"Wai ba zaki fito ki dau wannan Alalan ba". Rabi ta fadi tana hararar Badejo.
"Ni gaskia Ummati ba zani talla ba, kefa kika ce bayi da kyau. Kina ji satin da ya wuce karime ta haihu ba aure kuma sanadin talla ta yo cikin".
"Dallah rufe mun baki, mutuniyar banza".
Malam da ke kwance bisa tabarma a gefe ya buda baki yana kokarin magana "R...ra....bi". Yana magana miyau na bin gefen fuskar sa, Wayyo ciwo "ki ra....r....rabu da i....ta bata son ta...". Be ma kai ga gama magana ba Rabi ta watso mai wani kallo tana jaraba.
"Dallah can rufe mun baki, in bata je ba waye zai je? In bar wankaun da nike yi ne na dinga fita tallan koh kai zaka tashi ka tafi tallan. Dan rainin hankali, sai anyi magana kace Allah zai hore, shekara biyu kenan baka da aiki sai kwanciya gu daya kudin magani ni ce, na abinci ni ce. Mutuwar ka ki kayi na huta".
Badejo cikin hawaye tace wa mahaifiyar ta ya isa zata tallan. Ta wuce ciki ta dau hijaab dinta dogo mai tsafta ta saka, Auta na ganin ta sa hijaab ita ma ta dau nata ta saka, qafar Addan ta qafar ta. Badejo tayi tayi a kan cewa Auta ta zauna ta kammala assignment dinta amma ta qi. Ita Badejo dama tun Shekarar da ya wuce ta daina zuwa makaranta dan rashin kudi dan kuma ta taimaka wa Ummati wadda ke aikin wankau, da sana'ar suke ci, su sha, a siyawa malam magani.
Suna fitowa mahaifin su ya shiga zubda hawaye, wai yaransa ne yau wanda yike so kamar me zasu talla. Koh a mafarki be taba tunanin ganin irin wannan ranar ba. A zuciyarsa yayi tir da haihuwar na miji. Duk kudin sa yayi wasting akan wancan shashashan gashi yanzu shaye shaye a gun Suraj ba komi ba, da aka koresa daga makaranta ya dawo gida, at first yana yi aka boye amma yanzu kaf garin ba wanda be san halin da yike ciki ba, duk ya zama wani iri, daga shaye shaye sai fada da yawon banza kawai ya iya. Mahaifiyar sa ta ne ma ta dafa kuma ta basa ya ci, in ta ije kudi ma ya gani ya dauka ya je yayi shaye shaye da su.
Su kam tunda suka je bakin kasuwa suka zauna tare da wasu ýan mata wanda su ma talla suke ake ta tsokanar su, wai me ya sama yaran gwal, aka gansu da tallan alala. Su dai basu tanka ba suka zauna shuru. Suna kallo kusan ko wace yarinya ta siyar da kayan tallan ta amma su koh Rabi basu yi ba. Da samari sun zo sai suce zasu musu juye, su kuma su tashi su bi. Baya wuce ayi amfani dasu a biya su daidai kudin kayan tallan su su kai gida dun gudun fada daga iyayen su mata. Toh ýan uwa ina amfanin wannan rayuwa? A tura yara talla sannan ace lallai lallai sai sun sayar da gaba daya kayan da aka basu, ai dole a tunzura yaro ya bi hanyar da bata dace ba. Talauci ba hauka bane, and hawking isn't always the option. Akwai hanyoyin nema kudi iri iri ba lallai sai tallan ba kuma in ya kama dole sai tallan sai ayi sa cikin tsoran Allah, amma yanzu yarinya zata fita talla sai kaji ana tillasta mata akan dole sai tayi ado, tallan abinci ta fita koh na jiki? Ai dole ma maza su tare yarinya su mata zancen banza.
Badejo na cikin tunanin ta taji muryar wani kusa da ita. "Me alala nawa ne?".
"Naira ashirin ce". Ta ansa shi.
"Aah wai gaba daya Alalan nike tambaya". Badejo ta dago ta kallesa cikin mamaki, me zai yi da dukan alalan?.
"Naira dariya uku da sittin ne". Auta ta ansa mai.
"Toh tashi muje in baki kudin". Ya fadi yana murmushi.
"Aah, gaskia bazan iya bin ka ba. Kaje ka dauko kudin".
"Haba ýan mata, minti nawa ne zaki biyo ni na baki kudin ki, mu dan huta ki dawo".
"Dan Allah ka wuce, alalan ma na fasa sayar maka". Ta fadi rai a hade.
"Kaji ýar iska, ni zaki wa jan aji? Waye be san halin ku ba ýan talla. Karuwar banza da wofi". Ya ja tsaki ya wuce. Badejo ta ije kai a qasa tana kuka. In ba dan kaddara ba ina ita ina talla har wani namiji ya fadi mata zancen banza. Wai ita ce yau aka kira da sunan karuwa.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...