Khalifa na isa gidan ya zauna shuru mafarkin da yayi nata masa yawo a kai. Gaba daya yayi loosing focus yama mance da wani daurin aure, har lokaci ya fara wucewa. Ya fi one hour yana zaune shuru kan ringing din wayar sa ya katse masa tunani. Sai da ya duba caller identity din yaga Nawfal ne kan ya daga wayar ya kafa a kunne.
"Where are you man? Begum is about having an attack, duk hankalinta a tashe".
Khalifa be bi ta kan question din Nawfal ba kawai ya fadi masa abunda ke ransa. "I don't think I can do this Nawfal. Saima is not the one I want.... Laylah is". Ya fadi a hankula.
"Then go to her". Nawfal ya basa ansa.
"The wedding... Begum... Saima... media, so many factors Nawfal ban san yadda zan yi da raina ba". Ya fadi kan ya fara mayar wa Nawfal mafarkin da yayi. Dogon numfashi duka su biyu suka ja bayan khalifa ya gama narration dinsa.
"I'll send Tariq, get ready. I'll call the pilot to get the jet ready. You leave for yola immediately! Immediately khalifa, babu time".
"Aah Nawfal, kaima ka san I'll have to make Begum understand and Saima too".
"A minute delay could change things khalifa..... It's better you go. Begum will stick to her words in dai kana nan. Don't worry, I'll take care of things here. Just do the right thing. Yanzu I'll pack some things for you Tariq ya taho dasu, ka kashe duka wayoyin ka, go go.... go get your lady". Nawfal yayi ta ba khalifa karfin gwiwa. Suna gama waya Nawfal ya kira Tariq suka yi magana ya fadi masa what he has to do daga nan kuma ya kira land line din guest house dinsu da ke can yola ya basu umurni da su gyara wuri immediately sannan a shirya motar da zai je ya dauko baqo. Nawfal be nuna musu khalifa ne zai zo ba dun it was all over the press, daurin auransa.
In less than an hour sai ga Tariq ya iso, shi da kansa ya tuqa su zuwa airport, khalifa shikam yana zauna shuru be cewa kowa komi ba har jet dinsu yayi landing yola!.
"Sir where do we go?". Tariq ya tambaya. "I've gotten her address".
"Then what are we waiting for?".
"Baza ka huta ba?".
"Ba wani zancen hutu Tariq, but I need security". Ya fadi. Nan da nan Tariq yayi making phone call da commissioner of police aka providing musu maximum security. Kan ka ce me an hada convoy na 9 cars, when I say cars, I mean motoci masu ansa sunansu motoci ba qarafuna ba😂. Koh da suka isa gun gidansu Laylah, izza area din suka yi rowdy ga number din gidan da aka ce musu nan ne gidansu Laylah ya cika fal da cars and jama'a. Wani dan saurayi Tariq ya sauke window yayi wa sallama sannan ya tambaye sa me ke faruwa gidan.
"Auran diyar gidan ake". Yaron ya ansa. Khalifa na jin haka be ma bar Tariq yayi magana, da kansa ya tambaya wacce aciki? Dun a iya sanin sa, Laylah sister daya gareta dal! So if it's not her sister then it's....
"Wadda ke zama can Abuja, na mance sunanta. Bata dade da dawowa yola ba". Saurayin ya ansa. Kallon kallo suka fara ma juna, khalifa na kallon Tariq shima Tariq din khalifa yike kallo.
"Sir... what do we.....".
"I've come too far to stop now Tariq, get into the goddamn house. NOW! Tell the goddamn security dude to let the gate open!". Yayi wa Tariq tsawa. Kallon agogon hannun sa yayi yaga it was already past 2, sai kuma yaji hankalinsa ya koma can Abuja. Ya kamata ace an daura auransa by then but ya zasu yi in ba ango? How will Nawfal calm everyone down. Yana cikin wannan tunanin aka buda gate din gidan, convoy dinsu suka sa kai sai shiga kawai suke. Now let's hear from Laylah. Allah sa dai khalifa isn't late.
The next morning da wani throbbing headache Laylah ta tashi all thanks to rashin barci da kuma kukan da ta sha cikin dare. Duk throughout that morning she was moody, Yasmeenah kam tana ta lura da mood dinta, abun na ci mata rai yadda take ganin Laylah haka. Ji take kamar taje ta sama su Ummati tace musu dan Allah a fasa wannan auran saboda Laylah ba wai tana so bane. After zuhr salaah masu kunshin da aka dauko all the way from Sudan suka iso. Already dama an riga an gama gyara terrace din saman gidan a inda ake so ayi kunshin. The place had a traditional ambience to it, koh ina kaskon wuta ne an kunna bukhoor, ga tum tums an zuba ta ko ina, wuri yayi kyau. An sanya amarya a tsakiya an fara mata lalle, sai kuma wasu masu lalle guda 4 da suke ma kawayenta, ga masu kidan kwarya nan suma sun zauna ana ta kida ana rawa. Everywhere was looking amazing. Ita dai amarya sai fake smiling take ta yi dun ranar ta tashi with a very heavy heart, all because ta san daga ranar ta rasa khalifa Al-Haydar har abada. A ranar zaa daura masa aure to his Saima. Koh da ta ji ana cewa an sauko sallar jumu'ah wani baqin ciki taji dun ta san by that time, the deed has long been done.
YOU ARE READING
JIRWAYE✔
General FictionKhalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi. Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi. Labarin su ba kaman labari bane nayau da...