Koh da zasu wuce gida, Yasmeenah ta miqawa key din mota ta ce mata ta tuqa. Jikinta duk yayi sanyi. Lumshe idanu tayi ta settling sosai a seat din motar. Koh da ta rufe ido, vivid picture din abunda ta gani earlier ne ke ta yawo a kanta.
Suna cikin hira ne wani wai assistant din mahaifin Fadeel ya hango su ya zo daukar yaron. Da gudu Fadeel ya miqe, ya manna wa Yasmeenah kiss a kumatu, ita ma Laylah ya juyo ya yi hugging dinta sannan ya manna mata kiss a both cheeks dinta.
"I owe you". Ya fadi kan ya ruga. Juyawar da yayi ya ruga da gudu ne Laylah ta lura da rubutun da aka yi a bayan Tshirt dinsa....... *Fadeel Al-Haydar*. Koh da ya qarasa gun wanda yazo daukar sa, ta ga ya rada wa mutumin abu a kunne sai mutumin ya ciro pen da wani dan kamar complimentary card da aka basa ya bawa yaron. Juyowa Fadeel yayi ya dawo da gudu yana magana numfashin sa sama sama saboda gudun da yayi.
"Yo...your nu...mber". Ya miqa mata dan card din da pen. Bata iya cewa komi ba kawai ta rubuta mai number dinta ta basa. Da gudu ya ruga akai akai yana Juyawa yana daga musu hannu har ya bace musu da gani. Qarar horn inda Yasmeenah ta saki wa wani me keke napep ne ya dawo da ita reality.
"Hmmm Yasmeenah". Ta kira sunan a hankula.
"Yes bae".
"Yanzu wancan yaron dan khalifa Al-Haydar ne?".
"Do you need to question me again? Tun yaushe Google yayi confirming mana dan sa ne. Muhammad Fadeel Al-Haydar".
"Fadeel yace da Babansa yazo park din. Kenan we were close to meeting khalifa Al-Haydar".
"Ke fa wannan obsession din ya fara yawa. Dan Allah ki mance wannan Al-Haydar din. Ya sha karfinmu". Shuru ta yi ta cigaba da nazari har ta ciro waya ta fara kallon hotunan ta da Fadeel. Yaron ya tsaya mata a rai sosai. Sannan kuma wannan mutumin da yazo ya dau yaron ta san ta taba ganin sa a wani gu amma kwata kwata ta rasa inda ta taba ganin sa gashi ta fadi wa Yasmeenah ta karyata ta, wai maybe deja vu ne kawai. A haka suka isa gida ba me cewa kowa komi. Laylah na Wucewa dakin ta ta fara shirin kwanciya kasancewar the next day a very busy day for her.
Haka rayuwa ya cigaba, Laylah nata aikin ta. Aside from sayar da jikinta, Laylah tana da cover business wanda take wa iyayenta karya dashi. Tana events planning and management wa mutane in suna da sha'ani especially kuma mutane na alfarma, masu naira. Daga nan kuma atimes take haduwa da manya mutane, kusoshin qasa.
Ranar da aka sa na fundraiser event din ya iso. Kowa ya so aikin da Laylah da team dinta suka yi. Yadda tayi planning event din ya burge kowa and Alhamdulillah masu kudi da yawa da politicians sun halacci tarun dun haka aka sama donations da yawa. Zuciyar ta fara bugu tayi sosai da sosai da taji an ambaci sunan Khalifa Al-Haydar, cewa be sama damar zuwa taron ba amma ya aika aminin sa Nawfal Muhammad Fadoul yayi representing dinsa. Daga kai da Laylah zata yi ta hadu da abun mamaki.
Rufe idanunta tayi ta kuma budawa dun confirming koh what she was seeing was really a reality. Abdulmalik ne tsaye a gefen Nawfal suna ta gaisawa da mutane. Koh da ya dago idanunsa basu fada koh ina ba sai a kan Laylah. Nan suka tsaya suna ta kallon juna. Miqewa tayi jiki babu sauran karfi ta fara tafia. Kawai tuno last day dinsu tayi a Australia and all that ensued between them taji kunyar sa ta kamata. Gani take kamar bata kyauta mai and in ta tsaya a gun sanin yana kusa, da wuya ta iya controlling emotions dinta dan koh a lokacin da ta gansa, ji tayi kamar ta ruga da gudu tayi hugging dinsa, ta fadi mai how much she missed him. Ji kawai tayi an riqo mata hannu.
"Bamu gaisa ba zaki wuce. Haka kika tsane ni? Koh hello ba zaki iya tsayawa ki mun ba? Koh kina kunyar aga kina magana da driver ne". Ta ji muryar that she had been longing to hear for weeks. Dogon ijiyar zuciya ta sauke kan ta juya tayi facing dinsa. Ta kai minti biyu duk ta rasa me zata ce mai kawai sai tayi following instincts dinta. Jawosa tayi jikinta tayi hugging dinsa lightly. A hankali ta sauke ijiyar zuciya, taji lokacin daya hankalinta ya kwanta. Kanshin cologne dinsa me dadi tayi ta shaqa taji kamar kar ta sake sa amma kuma da ta tuno islamically it's not right tho wasu suna yi, ita ma tana cikin masu yi tunda ita har jiki take sayarwa bare kuma wani hug. Sai dai kuma bata san wani kalar mutum ne shi ba tho lifestyle dinsa clearly shows how social and western he is kuma gashi cikin mutane suke.
"I've missed you". Tayi saurin zame jikinta daga nasa "Sorry if I was too forward, I was just overwhelmed by your presence".
"Shhhhhh" ya sa mata yatsar sa a baki. "I've missed you more". Ya fadi yana mata irin murmushin nan da ke hanata barcin dare. Wani sonsa ke da da shiga zuciyar ta. A da, she was living in oblivion, Kullum tana yaudarar kanta cewa ba sonsa take ba amma tun dan months inda suka yi basu ga juna ba ta tabbatar da lallai sonsa take, Sosaima kuwa ba kadan.
"Shine baka neme ni ba?". Ta fadi tana dan bata rai.
"Ke fa kika nuna baki son na neme ki. Ba ajinki bane yawo da driver".
"Ni nace maka haka?". Ta fadi tana rolling idanu. Dariya yayi kan ya bata haquri a zuciyar sa kuma yana ta murna ne. What she just did ya tabbatar masa da cewa abunda yike feeling for her isn't one sided, ita ma from all indications she feels something similar.
Sannu a hankali suka taka zuwa parking lot, inda Laylah tayi parking hadaddiyar motar ta me qirar BMW. Buda motar tayi suka shiga suka bar kofofin a bude sabo da tsananin zafi da motar yayi. Sun jima a zaune ba wanda ke cewa kowa komi sai dai su dan saci kallon juna. Ita ta fara buda baki ta yi breaking silence din.
"How has life been?".
"Alhamdulillah". Murmushi tayi kawai bata ce komi ba kuma. "Soooooo are we still buddies?". Ta tambaya.
"Depends on you, in baki damu da zama friends da mere driver ba".
"What if I don't want friendship?". Ya tambaya. Shuru tayi ta dade tana nazari kan ta buda baki tayi magana.
"I'm cool with it. Just say the word and I promise to disappear without a trace".
"Oh really". Ya juya ya Kalle ta da kyau yana daga mata gira. Lura yayi da expression din da ke fuskar ta, kamar ya sanja. "So as I was saying", ya tsaya ya san gyara murya "What if I want something beyond friendship?".
"Something like?". Dariya yayi kawai be ce mata komi ba. Pen inda ke breast pocket dinsa ya ciro ya jawo hannunta ya rubuta number dinsa a kan tafin hannun. "Call me when you have the answer, and remember i'll be cool with whatever your response is. Fi waqt akhar". Ya fita ya rufe mata door din motar. Tana kallo ya wuce cikin hall inda ake fundraiser event din koh Juyowa ya sake kallon ta be yi ba. Kai kawai ta ije kan steering wheel din motar zuciyar ta na mata saqe saqe iri iri ga wani irin sonsa da ke da da shiga ran ta.
One thing she has noticed about Abdulmalik is that gashi dai talaka amma sai shegen attitude. Gashi da charisma and wani aura na power da yike da. Duk sanda zai yi magana, babu tsoro bare fargaban wani abu ya faru yike yi. Maganar ma in zai yi sai ya dau lokaci yana nazarin words inda zai furta, Yanga dai da jan aji akwai shi sosai a gun sa. In ba Abdulmalik ba, wana driver ne har ya kai yawa Laylah magana the way he just did. Murmushi kawai tayi, arrogance is a quality she had always adored in men. Rufo door din gefen ta tayi ta ja motar ta zuwa gida mind dinta too preoccupied with thoughts. Sai da ta kai gida tukun ta kira P.A dinta wanda ta bari a can gun event din.
Abdulmalik kuma tunda Tariq ya dawo dauke da Fadeel a kafadar sa suna wasa ya hau mai fada akan irin tsoron da suka basu. Shi dai Tariq be ce komi ba yayi ta bada haquri. Fadeel ne ya fara bawa mahaifin nasa labarin new friends inda ya hadu da. Tariq be ce komi ba sai da ya bari suka shiga cikin gida tukun ya nufi hanyar study din Abdulmalik inda ya same sa har ya shiga ya kama aiki a computer dinsa.
"Sir....".
"Yes Tariq.... what's the problem?". Ya tambaya.
"Ummm ba wani serious abu bane". Ya fadi yana sosa kai "dama.....".
"Look Tariq I don't have all day, dama me?".
"The lady little master was talking about, it was her sir. Laylah, the lady from Australia". Dago kai Abdulmalik yayi yana kallonsa.
"Laylah? You're sure of that?".
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Hey guys! This chapter is a little jumbled. Well thanks to umm Irfaan da bazata barni na sha iska ba because she misses khalifa. Anyways I hope you guys liked the chapter. Xx
VOUS LISEZ
JIRWAYE✔
Fiction généraleKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...