. Laylah dai kawai full package ce. Karya ne namiji ya mata kallo daya ya wuce, sai ya dago ya kuma kallon ta.
Shiga motar tayi ta zauna shuru a gidan baya shi kuma Mr Yates ya zauna a seat din driver ya fara jan mota. "should we start with the museum?".
"No, take me to a park". Ta fadi.
Cikin dan qanqanin lokaci suka isa wani qayataccen park wanda yike cike tam da mutane, ga yara suna ta wasa da guje guje. Masu sai da snacks da ice cream duk gasu nan ana ta musu ciniki, harta masu sai da abinci ma duk gasu nan. A hankula take tafiya tana wasa da wani dan fure da ta tsinka. Wasu tsoffi biyu ta hango, turawa ne su kuma daga ganin su mata da miji ne. Zaune suke a wani carpet mijin na ba matar abinci a baki ita kuma tana ansa. Jin wani abu tayi a zuciyan ta kallon wannan tsoffi guda biyu, gasu dai sun tsufa tukub amma basu daina so da kula da junan su ba. Ta dade tana kallon su cike da shaawar rayuwar su.
"I wish". Ta fadi gami da dan lumshe ido kan ta cigaba da tafia tana tunanin koh zata taba iya samun masoyi wanda zai so ta, yayi accepting dinta a yadda take har suyi aure su tsufa tare. Tana gaba kuma kadan, wasu couples ta hango da dan su wanda bazai wuci shekara daya da ýan watanni ba. Tafia suke riqe da hannun juna, sun sa dan yaron a tsakiyarsu. Can sai yaron ya balle ya rugo da gudu iyayen na biye dashi suna dariya, shima yaron dariya yike. Kawai bata ankara ba taji an auko mata, an riqe kafafun ta. Dan yaron nan ne da ke gudu.
"What's your name?". Cike da murmushi ta miqa mai hannayen ta biyu ta dago sa zuwa jikinta.
"Bubble" ya fadi yana dariya ita kuma sai wasa take da gashin sa mai laushi.
"Your name is bubble?". Ta tambaya tana dariya.
"Bubble!" Ya kuma maimaitawa. Kan ta buda baki tayi magana taji muryan maman yaron ta katse su.
"Owen! You naughty kid". Yana juyo wa ya kalli mamansa ya fashe da dariya. Ita kuma Laylah ganin mahaifiyar sa ta miqa mata danta. Cikin fara'a ta anshe sa.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...