A ranar Abdulmalik ya wuni cikin nazari. A karshe dai ya miqe yace bara ya dan rage workload inda ke kansa. Yana cikin aikin nasa ne email din Tariq ya shigo. Finally! Abunda yike ta jira tun safe ya isa, the face of Laylah Jaan. Sai da ya ja dogon numfashi kan ya buda email din and alas! By God ban san me ya gani ba😉 wata murmushi kawai ya saki wadda ba da dadewa ba ta koma dariya. Da gudu ya miqe ya ruga living room inda ya baro Nawfal, kwala mai kira yike ta yi kan ya isa, murmushin sa a fadade.
Can cikin dare bayan ya dan gama aikin, Abdulmalik ya kwanta ya dan samu hutu kan ya kuma tashi. yina kwanciya ya jawo wayar sa dun abun ya zama mai alada, sai yayi latse latsen waya yike iya barci. Notifications din tarin unread messages inda ya gani a whatsapp dinsa ya sa ya shiga app din. Yana ta duba messages din, wasu yayi tsaki, wasu ya gyada kai, wasu ya ci dariya; kamar hoton da Hajjo ta turo mai na Fadeel. Can sai yaga wani message from an alien number, har zaya share message din can kuma ya ce bara dai ya ansa.
[12:59Am] Abdulmalik: Hey🙋. Yayi replying. Ba da dadewa ba yaga number din na typing reply.
[01:00Am] Laylah: Laylah here, the lady you gave your contact to earlier.
Dama shi tun asali Abdulmalik dan jan aji ne, a komi baya so mutane su ga he's looking or sounding desperate shiyasa a wannan karan ma sai da ya dan bata lokacin kan yayi replying dinta.
[01:11Am] Abdulmalik: Or better still, the lady who has been trailing after me ever since I set foot in Australia😁.
[01:15Am] Laylah: Whatever rows your boat. Amma dai ka san cewa Laylah bata bin namiji, sai dai maza su bita.
[01:17Am] Abdulmalik: Too cocky I see. Well let's not start off on a bad note miss.
[01:18Am] Laylah: like we haven't done that already.
[01:20Am] Abdulmalik: Time to make peace then I guess.
[01:23Am] Laylah: Sounds cool.... so it's safe to call you my buddy?
[01:24Am] Abdulmalik: yes.... buddy!
[01:25Am]: Did you just call me buddy?.
[01:26Am] Abdulmalik: yes.... buddy! And I just did again😉
[01: 28Am]: That's cool... buddy😀.
[01:30Am] Abdulmalik: Okay buddy, gotta go. I have an early start with boss tomorrow. Do sleep well.
[01:31Am] Laylah: Okay.... do take care. We'll talk tomorrow right?
[01:32Am] Abdulmalik: Insha Allah.
Yayi typing kan ya ije wayar sa ya gyara kwanciya amma ya rasa samun kansa da iya barci. Tunanin Laylah kawai yayi ta yi. A rayuwa ba macen da ta taba having such effect on him, koh deceased wife dinsa lokacin da suka fara haduwa bata yi having irin effect dinnan a kansa ba. Hasali ma a lokacin baya son ta kwata kwata ita ma kuma haka, kawai iyaye ne suka yi hadin and there was nothing they could do about it. Sai da suka yi zama har na shekara daya da Fatima kan maganan kirki ta fara hada su, a haka suka fara har suka zama friends and from there, gradually, they realised they were in love and in no time, they accepted each other har rabon Fadeel ya shiga tsakanin su. Wata ýar dariya ya saki da ya tuno da zahra sa.
"Allah jikan ki Fati na, ya raya mana Fadeel". Ya fadi in a low voice. Da kyar Abdulmalik ya iya barci ranar. Tunani yike ta yi of both Laylah and Fatima. He was confused about his feelings, shi dai ya san har ga Allah after loosing Fatima ba macen da zaya iya taba so bare har zancen aure ya shiga tsakaninsu amma kuma yanzu ya rasa yanda yike jin Laylah nan a ransa, ta shiga kawai ta kwanta a ciki. Bai taba kula da harkar wata ýa mace kamar yadda ya damu da na Laylah ba.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...