As a celebrity, politician or a writer or better still let me just say as a public figure, fans are the ones that gives us life. In babu ku babu mu. Godia buhu buhu ga mosaya Jirwaye, Kullum ina samun messages dinku and wallah suna faranta mun rai kuma suna motivating dina to write more and now even my hausa is improving. Jirwaye appreciates your efforts, Haphsertuh appreciates your efforts also. Thanks for reading my book and ignoring my poor hausa😁😁😁
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Daukar tuxedo dinsa yayi ya mayar jikinsa sannan ya fito suka wuce. Yana fitowa bodyguards dinsa suka taho suna binsa a baya. Suna fita harabar building din daya daga cikin bodyguards din yayi hanzarin yin gaba domin buda wa Abdulmalik kofar mota. Wata Shegiyar mota aka buda mai wanda Tsayawa describing dinsa ma bata lokaci ne, kai da ka gan motar nan ka san kudi ne suke magana, iya haduwa motar ya hadu. Yana shiga abokin tafiyar sa ma ya shiga tukun bodyguard daya ya shiga motar dayan kuma ya shiga dayan motar na baya, motar escorts.
"Yawwa Tariq called me kuna meeting, yace Al-Mubaraq couldn't attend the meeting saboda abokin sa senator Junaidu na gari so they've been together".
"Meyasa Mamu ke haka? Ba sai ya kira ya fadi ba and moreover in suka koma Nigeria ai sai su cigaba da abokantansu, business ya kawo mu Australia". Ya fadi cikin bacin rai wanda Fuskar sa ke dauke da Kullum. Ba karamin abu bane ke sa Abdulmalik dariya.
Al-Mubaraq shine overall director din khalif airlines and group of companies kasancewar sa kawu a gun Abdulmalik. Shine general overseer na company din kuma shi ke tsayawa matsayin CEO a duk lokacin da ya kamata saboda Abdulmalik mutum ne mara son fame da popularity. Ko a cikin ma'aikatan sa ba duka suka san ko wanene khalifa Al-Haydar ba, sai dai su ji sunansa, manyan ma'aikatan ne kawai wanda yike haduwa dasu a meeting every six months suka san asalin shi wanene amma duk sauran Al-Mubaraq suka sani, sai dai su ji sunan Khalifa dan koh a TV ne baa taba nuna Fuskar sa sai dai ka ga Al-Mubaraq wanda bayan Abdulmalik, yafi kowa matsayi a khalif airlines and group of companies. Daga Al-Mubaraq kuma mutum na uku me babban matsayin a kampanin shine Nawfal muhammad Fadoul.
Suna isa park din yace wa escorts dinsa su bar masu mota daya su wuce.
"But sir".
"It's okay, I'll be good". Ya fadi masu "Tell Tariq to meet me here in the next 30 minutes" ya umurce su sannan suka wuce suka shiga ciki.
Yana zaune a gefe daya yana ta kallon yara na wasa yana ta dariya. Dauko camera yayi yata daukar hoto.
"I'll show all these pictures to Fadeel when I get back to Nigeria". Ya fadi a ransa. Tunanin dan sa kawai ya sa shi jin wani irin sanyi a ransa. Kawai dago kai da zai yi idanunsa ya gamu da wata ýar budurwa a can wani seat not too far from him a zaune. Tabbas! Ya san ta.
"Karbi ka riqe mun". Ya cire tuxedo dinsa da tie ya bar blue shirt din da ke ciki kawai.
"Mene haka".
"Kai dai karbi". Ya fadi tare da je fa kayan kan jikinsa. Qasa yayi da kansa yaga palms ne qafar abokin nasa sai ya saki murmushi. "Nawfal give me your shoes and take mine".
"Kai malam! Lafia kuwa? Dazun nan na sayi shoes dinnan saboda wanda na sa suna ci mun qafa".
"Just take mine yar, zasu ma daidai". Nawfal kam kai a daure ya cire takalmansa ya bawa khalifa.
"Khalifa wai me ne haka".
"Kai sarkin kauyenku! Abdulmalik nace ma. Yanzu ya ka ganni?". Ta tambaya "tsaya ka gani". Cire agogon da ke hannunsa yayi, agogo ne me matukar tsada, sannan ya cire tuck in dinsa sannan ya kuma tambayar Nawfal.
"You look like a simple person, someone from a middle class background".
"Masha Allah". Jirani. Har ya qarasa inda Laylah take zaune ya zauna bata san anyi haka ba. Daga gani kasan ta zurfafa a tunani har ýan hawaye suka fara saukowa daga idanunta. Kasancewar sa mutum me tsananin tausayi, most especially ga mata, ya tsani yaga ýa mace ta shiga wani hali, saboda wannan dalilin ne khalifa ya zura hannu cikin aljihun sa ya ciro hankie wanda ya daga hannunta ya sa mata a ciki. Tun da ya Kalle ta so daya ya cire ido a kanta. Duk sai ya qura idanunsa a kan wasu yara ýan mata biyu wanda suke ta wasa abun su.
"You!". Ya ji an fadi da karfi har sai da dodon kunnensa suka nemi su toshe.
"Na tsani naga mutane suna kuka, barin ma ýar budurwa..... kyakyawa". Sai da ya dan hanzarta tukun ya fadi kyakyawa.
'Subhanallah! I didn't check her out, did I? 'Ya fadi a zuciya when realisation dawned on him cewa he just admitted to Laylah being pretty.
"Whenever distressed, remember Allah and say Alhamdulillah. You'll feel okay" ya bata shawara sannan ya miqe ba tare da ya kuma kallon ta ba. Sai dai a zuciyar sa yana jin wani abu, abunda yayi shekara da shekaru be ji ba. Ji yike kamar wani force of attraction yana pulling dinsa towards this strange lady, ji yike yana so ya kuma ganin ta. Kawai sai ya tuna ai akwai ipad dinta a gunsa.
"Can I get your address?" Ya juya ya tambaye ta. Sai da taji dalilin son address dinta tukun ta basa. Shikuma Wucewa yayi ransa cike da tunani iri iri. Har ya isa inda Nawfal ke jiransa tunani yike, sai da Nawfal ya kwala mai kira tukun.
Sun shiga mota suna tafia ya fara tambayar Nawfal koh yasan Jk guesthouse.
"Ehhh, guest house din abokin Mamu ne ai, senator Junaidu. Nan yike sauka in yazo Australia".
"Hmm" kawai yace yana dan shafar sajen sa kamar wanda ke nazari. Hakika bayan zahra baya ganin zai iya taba son wata ýa mace amma kuma ya rasa meyasa tunanin wannan yarinyar ke ta addabar sa, duk yaji yana so ya san koh ita wacece.
"Shi senator yana da wata diyar koh niece a country dinnan?".
"Gaskia I don't think so, but I'll find out".
"Okay do that" ya fadi "and please Nawfal shopping nike so ka mun, kaya masu araha. Banda masu tsada". Ya fadi.
"Wai kai mai motive dinka na boye identity dinka, meyasa baka son mutane su san ko waye kai, gashi dai kana taimako, mutane suna son su nuna godiyar su gare ka amma ba dama".
"Ni duk abunda nike yi dun Allah nike, and I'm going undercover ne to know who my friends are and who my enemies are. Very soon the world will come to see the true face of khalifa Al-Haydar" ya fadi. Sun dade ba wanda yace wa kowa komi sai can Jim kadan Nawfal yayi breaking silence din.
"Chuchu wanted to talk to you in the morning amma nace baka kusa".
"Shine baka fada mun ba tunda na dawo" ya fadi ransa a bace. Wayar sa ya dauko ya fara neman number din Hajjo.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Hahaha haha haha how many people did I manage to mislead? So Khalifatullah da Abdulmalik mutum daya ne. Me kudi amma yana yawo kamar talaka mara komi. No wonder yaqi sanda mamansa tace zata kaisa airport, Hmmmmm Laylah ta hadu da Khalifa Al-Haydar bata san shi bane, ya kenan? Ya zasu kwashe. How will khalifa feel in ya gani true colours din Laylah, still dai ku biyo ni a Jirwaye ku sha labari. Xx
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...