JIRWAYE......... The Stained Veil!
An Engausa Story By Haphsertuh
Babi Na Talatin Da Biyu.
Wata ranar Saturday, ta shirya da niyyar zuwa Islamic foundation inda tayi enrolling kanta. Dama bata taba zuwa ba. Tsaf ta gama shiri at around 10 am, ta sa wata black abaya, veil din kanta shima black. From head to toe dai black ta sa kan ta dau suspender dinta da dark shades ta wuce. Mota ta shiga masu aiki nata gaisuwa. Tana fita gate din mansion dinsu bata tsaya ko ina ba sai Al-Ikhlaas Islamic foundation. Sai da ta ja dogon numfashi kan ta shiga ta izza about 7 women already waiting for counsellor din ta shigo. Cikin matan da ta izza kam har da zainaba zaune da qaton cikin ta kamar kwarya.
Cike da fara'a ta matsa kusa tana miqawa ko waccen su hannu ana gaisawa suna welcoming dinta to counselling sessions din amma da ta miqawa zainaba hannu sai tayi kamar bata ganta ba dun haka ta gaidata amma shuru kamar ba da ita ba. Hakan ya sa Laylah kiran sunanta dun ta san da ita ake.
"Zainaba ina kwana".
"Uhmmm". Kawai ta ce abun ya daure wa Laylah kai. Rana daya ta sanja mata. Koh hushi take cewa bata neme ta ba bayan sun rabu. Anyways ta kawar da wannan tunanin ta sama wuri ta zauna. Haka mata suka ta zuwa. All in all su 15 ne a class din sai counsellor dinsu, making them 15. Tana isowa kam aka fara tattaunawa akan topic dinsu na ranar which was; *Betrayal* wato *Cin amana*. Kowa cikinsu na kawo experience dinsa.
"Malama ke fa?". Aka tambaya Laylah koh ta taba experiencing betrayal. Immediately mind dinta yayi flying to khalifa Al-Haydar amma kuma what was the use of her narrating the story to them kuma koh ta basu labari karyata ta zaa yi dun khalifa Al-Haydar ba karamin mutum bane dun haka ta gyada kanta alamar aah.
"Nikam I just remembered wani mugun cin amana da na taba witnessing". Koh bata juya ba, ta san muryar wanda ke magana.
"About 10 years ago, lokacin ina kauye mahaifin mu ya mutu. Saboda wahala da rayuwa ya mana, aka tura ni Abuja aikin gidan wata mata. Da naje na fara aiki sha tara na arziki ana mun a gidan, har makaranta suka maida ni. Saboda tsananin karamci na roqa aka dau qawata aiki a gidan amma tsananin butulci irin na dan Adam, tazo ta ci amananmu; ni wadda na kawo ta da auntie wadda ta riqe mu tamkar kannen ta". Ta dan tsaya tana duba fuskar Laylah for an expression amma sai taga face dinta was expressionless, there was neither happiness nor grief written on it. Koh alamar tension babu fuskar ta sai ma wata ýar murmushi da take yi.
"Toh ita kam wannan qawa ta ki me tayi ne".
"Wataran auntie ta fita ta dawo ta kamata a gado da mijinta. Tayi seducing dinsa to bed saboda abun duniya". Ta cigaba da basu labari wanda duk karya ne ya fi yawa a ciki su kam mata sai tir suke da halin wannan yarinyar without them knowing koh wacece, basu san cewa tana zaune cikinsu ba.
"Amma wannan yarinyar Allah ya tsine mata".
"Matsiyaciya ce". Fadin wata.
"Dama shi talaka be iya cin arziki ba".
"Shegiya karuwa! ýar wuta kawai". Kowa ya dinga tofa albarkacin bakin sa. Kwalla fal suka cika idanun Laylah jin yadda kowa ke ta debe mata albarka bayan ba haka labarin yike ba.
"Aikam cikin dare auntie ta watsar mata da kaya waje".
"Ai haka yafi".
"Taje a cigaba da yawon iskanci a titi".
Zainaba kuma ta cigaba da basu labarin da over 80% of it karya ne a ciki "Aikam a daren ranar mijin auntie ya sabule, ya fita neman ta kamar zai yi hauka, da yike ta riga ta rufe mai ido da asiri. Haka abun ya ta kawo musu matsala. Har dai daga baya aka fara suspecting ya ije ita yarinyar can wani gu ne as his mistress. A karshe dai in taqaita muku tun randa auntie ta kori yarinyar tashin hankali ya shigo gidanta har ya kai ga mutuwar igiyar auran ta daya". Ta fadi. Nan ma matan suka tsine wa Laylah, a cewar ta kashe wa wata aure.
KAMU SEDANG MEMBACA
JIRWAYE✔
Fiksi UmumKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...