Babi Na Biyu (02).

4.7K 472 4
                                    

Yi hooooooooooo💃💃💃💃💃. I can't keep calm, koh kun san meyasa? Jirwaye is generating fans already.

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Kiran sallan subh ne ya tayar da shi daga barcin sa. Yana tashi zaune azkhar ya fara kan ya miqe ya nufi ban daki. Sai da yayi wanka, ya wanke baki tukun ya shimfida sallaya yayi sallah. Yau be fita zuwa masjid ba a dalilin tafiyar da ke gaban sa. Yana idda sallah ya hau kan arranging box inda zai yi tafia dashi. Be huta ba sai da ya gama hada komi tukun. Sake shiri yayi cikin kaya masu kyau, ya fesa su turare da sauran su tukun ya wuce sitting room inda ke part dinsa ya dau laptop dinsa ya hau kan danne danne.

Jim kadan sai ya ji motsin mutum ya buda kofar dakinsa ba tare da tambayar permission ba. Kanshin turaren da ya daki hancinsa kawai ya sanar dashi waya shigo.

"And here comes the lady before my heart". Ya fadi ba tare da ya dago kai ba daga laptop dinsa.

"Ya akayi ka san ni ce?". Ta tambaya bayan ta zauna kusa dashi.

"How can a son not recognise his mother?". Yayi murmushi gami da dago da kansa ya kalli mahaifiyar sa. Kamar yadda ta saba a Kullum, yau ma tana sanye da kaya masu kyau, kayana alfarma gata dama da jiki me kyau. A Kullum tamkar kara kuruciya take, kwata kwata ba alaman tsufa a tare da ita. Murmushi tayi ta jawo danta jikinta.

"Khalifatullah...." Ta kira sunansa kamar yadda ta saba kira a cikin murya me sanyi "Do you have to have go? Ni kwata kwata hankali na be kwanta da wannan tafiyar taka ba".

"Look here begum, you know I'm doing this for you and I. For both of us right? I promise zan kiraki each and every day and I'll be back in no time. Ina gama abunda ya kaini zaki ganni gida".

"Alkawari?".

"Cikawa" ya fadi yana murmushi.

"Toh tashi muje kayi breakfast na kai ka airport. I know how hot headed you can be, don't say no".

"No begum, kema kinsan we can't be seen together koh, i'll take a bus".

"Khalifatullah....." yayi saurin rufe mata baki kan ta ce komi. Yayi amfani da dayan hannunsa ya share mata hawaye.

"Ba yaro bane ni, na san hanyar gida. Zan dawo I promise".

"Shikenan, Allah yayi maka albarka da na". Ta riqe hannunsa zuwa kitchen inda tayi serving dinsa abinci. Ta zauna ta basa da kanta a baki har sai da yace ya qoshi tukun ta daina bashi. Zata tashi ta wanke hannun ta ya zaunar da ita.

"It's now my turn to fulfill my obligation towards you". Ya fara bata abinci yadda ita ma ta basa a baki. A duk lokacin da Khalifatullah ya ciyar da ita, wani irin murna mara misaltuwa ke rufe ta. A Kullum son dan ta kara cika mata zuciya yike ga kuma alfahari da take yi da shi a Kullum sai dai kuma rayuwar yaron nata na matukar bata mamaki, yadda yike tafiyar da alamuransa da kuma irin saukin kai da Allah ya basa.

Gama bata abinci yayi sannan ya kwashi plates din ya wuce dasu sink suka wanke hannun su yace bara ya wanke plates din ta hanasa.

"You'll miss your flight". Ta fadi tare da tura sa zuwa dakinsa ya shirya. Wucewa yayi ya sake kaya zuwa wani sweatpant da dan hoodie dinsa saboda yanayi weather ana dan sanyi. Bayan ya gama shiri ya fito yana jan ýar jakarsa. Yayi sallama da mamansa.

"Do give Hisham the keys to the apartment okay". Ya fadi tare da kissing goshin maman nasa wadda har wannan lokacin tana cikin jimamin tafiyar da dan nata zai yi.

"Beguuuuum....... come on. Wannan fa ba shine karo na farko da nike tafia ba, i'll be okay I promise".

"I'll miss you son". Ta fadi "You sure you don't want me to drop you off at the airport?".

"Aah, i'll be fine". Da kyar dai Khalifatullah ya iya sallama da mamansa ya ja box nasa ya wuce bus station inda ya sama drop na taxi har zuwa airport. Ba tare da bata lokacin ba ya shiga queue duk ya gama formalities na airport. Yana shiga jirgi aka yi directing dinsa zuwa seat nasa ya sama wuri kusa da window ya zauna. Can ya daga magazine da akan ije ma passengers a jirgi ya fara dubawa har barci yayi awon gaba dashi kasancewar a daren jiya be samu isasshen barci ba. After what seemed like forever, Khalifatullah ya farka daga barcin da yike, hasalima fitsari da ya riqe sa ne ya tayar dashi daga barcin. A lokacin ne ya lura har jirgin su ya daga. Juyawa da zai yi, idanuwansa suka yi ido hudu da seat mate dinsa. Mace ce wadda a shekaru ba zata wuci shekara ashirin da hudu zuwa da biyar ba haka. Be tsaya kallon ta ba da kyau ya dauke idanunsa a kanta. Shi ya kasance mutum ne me matukar kunyan hada ido da mutane tun bare ma mata. Duk yadda yike da son wasa da barkwanci, da wuya ya kalli mutum cikin ido bare ma har ya tsaya kallon mace.

"Hello" kawai ya fadi ba tare da ya kuma kallon gefen ta ba ya miqe dan ya nufi washroom ya biya buqatan sa. Har ya dan fara tafia muryar ta ya tsayar dashi. Cikin wata murya tayi maganan, cikin bacin rai.

"Malam koh dutsen da ka taka bata ji maka ciwo ba". Maganar kwarai da gaske ta dan sosa ran sa saboda irin muryar da tayi amfani dashi ba wai dun ya gane gatsen da ta mai ba kasancewar ba wata isasshiyar hausa yaji ba.

'Even begum doesn't use that tone on me' ya fadi a ransa amma a fili sai ya maida mata da ansa me cike da tsokana. "Dutse kuma baiwar Allah? Koh dai shigar ki jirgin sama na farko kenan" ya fadi gami da tuntsurewa da dariya ganin maganar ta da da bata mata rai.

Wata tsaki yaji ta saki shi kam koh a jikinsa ya wuce washroom yayi fitsarin sa ya fito sai dai yana iso wa seat dinsa yaga hajia almasifatu ta koma seat dinsa wanda ke kusa da window ta zauna. In zaa bi gaskia, Khalifatullah ya san seat din nata ne but shi kuma a gaskia ya fi son window seat don haka yazo yace mata alambaran sai dai ta tashi ita kuma ta qi sai ya rabu da ita amma a zuci ya quduri niyyar sai ya koma seat dinnan kuma true to his word, haka aka yi. Sai da ya sa ta tashi daga seat din ta bar mai.

'What Khalifatullah wants, he gets'. Ya fadi a zuci cike da murnan korar ta daga seat din baki daya dama shi mutum ne wanda ya tsani zama kusa da mata. Kwata kwata baya so abu ya hada sa da mata dun sha'ani dasu nada wuyan gaske kuma sai me haquri.

Da isan su qasar Australia ya shiga ya sanja kaya kafin ya fito ya nufa arrival lounge na airport din. A lokacin ne ya tuna da ipad din seat mate dinsa a jirgi wanda yike tare dashi.

"Shit! Where the hell do I start looking for her". Ya fadi tare da jan ýar tsaki. Nan dai ya fara dan tafia yana sa ido koh Allah zai hadashi da ita. Yana cikin tafia ya ji an tabo sa daga baya. A zaton sa, koh ita ce ta gansa ta biyo sa dun ta karbi ipad dinta amma yana juyawa yaga ba ita bace.

Nawfal ne, amininsa kuma cousin brother dinsa. Kan ya ankara ya jawo sa zuwa jikinsa yana hugging dinsa cikin murna. "Man I missed you". Nawfal ya fadi.

"I've missed you too". Shima ya fadi cikin murna. Bayan gaisuwan yaushe rabo, suka fara takawa zuwa parking lot Nawfal na jawo dan trolley din Khalifatullah har su isa inda yayi parking motar sa.

"Mamu doesn't know you're in Australia, does he?". Nawfal ya juya ya tambaya dan uwansa.

"No, I'm here for some work. I'd love to be uncovered for a while. Zan maka bayani in na huta". Ya fadi ma Nawfal wanda har ya jawo hadaddiyar motar sa me qirar chevrolet camaro sun hayo kan titi. Can jim kadan, Khalifatullah ya fito da wannan ipad din luckily for him kuma ipad din baya da password koh pattern dun haka swiping kawai yayi sai ya bude. Nan da nan ya fara buga game din candy crush can kuma yaji kawai wata zuciya tana raya mai da ya shiga gallery dinta.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Barka jama'a..... how are we finding Jirwaye? Still boring aye. Kada ku damu, the story is just starting, like I said you won't regret reading this story. That I assure you. Nasan hausan akwai mistakes da yawa, feel free to slid into my dm to correct me. Godia lodi lodi.

JIRWAYE✔Onde histórias criam vida. Descubra agora