Yau fa chapter din naki ne Oum Jawad. I hope you enjoy it.
*let's go back to the present muji what khalifa Al-Haydar has to say*💃💃💃.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
"......And?". Khalifa ya tambaya da yaji tayi shuru in banda jan majina da hawaye ba abunda take yi.
"Kashe gari da safe, Yasmeenah ta bani kudi eighty thousand na tura gida dun Ummati ta samu ta rage crisis inda family dinmu ke ciki a lokacin. Koh da na tura mata kudin, rashin lafiyar Abba kadai ya cinye dubu hamsin a cikin kudin kan aka zo aka yi bailing din ya Suraj out of prison, da kyar suka anshi dubu ashirin. Sauran dubu goman kuma bazai isa registration din Auta ba, bazai isa Ummati ta kama hayan gida ba tunda ya Suraj ya sayar da gidanmu, ga rashin kudin kula da buqatun su,......". Ta kuma tsayawa kan after some time ta cigaba.
"Dun haka, a few days after I sent the money to them, Yasmeenah tayi wani baqo wanda a lokacin babban ma'aikacin government ne. Zuwan baqon nan ne ya wayar mun da kai, har na san asalin sana'ar Yasmeenah. She's a pimp, connecting ýan mata take yi da manyan mutane a biya ta kudi. Dun haka ranar baqon yazo a sama me budurwa kyakyawa that'll entertain him for the weekend sai ya ganni.....". Ta fadi murya na rawa.
"He offered me a hundred and fifty thousand naira, I was desperate, I needed the money and afterall there was nothing left of me, tunda I've already lost the one thing I've always been urged to safeguard, na zama baqar ashana. Out of desperation nayi taking offer din, ya biyani kudina na tura gida na biya wa iyayena buqatun su. And since from that day, sunana ya tashi daga Badejo to Laylah Jaan...... The heartthrob of the whole city, the heart desire of every man. Slowly nayi ta kashe wa ýan mata kasuwa dun duk wanda yazo sai yace shima sai ya dandani zumar Laylah Jaan. It became like a competition to the men, kowa na so ace shi ya fi biyana kudi masu yawa da yayi amfani da ni".
Dogon numfashi khalifa ya ja, koh kallon ta ya kasa ya buda baki ya tambaye ta "And your parents? Kika ce musu kina samun kudi a ina?".
"Karya nayi musu, nasan baza su taba jin dadi sanin diyar su ta zama karuwa, me siyar da jikinta dun samun biyan buqatun ta ba dun haka nace musu na sama aiki da wata hajia me kirki kuma ta sani a makaranta sannan zata dinga tura musu kudin da zai ishe su kula da kansu har na gama karatu na fara aiki. A haka na koma makaranta, da kudin karuwanci, nayi sponsoring Auta, da kudin karuwanci, na kai ya Suraj rehabilitation har ya gyaru ya koma karatu, da kudin karuwanci, na kai Abba na kashen waje da dama, da kudin karuwanci, Ummati tayi hajji da umrah, da kudin karuwanci. Da kudin karuwanci na ginawa iyayena gidan da duk Girei ba irin sa. Da kudin karuwanci na ba the people that mean the world to me all the happiness they deserve in the world". Ta zube qasa tana kuka kamar ran ta zai fita.
"I sacrificed my love, my body, my conscience just to make them happy. Na sabawa mahallici na just to keep them happy. Na rufe jikina da zuciya ta da Jirwaye just to place food on their table and happy smiles on their faces". Ya so ya tambaye ta ya rabuwar su da Mahmoud ya kasance amma ganin irin kukan da take yi ya sa shi karaya.
"You need some rest". Abunda kawai ya iya fadi mata kenan kan ya bar dakin ya koma living room din suite din ya zauna shuru cikin utter darkness. He was just trying to digest all she told him, yana ta nazarin rayuwa, circumstances and how cruel some people can be and most of all, ba abunda ya mai zafi kamar yadda har da hannun ýar Uwar sa a cikin bacewar rayuwar Laylah.
Khalifa ya dade a gun zaune shuru yana nazari iri iri, kwata kwata be yi tunanin haka meeting dinsu zai yi turning out ba. Yanzu her story has thrown his heart in confusion, be ma san me yike so ba kuma, ya kasa tunanin da kyau. Can towards subh ya leqa ya sama Laylah a kwance ta ci kuka har barci ya kwashe ta a qasa. Da har kamar zai daga ta ya maida kan gado sai kuma ya sanja mind dinsa kawai ya dau tuxedo dinsa da ya jefar kan gado the previous night ya nufi exit din Suite din. Without second thoughts ya fita daga Suite din. Yana isa lobby din ya anshi car key dinsa ya fi ce. Kwata kwata be damu da koh karfe nawa bane yayi ta driving recklessly a empty streets din Abuja.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...