Abdulmalik kan sa ya daure a kan meyasa take son sanin relationship inda ke tsakaninsa da Al-Mubaraq amma be bari ta gane ba. Gyaran murya yayi kan ya bata ansa.
"Al-Mubaraq kawu ne a gun khalifa. Not like they're related by blood amma tun khalifa na yaro karami Al-Mubaraq ke aiki da su. Mohammed Mumtaz Al-Haydar was his godfather".
"Ohhhhhh I see". Ta gyada kai kamar tana nazari.
"Is there something between you both? As in Al-Mubaraq da ke".
"Aah! Not at all" ta ansa cikin sauri "He's just a blast from the past. Nothing out of the ordinary". Tayi dan murmushi.
Suna gama cin abinci suka fita zuwa cikin park din. Samun wuri suka yi suka zauna suna ta hirar rayuwa and all. Abdulmalik ya miqe ya je ya siyo mata ice-cream shikuma ya siyawa kansa popsicle dun ice-cream be cika damun sa ba. Suna zaune suna ta kallon wasu yara suna ta wasa, Abdulmalik ya ciro camera dinsa ya fara daukan hoto.
"Meyasa kake yawo da camera?".
"My boy loves adventures, so duk sanda nayi tafia ina yawo da camera to capture all I can for him".
"Awwwwnnnn. That reminds me, you were telling me about him the other....". Bata kai da gama tambayar sa ba wayarta ta hau ringing. Sanda kuma ta gama answer call din ta mance so haka aka bar zancen. Zaune suke shuru ba me cewa kowa komi kawai Abdulmalik yaji saukar abu me sanyi a hancin sa. Juyawar da zai yi yayi facing dinta kuma yaga camera yayi flashing.
"Crap! Allah sai na rama". Ice-cream ne tayi scooping ta zuba mai kan hanci.
"Ba sai ka rama mu gani ba". Ta fadi tana mai gwalo. Cigaba da daukan sa hoto tayi shikuma ya biye mata. Can bata zata ba zata kai cone din ice-cream dinta baki kawai Abdulmalik ya dungure mata hannu ice-cream duk ya bata mata hanci da face.
"Who's looking like a clown now huhh". Ya fadi yana mata dariya. "Click" taji qarar camera dinsa ya mata hoto. Ita ma ciro wayarta tayi ta matso kusa dashi suka ta hoto. Sai da suka gaji suka daina. Nan kuma ta hade rai wai ya bata mata face yanzu ina zata sama ruwan wanke wa. Be ce mata komi ba ya ciro dan hankie from his breast pocket ya fara share mata face. Ita kuma shuru kawai tayi tana kallonsa. Wani irin bugu kawai zuciyarta ke mata. Koh shakka babu wannan Abdulmalik din ya fara samun gun zama a zuciyarta kuma haka be kamata ba. Tana gudun wannan sabuwar lamarin da zuciyar ta ta bullo mata dashi. A tsarin ta babu soyayya dun a ganin ta ba namiji da zai taba accepting dinta after seeing her true colours.
"Earth to Laylah. Tunanin me kike yi haka". Ya tambaya.
"Nothing, let's go to the fish pond". Ta jawo mai hannu har zuwa fish pond din inda suka jima suna kallon fishes as they swam round the pond. Sai yamma sosai suka kama hanya. Bus station suka koma wannan karan suka yi saa akwai enough space, zama suka yi suna ta hirar su wata ýar tsohuwa kuma da ke zaune adjacent to them tayi ta kallonsu tana murmushi.
Suna sauka a bus stop din kusa da Jk guesthouse suka cigaba da takowa a hankula. Jefi Jefi suna dan taba hira. Suna isa wani florist shop yace su tsaya. Single rose flower ya siya ya bata sannan suka wuce. Har zasu tafi yaga wani bunch din lavender ya cira guda daya yasa mata a gefen gashi.
"Newly wed?" Ýar dattijuwan matar da ke da shagon ta tambaya. Dariya suka yi suka kalli juna sannan suka ce mata aah.
"I wish tho". Laylah ta fadi a hankula amma sai da ya ji ta.
"We can make it a reality you know" Juyowa tayi ta Kalle sa tana dariya kan ta basa ansa.
"Daga wasa".
"You look cute". Ya fadi, his voice sending chills to her spine.
"And you're so sweet". Basu yi nisa da shop din ba aka fara yayyafin ruwa kan kace me ruwan yayi karfi. Jawo ta yike ta yi su fake a patio din wani gida amma ta qi.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...