A haka barci ya kwashe Laylah. Jin shuru ya sa Yasmeenah bin sahun ta, ta san a duk lokacin da Laylah ke da meeting da client tana zuwa gun ta shiri amma kuma sai wannan karan taga sabanin haka so sai kawai ta bi. Tana isa ta izza Laylah ta ci kuka har barci ya kwashe ta a qasa.
"Hey baby, wake up. It's past 3 already". Ta fadi tana shafa mata lallausar gashin ta. A hankula Laylah ta buda ido ta dan wa Yasmeenah murmushi. Ce mata taje tayi sallah Yasmeenah tayi sannan in ta gama ta same ta a dakin ta. Hakan aka yi. Tana idda sallah ta wuce daki ta sama Yasmeenah na ta hada ruwan wanka. Dago kai tayi ta ga Laylah ta zauna shuru ta qura wa hotunan da ke bangon dakin kallo, hotunan Yasmeenah ne da leek, tun tana karama har zuwa girman ta. Wani hoton kuma na leek ne da yaran ta. Murmushi Yasmeenah tayi kan tayi magana
"Special gyara zan miki yau, irin namu na ýan Borno". (Shout out all my Borno folks🙌🙌).
Dariya kawai Laylah tayi bata ce komi ba, hankalinta na kan hotunan. "Yasmeenah". Ta kirata a hankula.
"Yes love".
"I've known you for about 10 years now, amma koh so daya ban taba jin kin ambaci gida ba. You hardly talk about your relatives, all I know is ke shuwa ce from Borno nothing more, nothing.......".
Bata gama magana ba Yasmeenah ta katse ta "Time for your bath, the water's ready". Ta fadi tana jan hanci alaman tana riqe hawaye. Laylah bata kuma pressing issue dinba ta tube shuru ta shiga qaton bathroom din ta zauna cikin bathtub wanda cike yike da ruwan turaren which was made out of sandalwood da jasmine flower. A haka ta zauna shuru ba mai cewa kowa komi, Yasmeenah ta dauko wani scented shampoo din ta wanke mata kai kan ta fito after spending about 30 minutes a bathtub din. Towel ta daura sannan ta daura wani karami a ka sannan ta fito ta zauna shuru a bakin gado. Yasmeenah ta fito ta kawo mata turaruka wanda zata bi jikinta dasu, dakin duk ya dau kanshi. Sai da ta gama shafa jiki kan ta koma vanity table, Yasmeenah ta zo da hair dryer zata busar da gashin ta.
"I've never come across a lady as pretty and graceful as you are". Yasmeenah ta fadi a hankula.
"Come on, duk da tsufar ki kin fa fi ni kyau. Kinga yadda maza ke kallon ki in muka fita kuwa". Laylah ta ansa ta.
Sai da tayi dariya sosai kan ta buda baki tayi magana "I'm made for just one man". Ta fadi kan ta tsaya ta goge hawaye. "Dazu you were asking about relatives, ina da ýan uwa amma almost 40 years kenan rabona dasu, rabona da gida since I was 15". Ta fadi wa Laylah wadda ta zare ido cike da mamaki.
"Baki taba missing dinsu ba?".
"I have, always. Da su nike kwana ba tashi a raina". Shuru Laylah tayi cike da mamaki, Tabbas Yasmeenah ta dade tana kunshe da bakin ciki a ran ta wanda ta qi fitowa ta fadi wa kowa. Duk kusancin ta da Laylah ba sa ta taba opening up to her ba.
"As for Leek..... I swear Laylah she has a father. Me rufin asiri, dan gidan kirki". Ta fadi mata.
"Toh ki fadi mata shi mana".
"Ban san Inda zan nemo shi ba Laylah, be taba damuwa da mu ba. Ban tunanin zai iya tunawa da ni bare wata diyar sa". Ta fadi hawaye suka kufce mata.
"Ba so na yike ba bare ita, gudan jinin sa. For 35 years I've been preserving myself for him, koh so daya ban taba siyar da jikina ba, I know that doesn't make me a saint amma you can bear me witness Laylah, bana abunda ya wuce hada ýan mata da maza masu kudi. Leek kam iya gwargwado na bata tarbiyya, ban bari ta baci ba. Na mata aure.....". Ta fadi tana ta kuka. Laylah ta juyo tana ta bata haquri. Sai da hawayen suka tsaya sannan ta cigaba da drying ma Laylah hair dinta.
"And I'm happy for you, zaki bar wannan rayuwar. You'll start a new life. I'm very proud of you Laylah, ba kowa ce mace zata iya sacrificing abunda kika yi sacrificing ba, you're a lady like no other. May you be happy always.". Laylah ita ma kuka mara sound ta fara.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...