Babi Na Talatin (30).

2.8K 315 47
                                    


Hello haters! Look I made it to chapter 30...... let's throw some confetti in the air🎉🎊🎉🎉🎊🎊🎉🎉. Don't mind me😂😂.
Dumbin gaisuwa gareku masoyan Jirwaye...... Jirwaye celebrates y'all, Haphsertuh appreciates the love and support.

Kuma ina kan baka ta na yajin aiki😕😕😕

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Tana isa yola ta kira number din Hamma Suraj wanda in no time ya isa airport daukan ta. Koh da be fito waje ya fadi ba, his expression said it all, he was highly surprised about his sister's sudden visit kuma gashi yaga tazo da kaya masu yawa, alaman ba irin casual visits inda take yi bane ta gansu ta koma. Be ce mata komi ba, shuru suka zauna a mota once in a while suna dan taba hira. In ka ga Suraj kamar ba Suraj inda ke shaye shaye da fadace fadace ba few years ago, ya wanku, ya gyaru ya koma makaranta yayi starting afresh. Yanzu haka ya gama ya kama business kuma Alhamdulillah he's making it. Yayi aure da diyar sa daya tal wanda aka mayar mata sunan Ummati, wato Rabi'atu. Ita kam Auta Hidayatu tana final year dinta a university inda take karanta dream course dinta, wato civil law.

Har suka isa gida bata sani ba, hankalinta na can yayi nisa cikin tunani. Sai da Hamma Suraj ya tabo ta kan ta fito daga motar. Masu aikin gidan ne guda biyu maza suka rugo da gudu dun kwasan kayan Laylah, sai gaidata suke a ladabce.  Ta dade tana kallon gidan tana yaba kyaun sa, sabon gida ne wanda baa dade da shigar sa ba dun koh 3 years iyayenta basu yi ba da tarewa a gidan wanda ke cikin garin jimeta, dun yanzu level ya sanja an rabu da zama kauyen Girei.

Dan kwalla da ya zubo tayi saurin sharewa kan ta fara taku a hankula towards main entrance na gidan. Ba komi ne ya sa ta kwalla ba illa tuna rayuwar su a baya da tayi. Hakika da 10 years ago zaa fadi mata cewa ita Badejo watarana zata mallaki irin dukiyar da take da a yanzu ba koh kadan bazata yarda ba. Kasashen duniya nawa taje? Manyan mutane nawa ta hadu da? Motoci masu tsada nawa gareta, gidaje, plots ga successful business empire da take da. Indeed Allah shine abun godewa. Yanzu in life, abu daya ya rage mata; to repent and move on in life.

Tana shiga ta izza Ummati da Abba zaune a living room din downstairs suna kallon news. Cike da murna ta qarasa inda suke ta fada Jikin Ummati sai hawaye kawai suka kufce mata. Ji tayi wani mugun so da kaunar iyayenta na da da shiga zucin ta.

"Laaa yau ina ganin shegantaka". Fadin Ummati "Badejo yau kika fara zuwa gida ne, da zaki tasa mu gaba kina kuka". Share hawayen ta tayi kan ta juyo ta zauna kusa da Abba tana fadi musu cewar tayi kewar su sosai.

"Kuma yanzu insha Allah na dawo yola, zan zauna nan da ku".

"Ke haba". Ummati ta fadi cike da murna, dama ta dade tana wa Badejo fadan zaman kanta da take yi a Abuja.

"Ehhh Ummati, ina so na buda branch na business dina nan yola sai na zauna kusa da ku koh". Ta fadi. Ana cikin haka muryar Zubaidah matar Hamma Suraj ya katse su. Tana isa ta miqa 3 months old baby dinta ma Badejo kan ta zauna kusa da Ummati suka fara gaisawa. Ranar murna a gun kowa abun baa cewa komi, kowa yayi Na'am da decision din Badejo na dawo gida cikin ýan uwan ta.

Duk yadda Badejo tayi ta boye damuwar ta, ta gaza. Sai da mahaifiyar ta ta gane da abunda ke damun diyar ta ta dun haka ta taso ta gaba akan sai ta fadi mata matsalar ta.

"Allah Ummati ba komi bane, kawai ina missing Yasmeenah ne". Tayi karya.

"Karya ne Badejo, ban yarda ba. Yau watan ki daya da dawowa gida amma duk na lura kina boye mana wani abu. Kina da damuwa amma kin kasa fitowa ki fadi mana". Ummati ta fadi kan ta fara emotional blackmail irin  nasu na iyaye.

"Yanzu ban kai ki yi sharing matsalar ki da ni ba ko Badejo, ni Uwar da na dauke ki wata tara a cikina, ni zaki boye wa problem dinki......".

"Ba haka bane Ummati, zan fadi muku komi. So nike sai randa family din is full, in Auta ta dawo duk sai mu zauna a tattauna". Ta fadi mata.

JIRWAYE✔Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt