Babi Na Arba'in Da Shidda (46).

2.5K 324 19
                                    

Koh da Nawfal ya daga wayar, cikin nutsuwa Laylah ta gaisa da shi tayi tambayar me jiki kan ta buqaci tayi magana da khalifa. Koh da ya ansa sun dade shuru ba me cewa kowa komi kan Laylah tayi breaking silence din. Comforting din sa ta dinga, tana ta fadi masa soothing words har daga karshe ta fadi masa cewa first thing the next morning zasu taho Abuja. Khalifa yayi da ita akan ta bari, kar ta damu da zuwa but she was being adamant.

"It's my duty. Please don't deprive me of that right. Farin cikin ka yanzu ya zama nawa, haka ma baqin cikin ka. I want to be by your side through this phase habibi, let's face it together". Da kyar dai khalifa ya yarda sannan ya fada mata cewar ta shirya he was going to send his private jet the next day a zo a dauke ta.

Ranar da kyar Laylah ta iya samun barci, gaba daya ta qosa next morning din yazo ta ganta a Abuja, by her husband's side. Shiryawa duka suka yi tsaf; da ita, Yasmeenah and Leek. Private jet din be yi arriving ba sai around 4 in the evening. A lokacin suka bar yola ana ta musu fatan alkhairi. Few clothes tayi parking dan ta san ba tafiya gaba daya zata yi ba, she'll still come back home kan a mata proper send off ceremony. Koh da suka isa Abuja, gidan Yasmeenah suka sauka. Da kyar ta yarda ta ci abinci, ta watsa ruwa ta dan huta kan suka kama hanyar zuwa The Regent hospital, a hospital which belongs to the Al-Haydar family. Hospital wanda sai dan wane da wane kawai ke iya affording saboda high standard dinsu, gashi asibitin is well equipped with first grade facilities and well qualified medical practitioners dun hospital din har turawa akwai, da Indians all working under khalifa Al-Haydar.

Koh da ta tashi barci, bathroom ta shiga ta kuma watsa ruwa kan ta fito ta sa wani A-line gown na atamfa me kyau sosai. Bata tsaya wani kwalliya ba saboda powder and kohl kawai ta sanya ma face dinta but she was still looking pretty. Waya ta daga ta kira Tariq wanda ta sama contact dinsa ne gun Nawfal. Tambayar sa tayi koh su khalifa sun ci abinci.

"Gaskia tunda muka dawo in ba coffee ba I can't remember them ever eating". Ya fadi mata dun haka da suka fita sai da ta cewa Yasmeenah suyi driving zuwa wani fancy restaurant su siya take outs for both men. Haka kuwa aka yi, abinci me lafia suka siya da desserts and cans of soda kan suka dau hanyar hospital din. Suna isa lobby din hospital din suka qarasa help desk suka wa receptionist inda ke wajen magana.

"Excuse me". Laylah ta fadi cikin wata murya me sanyi.

"Yes, how may i help you ma'am".

"Could you direct us to the special ward please". Ta fadi. Sai da receptionist din ta dan tsaya, dumbfounded for a few seconds tana kallon Laylah as if she had just grown a second head.

"Could you come again please".

"I said we need directions to the special ward. I'm here to see my husband whose mother is bedridden". Ta mata bayani, dariya matar ta tuntsure mata da shi. Abun ya batawa Laylah rai but still tayi maintaining composure dinta.

"I'm sorry ma'am but you must be mistaken, only the Al-Haydars have access to the special ward, you could check your husband in the other wards".

"Excuse me, I know what I'm saying, i'm here to see my hubby khalifa Al-Haydar".

"What, come again". Receptionist din ta kuma fadi tana dariya.

"Look i'm not here to joke. I need to see my husband".

"If you're Mr Al-Haydar's wife then I'm Aisha Buhari". Receptionist din ta ansa ta tana dariya. By that time haushi ya gama cika Laylah gashi ta mance wayar ta a mota bare ta kira Tariq and parking lot din was quiet far from the hospital's main building. Suna cikin wannan hayaniyar sai Allah ya kawo Tariq.

"Mrs Al-Haydar. Good day ma'am". Kawai taji an gaida ta. Kallon expression din fuskar receptionist din tayi sannan tayi smirking before returning Tariq's greeting. "This way please". Tariq ya fadi yana karban take out boxes inda ta riqe a hannunta. Koh second glance bata yi sparing ma receptionist din ba whose expression was now apologetic kawai ta wuce ta bi bayan Tariq suka wuce. Ward din ya fi ko ina a gaba daya hospital din kyau da tsaruwa.

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now