Babi Na Sha Shidda (16).

2.5K 263 1
                                    

Jirgin su na isa Nigeria ta tadda Yasmeenah na jiran ta. Cikin murna ta qarasa ta yi hugging din Yasmeenah.

"Ya Allah! I've missed you Yasmeenah". Ta fadi kawai ta fashe da kuka.

"Nifa dadina da ke kenan, shegen son kuka. Oya yi shuru, 3 weeks kawai fa kika yi biki ganni ba". Yasmeenah ta anshi jakarta ta riqe mata suka karaso inda tayi parking mota. Laylah na maida sim dinta na Nigeria gida ta fara kira, ta yi dialling number din umman ta.

"Ummati". Ta kira sunan mahaifiyar ta kamar yadda suke kiranta.

"Na'am ýar albarka, kin dawo kenan".

"Shigowa na Nigeria kenan".

"Masha Allah, ya aikin? Komi lafia koh?". Ummati ta tambaya ita kuma Laylah ta ansa ta da komi lafia lau. Ta tambayi Abban ta da kuma ýan uwan ta.

"Duk lafia lau suke, Abban ki nema be ji dadi ba, jiki ya dan tasan me".

Salati tayi kan ta ansa mahaifiyar ta "me ya same sa ne haka? Kuna da kudi isasshe? Zan turo kudi da na shiga gida kuma ina samun hutu daga gun aiki zan zo". A haka suka ta zance har suka wa juna sallama ta ije wayar. Duk hankalinta a tashe da taji an ce Babanta ba lafia.

Bayan sun isa gida, sai da Laylah tayi sallah sannan ta ci abinci ta huta tukun ta kwashe tas duk abunda ya faru a Australia ta fadi wa Yasmeenah. Guda Yasmeenah ta saki.

"Ahhh Lallai! Diyata akwai ki akwai goshi. Tunda nike hada Junaidu da ýan mata ba wadda ya tabawa kyauta irin naki. Amma kuma Laylah baki ji, na sha fadi miki a wannan sana'ar there's nothing like love, baa soyayya. Ke a ganin ki wa zai auri karuwa?". Ji tayi kalaman Yasmeenah sun sosa mata zuciya amma kuma ta san gaskiyar zancen kenan, ba wanda zai taba accepting dinta.

"Yanzu mance wa zakiyi da wani Abdulmalik ki fara shirin tarban next customer dinki. Na fadi miki Ali Na sidi har nan gidan ya tako kafarsa yazo yace shima yazo Laylah Jaan ta lasa mai irin nata zumar". Ta fadi mata "kuma kema kinsan kudi zasu fito jikinsa. Yanzu duk wani zancen Al-Haydar a watsar, wannan ya ma na nisa. Tunda ga wanda ke hannu sai mu kama su gam ai koh". Yasmeenah ta fadi tana taunar chewing gum. Ita kam Laylah duk ji tayi wannan rayuwar ta fita mata a kai amma kuma bata san daga ina zata fara ba.

Tunda ta dawo rayuwar ta ta sanja, ta rage fita in ba dai aiki ne ya fita da ita waje ba. Kullum bata da aikin yi sai kallon hotunan ta da Abdulmalik tana zubar da kwalla. Duk yadda take son barin wannan sana'ar ta riga tawa kanta alkawarin bazata bari ba har sai randa ta ci kudin Al-Haydar. Amma kuma yanzu da babu Abdulmalik ta wace hanya zata samu ta hadu dashi.

Shikam Abdulmalik yana dawowa sai da ya fara biya wa ya duba lafiyar dan sa kan ya wuce gida. Nawfal ya lura da dan uwan nasa, tun ranar da ya hadu da Laylah, ana gobe zasu dawo be dawo normal ba, duk ya sanja. Kwata kwata ya ma daina zancen ta, baya so kuma a dago hirar ta.

"Khalifatullah". Ya ji muryar mamansa. Matsowa tayi kusa dashi ta dora kanta a shoulder dinsa. Wani dan kiss ya dora mata a kai kan ya tambaye ta abun da ya faru.

"What's wrong Begum?".

"Duk ka sanja, wani abu ne ya faru a Australia?". Ta fadi "Ni bani son ina ganin ka haka, duk sai naji ba dadi".

Shafar lallausar suman kanta ya fara kan ya gyara murya. "Ke fa kin cika damuwa, nothing happened, everything's going well. Na kusa kama barawo insha Allah". Ya gama mata bayani kan ya tashi zai fice. Har ya kai bakin qofa sai ya juya ya kuma mata magana.

"Fadeel is moving back here next week".

"Da gaske. Jikana zai dawo hannuna". Ta miqe tana murna "Na dade ina jiran zuwan wannan ranar. Have you finally made up your mind? Akwai diyar qawata dama, yarinyar akwai hankali, nasan zata riqe mana marayan Allah tsakanin ta da Allah".

"Begum ya isa please. Ban shirya aure ba har yanzu. Kawai dai zai dawo nan ne, na fi so yana kusa dani. Yola yayi nisa".

"Kayya, for how long?, next month zaka yi 35 for heavens sake khalifa".

"Begum let's not start please. I'm stressed". Ya fadi ya wuce dakinsa wanda ke ground floor din gidan. Tun faruwar incident din Fatima khalifa ya rabu da hawa bene, koh elevator sai ya dage ya rufe ido yike shiga.

Wuni yayi ranar a cikin bedroom dinsa dun koh da aka kirasa out for dinner sai cewa yayi a kawo mai nasa dakinsa baya ji da fita. Begum ta gane cewa akwai abun da ke damun dan nata kuma baya son sharing shiyasa yike dodging haduwa da ita dan haka ita ma sai ta fita harkar sa ta basa space. Ranar isowar Muhammad Fadeel ya zo, ranar babu sukuni Al-Haydar mansion. Masu aiki ne ke ta kai komo, ana shirin isowar karamin uban gidansu. Dama already tunda Abdulmalik ya fadi wa Begum cewa Fadeel zai dawo gun su ta sa aka sake interior in dakin da yike zama in yazo hutu, aka sanja komi na dakin an siyo sabo an saka. Kayan wasa ma duk an cika dakin dashi. Har game room aka hada mai. Garden din gidan shima haka an zuba kayan wasa.

Girki kam ana ta yi iri iri, a dora wannan a sauke wancan. Duk abincin da Begum ta san yana so ta sa a dafa mai. Sai da ta tabbatar an gama komi tsaf tukun ta wuce gefen ta dun ta shirya. Tana cikin shiri taji alaman shigowan motoci.
Shima dama Abdulmalik ba inda yaje ranar, yana gida jiran isowar dan sa, tun safe ya aika one of their private jets zuwa yola ya dauko dan nasa. Yana jin qarar mota ya fito waje. Motoci ne guda 3 masu na alfarma suka yi parking a harabar gidan. Fadeel be ma jira an buda mai qofa ba ya buda da kansa ya rugo da gudu zuwa inda Babansa ke tsaye. Gudu yike yana murmushi irin na mamansa, duk sanda Fadeel yayi dariya Abdulmalik gani yike kamar Fatima ce ke dariya. Dukawa yayi qasa sanda yaron nasa ya qaraso ya rungume sa kamar zai shige cikin sa. Be san sanda kuka ya kufce mai ba. Fatima kawai yike tunawa, yana jin wani so da kaunar dan sa na dada ratsa jikinsa.

"Ab....Ab...ba". Yaron ya fadi yana numfashin sama sama sabida gudun da yayi. "Abba hayatee".

"Chuchu na..... my little tiger". Ya fadi still hugging the boy. "It's good to have you back son".

"Then stop crying, the occasion is a happy one". Ya fadi yana gogewa mahaifin sa hawaye. Yana hango Begum ya ruga da gudu ya fada mata a jiki shikuma Abdulmalik ya qarasa inda Hajjo take, tana takowa a hankula ya anshi jakar da ta riqe da ya riqe mata har suka iso ciki.

Kan ka ce me Fadeel ya fara displaying halin sa na barna da rashin ji a gidan. Yana ta faman ba masu aiki ciwon kai gashi ba daman suyi bugu a bakin aikinsu😁. Sai da Hajjo tayi 2 days a Abuja kan ta koma yola. A ranar da zata koma kam ta sha kuka dan ba karamin kewar jikan nata zata yi ba, abun farin cikin ta amma ya ta iya. Week na zagowa aka hiring teachers inda zasu dinga zuwa gida suna koya wa Fadeel karatu. A duk lokacin da Abdulmalik ya sama kansa da shiga cikin damuwa in dai ya ga fuskar dan sa duk sai yaji damuwar ya gushe, a haka dai life ya cigaba gradually duk da akai akai ya kan yi tunanin Laylah amma koh so daya be taba yunkurin neman ta ba. A cewar sa, if they're destined to meet again to komin dadewa fate will bring them back to each other.

Wata ranar sati, Abdulmalik na cikin study dinsa yana aiki daga nan ya fara lulawa duniyar tunanin sai ji yayi ana kwala mai kira ana jan hannun rigarsa.

"ABBA! ABBA!", Fadeel ya dinga ihu dama ga muryan nasa very sharp.

"Wai me? Dawo da kai gidan nan laifi ne Fadeel?". Ya tambaye dan nasa dun tun randa Fadeel ya dawo gidan Abdulmalik ya rasa sukuni, daga Fadeel yayi fitinar yana son kaza sai yayi na yana son wani abun. Gashi da shegen tsiwa da tonan fada. Da ace ba a gida ake zuwa koya me karatu ba da an sha fama dun da sai ya dinga neman fada a makaranta.

"You promised to take me out today rememberrrrrr". Ya fadi da wani irin grin da ke nuna wawulon bakin sa. Sanin halin yaron nasa ya sa ya miqe ba gardama.

"Go tell your nanny to dress you up, i'll be downstairs waiting". Sai da Fadeel ya tsaya yana imitating wai irin rawar Michael Jackson kan ya wuce dakinsa shiri. Abdulmalik kam dariya kawai ta tsaya yana ta yi.

Koh da suka isa national park and zoo be san meyasa zuciyar sa ta dinga wani irin bugu ba, kaman wani abu na shirin faruwa, something great, something amazing.

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Hi hi hi hi hi me ke shirin faruwa ne. Who likes little Fadeel, I definitely like him, he reminds me of my childhood😁😁😁. Sai mun hadu a next chapter. Xx

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now