Ina kike qawata, yaya ta, mahaifiyar Habibi na...... wannan chapter din naki ne, ke daya auntie Zubaidah na (umm Haidar). I hope you enjoy it.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
A hankula ta buda kofar ta shiga. Wani mutum ne zaune a kujera, a wulakance bazai wuce yana late 30's dinsa ba koh early 40's. Da ka gansa ka ga naira da hutu, ba zaa kirasa mummuna ba at the same time kuma ba wai irin wannan tsinannen kyau garesa ba, he's just okay. Cike da murmushi ya tarbeta.
"Ýan mata sannu koh". Ya fadi yana mata wani kallo wanda yayi shige da irin kallon da uncle Mukhtar ke mata.
"Yallabai ina yini". Ta rusuna tana gaida shi cike da girmamawa.
"Yawwa malama sannu, Bismillah zauna mana". Ya fadi. Jiki na rawa ya buda fridge ya dauko juice ya ije mata. Ita kam Badejo sai mamakin fara'ar mutumin take dun tun jiya Baba Haruna ke fadi mata ba wani mutunci ne da boss ba. "Toh me ya kawo ki?". Ya tambaye ta.
"Aiki nazo nema". Ta fadi kawai taga ya fashe da dariya.
"Aiki? Toh kina da takardun ki?". Ya tambaya tace mai aah ita shara ma take so dun ba takardu gare ta ba, koh school cert bata da.
"Amma kinga shara be kamaci yarinya tsaleliya irin ki ba. Kinga ki a mudubi kuwa. Ba wanda ya taba fadi miki kina da kyau?". Ya tambaya tayi shuru. "Kamata yayi ace kin zama secretary na, post din zai an she ki sosai".
"Da gaske". Ta dago kai tana kallonsa da ýar murmushi. Gani tayi ya lashi labbansa yana mata murmushi.
"Ehh mana, kuma albashin ya fi tsoka". Ya fadi mata. "Amma kuma gashi baki da takardu".
"Toh ai matsalar kenan". Ta fadi tana dan tabe baki. "Ni dai kawai in zan sama sharan falillahil hamd".
"Kinsan ya zaa yi, naga kina da hankali, kuma kin kwanta mun a rai. Goro kawai zaki ban na baki aikin, a matsayin secretary na".
"Kai haba! Goro wannan, toh bara nai maza na je na siyo". Ta miqe tana fadi. Har tayi hanyar qofa ya tsayar da ita.
"Ke dawo, ba wannan goron nike nufi ba".
"Toh wanne?".
"Zauna man tukun". Ya fadi mata "wato kinga koh, ke yarinya ce me matukar kyau, ga ki da elevations; front and back. Kin hadu wallahi, kamar hadari. I just want a glimpse through your veil. Kina jin turanci ai koh".
"Ehh ina dan ji amma fa ban gane zancen ka ba".
"Kin gane koh, guesthouse dina ya kamata muje, ki huta mu dan shakata. Gobe sai ki fara aiki. Albashin ki dubu sittin". Salati kawai Badejo ta saki, wai ita meyasa duk mazan da take haduwa dasu ke neman ta da alfasha ne, ba me so ya taimaka mata fisabilillah. Duk jikinta suke bi. Hakika kyau ma wani lokacin in yayi yawa ya kan zamo jaraba.
"Aah nikam, bazan iya ba".
"Haba ýar gari, so daya fa kawai. Ai ke ba kalar talaka bace ba wallahi".
"Amma ni ýar talakawa ce, a cikin ta na tashi, a kauye kuma Kullum cikin godiyar Allah nike".
"Baki so ki bar rayuwar kauye? Baki so ki zama big girl. In biya miki hajji da umrah, in kaiki India mu huta. Da mun dawo na turo gidanku". Ya fadi, all in an attempt to convince her "kinji ýar budurwa, so daya kawai, bazan bata lokaci ba. Kan ki sani munyi mun gama".
"Auzubillahi min nas-shaydanir rajim". Ta fadi "Ka cinye aikin ka baa so, Allah shine gata na, bazan saba mai ba dun biyan buqata ta". Ta miqe ta wuce shikam ya ja tsaki yana zagi.
"Shegiya, da kafafun ki zaki dawo. A ina zaki sama aiki a sama in Abuja. Koh ba nan ba sai kin sayar da Jikin ki can wani gun". Ya fadi kan ya cigaba da aikin sa.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...