Fatan alkhairi gareku fans din Jirwaye...... naga messages dinku na gaisuwa da fatan alkhairi. Godia nike sosai da sosai, Allah ya bar zumunci
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
A haka suka fara kokawa, uncle Mukhtar na kokarin cin ma burinsa a kan ta ita kuma tana kokarin kwato kanta. Gashi ba abun ta saki ihu ba, ya toshe bakin ta. Cikin wannan halin ba wanda a cikin su ya ankara da shigowar motar auntie Sarah gidan ba sai da suka ji motsi, alamar ana kokarin buda lock din dakin. Nan uban gumi ya fara keto wa uncle Mukhtar, Tabbas yau dubun sa ta cika. In Sarah ta kama sa kashin sa ya bushe, wa zai dinga nemo mai projects kuma dun dama duk projects in da ake kawo masa dan uwan ta ne ke masa hanya.
Nan da nan basira tazo mai, ya buda button nasa biyu ya fada kan gado kan ya jayo ta ta fado saman sa.
"Dan Allah kiyi haquri ki rabu dani. Bazan iya yaudarar mata na ba, in ba ke ba Badejo wani irin kyautatawa ne Sarah bata miki.......". Ya dinga fadi a lokacin da auntie Sarah ta shigo dakin.
"Me zan gani haka". Ta fadi tana sakin wayoyin da ke hannunta da key din motar ta a qasa. Cikin hanzari Badejo ta sauko jikinsa ta dau kallabinta wanda tuni ya fadi qasa. Qasa kawai tayi ta fara rokon auntie Sarah.
"Wallahi auntie ba haka bane..... Un.....unc....uncle ne.....". Bata gama magana ba auntie Sarah ta matso kusa ta cakumo ta ta fara jan ta waje, suna isa gun da daya daga cikin masu aikin gidan ke gugan uniforms din yara auntie ta tsaya.
"Sai kin ci uban ki yau wallahi". Ta fadi kan ta kwata iron din me zafi daga hannun me gugan zata na na wa Badejo a fuska.
"Auntie dan Allah kiyi haquri, wallahi uncle shi yace naje na gyara mai daki". Ta fadi cikin hawaye.
"Shine kika ce bari kiyi using opportunity ki mun seducing miji koh, wallahi sai kin ci na jaki yau". Auntie Sarah ta fadi tana kai wa fuskar Badejo hari da iron din ita kuma ta kauce da sauri ta hanyar duqawa sai saukar iron din ta ji a bayan ta ta saki wata ihu me karfi.
"Ai Allah yau sai nayi disfiguring wannan fuskar da kike alfahari da ita, har kike ganin zaki iya kwace mun miji. Kai Musa qara zafin iron din". Ta fadi cikin zafin rai. Ta daga hannu zata kuma sakin wa Badejo iron din a jiki wani namiji ya zo ya riqe ta gam.
"Sarah! What's this? Me ya faru". Ya tambaya.
"Nawfal ka rabu dani, yau sai na kassara yarinyar nan. Ta rasa wanda zata bi sai mijina". Ta fadi tana fisge kan ta amma ina dan uwan ta ya mata riqo sosai ta kasa kwance kanta daga riqon. Da kyar ya shawo kanta ta ije iron din suka fara tafia, Badejo kam na gun tana ta faman shara kuka, ga zafin qazafin da aka mata ga zafin qunar da tayi. Koh bakin door din barin dakin basu isa ba auntie Sarah ta saki wata ýar ihu, water dinta yayi breaking. Nan da nan Nawfal ya dago ta yana kwala kiran uncle Mukhtar ya fito. Cikin hanzari aka wuce da ita asibiti.
Ita kam Badejo na isa quaters dinsu ta fada Jikin zainaba tana kuka tana fadi mata duk abunda ya faru. Zainaba ta rungumo kawarta suka ta kuka tare, sai da suka yi kukan ta ishe su kan zainaba ta miqe da niyyar dressing ma Badejo burn dinta. Auntie Sarah kam tunda aka wuce da ita hospital sai bayan 2 days suka dawo gida ta haifi danta santalele, Aikam a ranar da ta dawo Badejo bata qara koh da 30 minutes ba a gidan.
Tana shiga ta izza ta kitchen ta jawo ta waje a wulakance tace wa wata mai aikin gida ta je ta kwaso mata kayanta ta bar gidan. Masu aiki ne sun kai su biyar suka taru ana ta ba auntie Sarah haquri, at least ta bari kashe gari da safe, yanzu ina zata cikin dare haka, an riga da anyi sallah isha'i. Sam auntie Sarah tayi kememe kan cewa Badejo baza ta kuma kwana mata a gida ba dan haka tayi mata watsi da kaya a waje tare da kudi naira dari biyu wai tayi kudin mota dashi zuwa yola dun mugunta da rashin imani. A ina dari biyu zata ishi mutum kudin mota daga Abuja har zuwa yola.
ESTÁS LEYENDO
JIRWAYE✔
Ficción GeneralKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...