Immediately yana sauke Laylah be tsaya koh ina ba sai gidan newspaper inda suka publishing the story about Laylah. Da saurin sa ya shiga rai a bace ya dinga tambayar a nuna masa who the journalist that published the article was.
"Labaran Mustapha?". Ya kira sunan.
"Yes" wani mutum dan dogo, da ka gansa ka ga bafulatani ya ansa "How may I he.....". Be qarasa maganar ba khalifa ya kai masa nushi a hanci.
"Waye kai?" Ya tambaya tare da kai masa wanin nushin "Who do you think you are to publish such article about my wife?". Ya kuma kai masa wani punch "Tell me who are you?". Khalifa pounced on the poor man like an injured lion. Haka yayi ta kai masa nushi har sai da hancin sa ya fara fidda jini, ya kai qasa amma still khalifa be rabu dashi ba ya bisa ya cigaba da kai masa duka. Da kyar security din publishing house din suka zo suka janye khalifa daga kan mutumin suka yi waje dashi. Manager din publishing house din har mota ya bi khalifa yana ba da haquri amma koh sauraron sa khalifan be yi ba ya ja mota ya wuce after threatening to close down the publishing house.
Straight be tsaya koh ina ba sai gida, ya wuce side dinsa ya fada bathroom. Shower ya shiga ya kunna ruwa ya tsaya motionless under the cold water. Zuciyar sa har zuwa lokacin be bar tafarfasa ba. Ya dan jima a bandaki kan ya fito ya sa kaya. Ya gama shiri kenan ya sauko qasa da niyyar shan iska a garden to help relive him of the stress he was going through sai ga Nawfal ya shigo gidan da wani uban speed. Koh tsayawa rufe qofar motar be yi ba ya shiga cikin gidan da hanzari yana kwalawa khalifa kira.
"Can you explain what this was?". Ya fadi rai a bace yana shoving wayar sa to Khalifa's face.
"It's a video of me punching that stupid journalist". Ya bashi ansa kamar it wasn't a big deal.
"God! Khalifa ka fara hauka ne? Ever since Laylah got back into your life you've been acting so irrational. So hauka ne?". Ya tambaya "You're on the edge of losing your sanity over a lady".
"You'll talk about my wife with respect". Khalifa yayi masa warning.
"What respect has a whore?". Nawfal ya fadi cikin bacin rai sai dai gama furucin sa ke da wuya khalifa ya kai masa wani mugun punch a face.
"You'll learn to talk about her with respect saboda wallahi dan ita ba abunda bazan yi ba, koh da kuwa dukan ka ne or throwing you to bars". Ya fadi kan ya juya ya wuce dakinsa ya dau key din motar sa ya fita not minding at all to pick his phones. Yana fita shima Nawfal cikin bacin rai ya juya ya fita zuwa inda ya bar motar sa ya shiga and drove straight to the hospital. Shikam khalifa tuqi yike ba dun ya san Inda yike son zuwa ba. Ya dade yana tuqi kan yayi parking da ya kai wajen gari. Ya dade zaune kan motar sa ba irin tunanin baya yi kan daga baya ya koma cikin mota ya fara tuqi.
The next morning Kiran Begum ne cewar tana son ganinsa ya tashe sa daga barci. Wanka kawai yayi ya shirya ba tare da yaci abinci ba ya wuce hospital din. Koh da ya isa a lokacin Al-Mubaraq yazo duba jikinta dan haka a corridor din ward din ya zauna shuru yana jiran fitowan Al-Mubaraq din kan ya shiga. Yana cikin wannan zaman ne Nawfal yazo, kallon juna kawai suka yi ba wanda yace komi. Khalifa ne ya fara dauke ido shikuma Nawfal ya wuce ya shiga room din. After about 30 minutes, Al-Mubaraq ya fito with Nawfal behind him. Dan gaisuwa suka yi sama sama kan Al-Mubaraq din ya wuce stating that he had a conference to attend in Calabar that morning dan haka private jet na nan na jiran sa. Har qasa Nawfal ya tafi raka sa shi kuma khalifa yayi ceasing opportunity din ya shiga room din Begum after saying a silent prayer. Koh da ya shiga tsayawa yayi shuru yana kallon mahaifiyar sa wadda kamar Kullum idanunta na kan newspaper except that at that time she wasn't on the hospital bed anymore, zaune take a balcony din room din, in a comfortable chair which gave her maximum support, ga bisa dukkan alamu she had just finished breakfast kenan.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...