JIRWAYE....... The Stained Veil!
An Engausa Story By Haphsertuh
Babi Na Talatin Da Uku.
"Baban Ammah lafia?". Zubaidah ta tambaya, face dinta cike da mamaki. Sai da ya wuce guestroom ya Kwantar da Laylah, sannan yace wa Zubaidah ta dauko kayan aikin ta tazo ta duba Laylah, kasancewar ta a qualified nurse. Ba tare da bata lokaci ba ta shiga duba ta.
"She's running a very temperature". Ta fadi tana rubutu a wani dan takarda "Go get these stuffs now". Ta miqawa mijinta takardan. Kan ya je pharmacy ya dawo ta samu ruwa a dan bowl da hand towel tana goge mata jiki to help with the fever. Yana dawowa ta fara fixing cannula din aka sa mata saline nan da nan. Drugs din kuma aka ije sai ta farka ta dan sa abu a ciki tukunna.
Koh kadan Hamma Suraj be matsa daga dakin ba ranar. Wuri ya samu ya zauna idanunsa na kan ýar uwarsa. Sai can cikin daren at around 3am kan Laylah ta farka. Lokacin barci ya dan fara tafia da Hamma Suraj, kamar a mafarki yaji tana magana.
"Water...". Ta fadi a hankula. Miqewa yayi ya dauko jug din ruwa da matar sa ta ije kan ta wuce barci, ya zuba a glass ya miqa mata yana mata sannu. Sai da ta shanye ruwan ya karbi glass din ya ije kan ya fara tambaya ya take ji.
"Just a headache". Ta fadi mai.
"Are you sure? Your body doesn't ache? Your eyes, your.....".
"Hammaaaa" ta ja sunansa "Nace i'm okay, cross my heart". Ta fadi kan ta dan lumshe idanunta tana sauke ijiyar zuci.
"Are you ready to talk about everything?". Ya tambaya amma sai ta share tambayar sa ta fadi mai ita yunwa take ji. Nan da nan ba tare da bata lokaci ba ya hada mata tea da sandwich ya kawo ta dan ci kadan after which ta kwanta ta koma barci. Sai lokacin shima Hamma Suraj ya wuce ya same matar sa suka kwanta.
Washe gari bayan ya tashi daga office ya shiga ya duba factory dinsa, inda ake producing bread da refined water, ya ja mota ya wuce gida ya cewa Auta ta hado wa Laylah ýan kayan da zata buqata saboda yana ganin she'll live for a short while in his place. Ba gardama duk su Ummati suka yarda da judgement dinsa aka hada mata kaya a wata ýar akwati ya wuce mata da su. Koh da ya koma gida yaji dadin yadda ya izza Laylah ta sama sauki sosai tana ta wasan ta da baby Ammah, Zubaidah kuma na zaune tana ta faman daukar su hoto. A Kullum yana godewa Allah da ya hada kawunan matar sa da na ýan uwansa, koh kadan tunda ya aurota Zubaidah bata taba experiencing wani baqin hali from his people ba, ita ma kuma haka bata taba nuna musu halin ko in kula ba koh ta musu rashin mutunci. Suna zaman su cikin kwanciyar hankali.
Murmushi yayi, yazo yayi kissing dukan su a kumatu kan ya wuce daki to freshen up and change into something casual. Hamma Suraj dai yana nan yana ta noticing din sister dinsa, dan ya lura koh abincin kirki bata iya ci, sai tunani kawai. Suna gama cin abinci ya wuce ya dauko mata box dinta ya kai mata har daki. A hankula yayi sallama ya jira ta basa izinin shiga amma yaji shuru. Da yayi sallama har 3 times ba answer sai ya dan turo kofar kadan ya shiga. Izza ta yayi a tsakiyar bed zaune tana ta faman sharar kuka. Cikin hanzari ya ije box din ya nufi inda take.
"Hey! What's wrong". Ya tambaya yana tallafo ta zuwa jikinsa. Shuru tayi bata ce komi ba tana ta kuka a jikinsa shikuma yayi ta rarrashinta har dai ta haqura ta daina kukan barci yayi gaba da ita. Tashi yayi ya bar dakin ya wuce ya sama matar sa.
"Na rasa how to go about this, abu na damunta ta qi fadi. Ni dama ban yarda da dawowar ta yola ba". Ya fadiwa Zubaidah da tayi shuru tana sauraron sa.
"Haquri zaka yi, mu bi ta a hankula. She'll open up gradually". Ta fadiwa mijin nata tana daurawa baby Ammah diaper.
"Yawwa least I forget, nayi inviting Mahmoud da family dinsa for dinner on Friday night".
Murmushi tayi kan ta ansa shi da "Allah ya kaimu ranar lafia". Shikuma ya ansa ta da Ameen kan ya cigaba da tambayar ta abubuwa da babu a gida.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...