Babi Na Takwas (08).

3K 314 6
                                    

Kullum ina receiving encouraging messages din readers, wallah ban taba tunanin Jirwaye zai sama irin wannan karbuwan ba. Godia lodi lodi. Masu cewa na qara tsawon chapters dina naji kuma na gode for the suggestion. I'll try and and do that gradually. Rn i'm so choked up ne wallah, writing 3 novels at the same time, coping with school apart nd assignments ga rashin iya hausa sosai amma gradually insha Allah zaku ga change. Haphsertuh appreciates y'all💖

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

wani irin tsaki na takaici ta ja sannan ta cigaba da durza lallausar fatar ta da soson da ke hannun ta. Durza take kamar zata daye fatar ta amma bata daina ba har sai da taga fatar ta yi jazur kuma yana mata zafi. Kuka sosai ta fara saboda tsananin takaici da ya ishe ta, duk yadda tayi kokarin ta goge, ta sama kanta da rasa iya goge jirwayen dake manne da jikinta.

'Stop fussing about it Laylah, the stain is here to stay' wani zuciya ya fadi mata.

Kuka take yi irin me ratsa zuciya tana zaune a cikin jacuzzi bathtub wanda ke cike da ruwan kumfa. Kullum ta tashi da safe bayan biyan buqatar customer dinta sai taji zafi a cikin ran ta, sai taji ta tsani kanta, ta tsani rayuwar ta, ta tsani randa ta taka qafa zuwa birnin tarayya. Ta dade tana tunani kan ta qarasa wankar ta, tayi drying jikinta ta fito out of the bathroom. Senator Junaidu ya riga ya koma Nigeria bayan rubuta mata cheque just as he promised amma kuma ya umurce masu aikin gidan da suta mata hidima, duk abunda take so a mata har randa zata bar Australia.

Tana fitowa tayi salatul nawafil kan ta shirya ta sa wani sweatpant da kuma wani shirt wanda was very loose a jikinta. Kasancewar ranar Sunday yasa tayi deciding zata zauna indoors. Har ta dauko wani novel din Dan Brown ta fara karantawa sai daya daga cikin masu aikin gidan suka shigo kiranta.

"There's someone here to see you ma'am".

"A male or female?" Ta fara tambaya.

"It's a male, he says he came to return your ipad".

"Oh that arse hole, i'll be out in a sec". Sai da ta dan bata lokaci kan ta tashi ta dauki sheilah ta rufe kanta sannan ta fita. A gazebo ta izza shi yana zaune, da cup din orange juice a hannu.

"Don't tell me you're planning on spilling that on me". Ta katse mai tunani.

"Wa alaikum Salam, good day to you too lady, i'm very much good thanks for asking and yes, I'm not spilling the juice on you". ya fadi cikin sarcasm.

Dariya kawai tayi 'such a sarcastic guy' ta fadi a zuciya amma a fili sai cewa tayi "Pardon my manners. Salaam alaika". Ansawa yayi ba tare da ya kalli face dinta ba, dan Jim kadan ya miqa mata ipad dinta ya tashi ya mata sallama.

"Fi waqt akhar". Har ya miqe zai wuce ta dakatar dashi

"Wait please". Sai da ta bari ya juyo tukun ta tambaya sunansa "I'm Laylah and you?".

Sai da ya dan yi nazari kadan kan ya ansa ta "I'm Abdul.... Abdulmalik".

"Nice meeting you Abdulmalik".

"The feeling is mutual". Ya fadi ya wuce ita kuma bata miqe ba daga inda take zaune. Zaune take tana kallonsa as figure dinsa yike ta retreating out of Jk guesthouse. Dogo ne, yana da body build me kyau, like very exceptional. Kana ganin sa ka san it took him lots of hard work to attain that kind of body.

'Just like a Greek god.... hmmm' Ta fadi a zuciyar ta. Gashi nan ba fari ba, Amma dai yana da dan haske. Ga saje me kyau da yike dashi a face dinsa da gashin sa wanda is ebony black and silky. Gashi dai kamar Nigerian, kamar kuma ba Nigerian ba. Babban abunda ya ma fi daure mata kai shine ga English accent dinsa is flawless, in yana yi kamar bature. Ga kuma skin dinsa da ka gani kaga hutu amma kuma yanayin shigar sa bata yi kama da na mai kudi ba kwata kwata kuma gashin nan ga dukkan alamu ba da mota yazo ba. Tashi tayi ta wuce cikin gidan amma sai dai tana ta jin wani abu a zuciyar ta wanda ta kasa ganewa gaba daya. Wannan stranger din, Abdulmalik, bata san meyasa ba amma taji tana so ta kuma haduwa dashi. He seemed like a nice person to her.

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now