fateemahh0023 Happy birthday in arrears habibty. The chapter is for you. Ina nan ina jiran cake dina, have fun!
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Ta sauke yaran kenan a school ta dawo gida tana ýan gyare gyaren ta kamar yadda ta saba sai ga Mahmoud ya fito cikin shirin sa tsaf zai wuce aiki. A safiyar ranar yana da lecture na safe.
"Masha Allah" ya fadi da yaji irin kamshin da gidan ke ta faman yi "wannan kamshi haka ai sai ya hanani zuwa aiki ince ni a gida zan zauna yau". Qarasawa tayi inda yike ta fara gyara masa hular Zanna Bukar inda ke kansa.
"Har ka fito... wallahi yau ka matukar yin kyau. Har gayun yau ya fi na jiya, Anya zan iya bari ka tafi makaranta kuwa yau, kar ka je students su ta Kalle mun kai, I think blue is your colour". Ta fadi tana dariya.
"Karki damu Hidayah, ai ni naki ne ke daya".
"Mamansu Kauthar kuma fa? Bazata dawo ba yaya?". Ýan yatsun sa biyu ya hada ya dan bugi bakin ta.
"Ba nace ki daina dago mun zancen ta ba kuma sannan ba nace a sama mun wani sunan da ya dace dani ba?".
"Afuwan mai gidana. Insha Allah zan kula" ta fadi tana riqo hannunsa "Muje ka karya kan ka fita koh".
"Yaran fa?".
"Tab! An sun jima a school". Dadi sosai yaji, irin kular da yaransa suke samu har zuwa shi kansa basu taba samun irin sa ba a lokacin da yike tare da zainaba. Hasalima Kullum hukumar makaranta tana qorafi akan yadda yaran ke zuwa latti, kuma Kullum unorganised, koh ba suyi kitso ba koh kuma baa goge uniform nasu ba. Makaranta kam dama mafi yawanci in yana da morning lectures sai ya riga su barin gida dan baa kai su da wuri. Amma tun sanda Auta ta shigo gidan a matsayin matar sa komi ya sanja, kula sosai take basu, ga yadda take tarairayar sa, da ka gansa ka san yanzu Mahmoud ya sama kwanciyar hankali. Ýan uwansa kowa sai sa mata albarka ake haka ma abokan sa.
"Allah ya miki albarka" ya fadi yana placing dan kiss a saman goshinta bayan ya gama cin abinci ya miqe zai wuce. Har bakin mota ta raka sa riqe da jakar sa, tana ta masa addua. "Yawwa kan na mance, saman drawer dun bedroom akwai kudi na ije, sai ki shiga market yau koh kiyi shopping din komawa makaranta".
"Nagode sosai ya... mijina. Allah ya qara budi". Ta fadi fuskar ta cike da fara'a "Amma kuma...".
"Amma kuma me Hidayah?".
"Zancen baby Isma'il".
"Ai na fadi miki zan maida shi gidan Daadan sa tunda zaki koma school".
"Aah wai zancen da na maka akan in ta fi dashi, in ya so sai na sama nanny".
"Toh ke kya hada karatu da dawainiyar yaro? Ehh".
"Toh ai semester daya ya rage mun kuma nace zan sama nanny, gashi yaro ya saba dani ban son muna raba masa hankali, yau yi na nan gobe yi na can". Ta fadi tana dan tabe baki.
"Toh toh naji, amma yanzu i'm late. We'll discuss about that when i'm back okay, ki kula mun da kanki". Ya fadi yana shafa lallausar kumatunta.
"Kai ma haka". Ta fadi kan ta manna masa kiss a kumatu ta rufe masa door din mota, sai da taga fitar sa daga harabar gidan kan ta koma ciki dubo baby Isma'il koh ya tashi ta shirya sa.
Tunda ya isa Lagos ba abunda yike in ba aiki ba, once in a while sparing a few minutes to speak to Laylah and Fadeel. Kamar yadda yayi a daren sa na farko a Lagos, ranar ma kwana yayi a office yana going through reports, kadan da kadan yana warware komi da komi, every transaction da property na khalif airlines and group of companies yana going through details din.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...