Babi Na Shidda (06).

3K 296 13
                                    


Kallonsa doctor din yayi cike da tausayi, ya matso kusa dashi ya dafa mai baya. Kasancewar sa family doctor dun Al-Haydar family yasa shi da Abdulmalik suka shaqu.

"Khalifa, you're a Muslim and I'm sure kasan qaddara. Kasan kuma ladan mutum wanda ya rungumi qadr; me kyau koh mara kyau.....". Be gama statement dinsa ba Khalifa ya katse sa.

"Fatima fa? Fatima na fa? I want to see her, this minute!". Ya bangaje doctor din ya ruga dakin da take da gudu.

"Time of death.......... 9:21pm". Kalaman da suka fara dukar kunnunwansa kenan da shigar sa dakin. Dago idanunsa yayi wanda sun dade da zama jazur, ya kalli dayan doctor inda ke dakin da wata nurse a gefen sa ta na rubutu a notepad. Ya kuma juya ya kalli zahra sa wadda take kwance, idanunta a rufe kamar me barci. Ji yayi an riqo sa amma ya sa hannu ya hankade wanda ya riqe sa, be ma damu da ya juya yaga ko wanene ba kawai ya nufi gadon da zahra sa ke kwance.

"Habibty..... ki tashi barci. I'm sorry you had to pass through all these pain just to have my baby. Na qosa na ganshi, naga da wa yayi kama amma in ba tare da ke ba bazan iya zuwa ganinsa ba. Dan Allah tashi muje muga dan mu, kinji zahra na". Ya gama magana yana jiran yaga ta buda idanunta da yike matukar son kallon su a ko da yaushe amma yaji shuru.

"Hushi kike dani har yanzu? I'm sorry habibty, please wake up". Wannan karan ya jawo hannun ta ya riqe a cikin nasa yana wasa da ýan siraran ýatsun ta.

"Sir you have to take it easy on yourself". Wata nurse ta matso kusa dashi tana fadi amma sai tsawa kawai ya mata, ta tashi ta basa gu.

"Ki daina sa mun baki, i'm talking to my wife. Get out!".

"Zahra dan Allah.......". Be gama maganan ba wasu maza biyu suka shigo suna jawo sa waje shikuma yana kokarin fisgewa. Yana kallo wasu nurses suka kawo auduga suka sa ma Fatima a hanci, aka hada Jikin ta yadda ake wa gawa. Subhanallah! Ina zai mance, 7 months ago a idanunsa haka aka wa mahaifin sa. Wani irin kuka ya saki me shiga zuciya, ya zuba gwiwa a qasa yana kuka yadda ka san yaro karami. Duk mutanen da ke cikin dakin tausaya masa suke. Kowa ya kasa ce mai komi dan a wannan lokacin shi daya ya san yadda yike ji da kuma Allah wanda ya halicce sa.

"Fatima why..... why did you leave me. I told the doctor to save you for me. Why! Ya Allah sai da na fara son ki Fatima, sai da zuciya ta ta saba da ke, sai da idanuna suka zama addicted to seeing your face Fatima. What will I tell our son, what will I tell your Fadeel? Dan Allah Fatima ki tashi". Yayi ta kuka har kalaman sa suka sa wasu daga cikin wanda suke gun hawaye. Hakika yaji wannan rashin da aka mai.

Da kyar aka samu aka ja sa out of the room. Shikuma doctor already ya kira family dinsa ya sanar dasu mummunar abunda ya auku. Can yana zaune shuru a corridor in dakin da gawan Fatima yike sai ga ýan uwansa da na Fatima sun shigo. Hajjo na hada ido dashi ta farke da kuka.

"Fatima ashe ban kwana kika zo mun yau. Shiyasa kika ta hugging dina, kina ta kallona. Harda mun addua Fati na. Wayyo ni". Tai ta kukan ta ana bata haquri. Ita kanta mahaifiyar sa kuka take, sai dai amma tana da karfin hali, ita tayi ta fama bawa dan nata da surukarsa haquri. A nan dai close family members suka taru, masu kuka suna yi, masu suma nayi duk dai gu ya kidime. Shi dai Abdulmalik baya cikin hayyacin sa dan duk a gigice yike. Yaya Fu'ad ne yayi ta cika formalities din Asibiti kan aka gama suka tafi da gawar domin ayi mata sutura a kai ta makwancinta. A lokacin da zaa tafi ne ma aka tuna da dan jinjirin data bari wanda baza su iya tafi dashi gida ba. A nan dai aka cewa Hajja Ganah ta zauna da baby din kan a san yadda zaa yi. Ita Hajja ganah kanwa ce ga mahaifiyar Fatima.

Cikin kankanin lokaci duk an sanar da ýan uwa mummunar abunda ya samu Abdulmalik. Ana daukar gawar daga Asibiti gidanta aka kaita. Kasancewar da dare ta rasu, sai da aka jira wayewar garin Allah tukun aka yi janaizar ta. Har a wannan lokacin Abdulmalik baya cikin hayyacin sa, duk ya sanja, ya zama wani iri da shi, mutuwar ta taba sa ba kadan ba. Da kyar aka iya lallaba sa yaje yaga dan sa yayi mai khutbah da Tahneek. A ranar kam ya ci kuka, duk wanda ke gun ma sai da suka sha kuka saboda ya basu tausayi matuka.

"Da na bansan me zan ce maka ba, ban san da wani ido zan Kalle ka ba a ranar da zan tsinci kaina da baka wannan mummunar labari, cewa mahaifiyar a ranar da ta haife ka ta rasa ran ta. Ban sa ta ina zan fara ba, ban san ta ya zan tarbiyyantar da kai ba without your mother by my side. I don't know what the future holds cause right now I can't even see the future, I don't know what it has in store for us. I'm sorry I could do little or nothing at all to save your mother, I'm sorry you'll have to grow up without a mother, i'm sorry.... For everything son. Forgive your father for he is nothing but a mere mortal. All I can promise you is that I'll always be there by your side son, it'll always be us, you always nd is against the world. Even though it would not make up for your loss, I promise to give you all the joy and happiness in the world". Kawai bai san sanda kuka ya kufce masa ba, tuna lokacin da yike gardama shi da Fatima takan sex din baby dinsu kawai yike.

"You were right zahra, we now have a little boy, our son. Your Fadeel. Allah ya raya mun kai ďa na muhammad Fadeel". Ya tofa mai addua yayi hanzarin fita daga dakin idanu cike da hawaye. Bayan ýan watanni da rasuwar Fatima, anso Abdulmalik ya auri cousin sister dinta, Salma wadda ita da zahra tare suka tashi. Kasancewar Fatima the only girl ya sa Hajjo ta dauko Salma tun tana ýar yarinya ta tarbiyyantar dasu tare. Aka yi akayi ya aure Salma dun ta kula da Fadeel amma yaqi. In ba zahra sa ba, be ga ýa macen da zai taba zama da ita ba a doran qasa.

"It's either my zahra or no woman at all". Ya fadi.

Bayan sallamar Fadeel daga hospital aka sama mai nanny ya fara zama da family din Abdulmalik, wato mahaifiyar saboda Abdulmalik ya kasance shi daya tal aka haifa kuma ga arziki da Allah ya azurta iyayen sa da shi kamar me. Duk duniya an san khalif airlines and group of companies. Babban business empire ne wanda ya sama karbuwa da kuma support from different countries round the globe. Kan rasuwar Mohammed Mumtaz Al-Haydar, ya kasance mutum ne me fada a ji, yana da influence matuka a siyasar qasa da kuma business world ma in general. Bayan mutuwar sa kuma shi ne dan sa Khalifa Abdulmalik Al-Haydar ya gaje sa.

Bayan ýan watanni Hajjo tazo ta roqa dan Allah a ba ta jikan nata ta riqe, ko ganinsa zai dinga debe mata kewar diyar ta.

"In ya so duk randa Khalifa ya sama mata yayi aure sai na dawo masa da dan sa". Amincin da ke tsakanin both families ya sa Khalifa ya yarda ba tare da bata lokaci ba.

Back to present.......

"Khalifa!" Yaji an kira sunansa da qarfi "Tunanin me kake yi haka ne". Dago ido yayi ya kalli me magana.

"Nace ka dinga kirana Abdulmalik if we are in an office environment. At home you can call me Khalifa all you want".

"Yes boss". Ya fadi yana salute. "Ya kake? Done with the meeting?" Ya tambaya, Abdulmalik be ce mai komi ba ya gyada kai alamar ehhh.

"Ka zauna kana ta tunanin ta koh?".

"Let's go to the park". Ya fadi ba tare da ya ansa tambayar da aka masa ba.

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Toh jama'a....... who is confused here, hands up in the air dun ni kai na a rude nike. Ga Khalifatullah ga Khalifa Abdulmalik. Toh daya dai kamar me dan rufin asiri haka daya kuma me shegen kudi. Ikon Allah! And they're both in Australia, gashi Laylah na neman daya, shikuma daya ya hadu da Laylah. Me ke shirin faruwa ne? Wane zuciyar Laylah zata so? Me kudi koh me rufin asiri? Wanne a cikin su zai yi accepting Laylah for the person she is. Allah kuma zai sa da ta da Khalifa Abdulmalik Al-Haydar? Domin burinta kenan for years, ta gansa, ta mai tallar jikinta. Hmmmm na gaji da surutu, kawai ku biyo ni a chapter na gaba muga ya labari zai cigaba. Wa ke son ya ji yadda Laylah da senator suka karashe? Ku biyo ni. Thanks for reading. Xx

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now