Babi Na Ashirin Da Uku (23).

2.5K 284 2
                                    

Kamar yadda yayi alkwari, da yamma da Mahmoud zai wuce gida sai da ya biya ta gidan su Badejo ya kai mata movie inda yace zai kai mata da kuma ýan kayan kwalama. Nan ma suka kuma taba dan hira kan ya mata sai da safe ya wuce. Rashin wuta ya hana Badejo kallon film din dun haka Washe gari ana tashi makaranta bata tsaya tsokana da iya shege ta jawo hannun Auta suka kama hanyar gida. A hanya ne suka ga wani dan dattijo da gemu suka ta mai dariya wai gemun sa kamar na bunsuru.

Suna cikin dariya Auta ta tambayi yayarta "Amma Adda".

"Na'am ya aka yi?".

"Yanzu ace ke ce da wannan gemun" ta fadi ta tuntsure da dariya "me zana dinga ce miki".

Sai da Badejo ta jima gun tunani kan ta bata answer "Sai ki kirani Hamma Bunsuru". Ta fadi suka tuntsure da dariya "Amma kuma Auta, da ace kina da bindi irin na saniyar Malam Jauro fa?".

Auta bata gama tunani ba Badejo ta bata ansa "Da na kiraki Auta Saniya". Auta kam ta sha kunu, ta hade rai wai ita bazata yarda ba. Nan fa ta kama bin yayar nata da gudu, suna gudu cikin gari suna dariya, basu da matsala a rayuwar su. Irin so da shaquwar da ke tsakanin Badejo da Auta har daure kan mutane yike atimes, gasu dai zaka ga daya ta girmi daya da dan ne sa amma kuma a kaf kauyen Badejo bata da wata qawa, ýar uwar shawara wadda ta wuce ýar Uwar ta. Yadda kasan a manne aka haife su dan koh aike tare suke zuwa, duk wanda kam ya taba ta sai ya gamu da bacin ran ýar Uwar ta dun koh a makaranta ne in zaa hukunta Auta dun ta yi wani laifi Badejo ke Karbar hukuncin indai tana kusa. Indai har Auta ta nuna tana son abu, Badejo na kokarin ganin ta ne ma mata shi, bata son ganin ýar Uwar nata cikin bakin ciki kwata kwata. Gashi ita kuma Auta karamar yarinya ce wadda bata san babu ba, ita kawai a duk lokacin da ta so abu a bata shi. Alhamdulillah dai mahaifin su iya gwargwado yana da na rufin asiri kuma irin tsananin son da yike wa yaransa, duk abunda suka nema gunsa yana kokarin yaga ya basu. Inda malam Barkindo suka sha bamban kenan da Uwar dakinsa Rabi, shi mutum ne shuru shuru mara hayaniya, magana ma be cika son yi ba, ita kam Rabi irin matan nan ne masu jaraba, sha yanzu magani yanzu, kwata kwata bata son rainin hankali. Dalilin haka ne yasa yaran duk suka fi kusanci da mahaifin su wanda shi a Kullum yike lallaba su yana bin su a hankula koh da laifi suka yi dun shi a nasa tunanin duka baya gyara yaro, wai! Banda Uwar gida Rabi ita da yaro yayi laifi muciya ne, tabarya, icce koh duk abunda hannunta ya fada zata dauka tayi ta rafkan yaro dashi har sai maqota sun kawo ceto. 

Basu bar gudu ba sai da suka sha kwanan layin su sannan. Sanin halin mahaifiyar su ma ya tsagaitar da gudun nasu. Suka shiga suna wakar ayye mama, ayye mama. Suna shiga suka sama iyayen su zaune kan tabarma.

"Sannunku da gida". Suka gaisar da iyayen su. Rabi ce kawai ta dago ta ansa, bata bar fifitan da take wa babansu ba, ga kwanon hura gabansa koh tabawa be yi ba. Ita dai Badejo cike da mamaki, Meya dawo da Abban su gida da wuri haka yau, shi da sai bayan sallan asr yike dawowa gida. Ita kam Auta ba ruwanta, ta kutsa Jikin Babanta ta jawo kwanon huran ta fara kai hari, Rabi zata hanata yace ba komi a bar mata ta sha.

"Abba ka dawo da wuri yau". Badejo ta tambaya. Murmushi kawai yayi ya Kalle ta ya ce ta matso ta zauna kusa dashi.

"Mamana ban jin dadi ne sosai yau dinnan". Koh malam Barkindo be fadi ba da ka gani zaka san cewa a cikin yaransa Badejo ce favourite dinsa dan koh kadan be cika son ganin Rabi na hukunta ta ba in tayi ba daidai ba. Har zuwa yamma malam Barkindo na zaune da ýan matansa biyu suna ta mai hira har zuwa lokacin da aka gama abincin dare, dama al'adar su ce cin abinci gu daya dun haka Rabi ta kawo abincin inda suke a tsakar gida kan ta shiga ta kirawo Suraj.

Suna cikin cin abinci ne Badejo ta lura Babansu baya wani cin kirki. "Abba baka ci". Ta fadi rai a hade.

"Bani da appetite ne mamana". Yayi mata murmushi.

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now