Wani qaton gida suka iso, filin gidan qato ga motoci iri iri masu tsada anyi parking. Yara biyu ne kananu suka doso su da gudu daga saukar su mota. Suna gudu suna kiran sunan zainaba, daga gani sun saba da ita sosai. Babban ne ya riga isowa ta jawo sa jikinsa tana mai wasa da gashin sa. Can sai karamar me suna Tasneem ita ma ta iso tana kuka a dauke ta. Badejo ce ta kai hannu zata daga ta amma ta qi zuwa saboda rashin sabo da ita. Suna shiga ciki, wani babban sitting room suka iso, Badejo nata mamakin girman dakin.
'Ai wannan yayi girman gaba daya gidanmu' take fadi a zuci. Sai kauyanci take ta yi, ta taba nan ta taba can. Hankalinta na can kallon chandelier inda ke sama taji muryar wata mata cike da fara'a na masu maraba. Tana dagowa suka hada ido da matar, fara tas, kyakyawa da ita ga jikinta sai walkiya yike ta yi alamar hutu. Sanye take da riga gown wanda da ka gansa ka san ba kalar talakawa bace, tsaye take tana shafa cikin ta tana tambayar zainaba ya ta baro mutan gida.
"Wannan ce yarinyar?" Ta tambaya da fara'ar ta. Kai zainaba ta daga mata, nan ta shiga gaisawa da Badejo tana tambayan ta ya gida ya ýan uwan ta. Matar dai daga gani tana da kirki.
"Ni suna na Sarah, Sarah Muhammad Fadoul". Ta fadi wa Badejo.
Kallon ta Badejo ta sake, a gaskia in kyau ne auntie Sarah akwai kyau ga kudi ga Ilimi. Family dinsu sanannun masu kudi ne, kuma ita yaya ce a gun Nawfal Muhammad Fadoul (mind you: a lokacin duk Badejo bata san da wannan ba). Mijinta babban architect ne, shima dan gidan masu kudi kuma Allah ya albarkaci auran su da yara biyu; Suleiman wanda shine babba danta, dan yaro be wuci 5 years ba sai kanwar sa Tasneem, ýar shekara 3 sai kuma cikin da take dashi a yanzu.
"Ai sai ki nuna mata daki koh, ku ci abinci ku huta". Riqo hannun Badejo zainaba tayi zuwa quaters din ýan aiki, nan da nan aka kawo musu abinci suka ci suka yi sallah suka huta.
Kan ka ce mai, Badejo ta zama ýar gida kuma auntie Sarah na son ta sosai saboda tana da tsafta da kuma kula gashi ta lura tana da Ilimi kuma tana son karatu. Yaran su ma duk sun saba da Badejo, kowa a gidan son ta yike. Ita kanta rayuwar gidan na mata dadi dan duk tayi kyau ta murje. Abu daya ne bata jin dadinsa a zaman ta a gidan, yadda mijin auntie Sarah ke mata wani irin kallo me cike da sha'awa.
Tana kitchen tana wanke wanke bayan lunch sai ji tayi kamar tafiyar mutum a hankula amma koh da ta juya sai bata ga kowa ba dun haka kawai ta cigaba da wanke wanken ta tana ýar waka. Can ta kuma jin motsi ta leqa amma ba kowa. Juyawar ta ke da wuya taji hannun mutum an rungumo ta. Salati ta saki da karfi kan aka yi saurin toshe mata baki. Turaren sa me dan Karen kamshi ya sanar da ita koh wanene. Juyowa tayi da qarfi, idanunta cike da kwalla.
"Un...unc....uncle wani abu kake so". Ta tambaya murya na rawa.
"Ni ke nike so". Ya fadi yana wata irin dariya gami da mata kallo me cike da sha'awa. "Kinyi shuru". Koh kallon sa ta kasa bare ta ce wani abu.
Ta buda baki zata yi magana kenan taji muryar auntie Sarah na magana, kuma daga ji hanyar kitchen in ta doso. Da sauri ya wayance yayi kamar yazo daukan abu ne a fridge ita kuma ta juya ta cigaba da aikin ta, zuciyar ta cike da mamakin yaudarar ďa namiji. Me mutum me kudi da matsayi irin uncle Mukhtar zai yi da ita bayan yana da matar sa ýar boko, kyakyawa, ga iya kwalliya.
"Ina ta neman ka, me ka shigo yi kitchen". Ta tambaya.
"Apple nazo dauka". Ya fadi yana mata murmushi. "Wannan ýar aikin ta ki akwai kallon banza". Ya fadi kan ya kama hanya ya fita. Auntie Sarah kam abun ya daure mata kai dun ta san Badejo a yarinya me ladabi da nutsuwa, toh me zai sa me gidan ta fadin ta mai kallon banza. Bata dai ce komi ba ta wuce ta bi bayan sa. Ita kam Badejo suna fita ta fashe da kuka, tana wanke wanke tana kuka, duk taji bata ma son zaman gidan kuma dan uncle Mukhtar ya tasa ta gaba kuma ita har ga Allah baza ta taba iya yaudarar auntie Sarah ba, mace me kirki da karamci.
ESTÁS LEYENDO
JIRWAYE✔
Ficción GeneralKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...