Babi Na Sittin (60).

2.1K 260 10
                                    

"And this will be your room". Sahar ta fadi cike da fara'a. A hankula Adama ta shiga tana kallon dakin. Babba ne, ya kusa girman gaba daya gidan Babanta can Borno. Sosai ta saki baki tana ta mamakin haduwar gidan, wani abu ma sai da ta buda bathroom taga yadda yike, gashi most abubuwan bata iya amfani dasu ba. Komawa tayi gefen gado shuru ta zauna tana nazari. Yanzu kwana nawa zata zauna da wannan bayin Allah kan su gaji da ita su kore ta? Me zata yi da wannan cikin da ke jikinta? In ta haifa yaron fa ya girma yana tambayar ubansa ya zata yi? Ya zancen karatun ta? Ýan uwanta kuma fa? Kenan baza ta sake ganin su. Wannan tunanin shi sa ta fashewa da kuka. Sahar wadda ta shigo bata kayan sawa ta izza ta tana kuka. Da hanzarin ta ta qaraso ta hau rarrashin ta.

"Ina ma wannan cikin ya fita a lokacin da kuka buge ni. Me zanyi da yaron? Me zan ce masa in ya tambaya ubansa". Take fadi tana kuka. Rarrashin ta Sahar ta cigaba da yi a zuciyar ta kam tana murna cewa ga bisa duka alamu shawo kan Adama ta basu abunda zata haifa zai zo da sauki. Sai da ta tabbata ta Kwantar hankalinta tukun ta fita ta wuce kitchen yin girkin yamma. Bayan sun gama cin abinci ne Mumtaz ya kirawo Adama domin zantawa da ita.

"Uhmm na san kina so kiyi karatu. Kuma na san kina so kiga abunda zaki haifa ya samu karbuwa a al'umma". Ya fadi kan ya tsaya yayi noticing expression dinta.

"Ba sai munyi boye boye ba. Adama kina sane da matsalar mu na rashin haihuwa. Kawai so muke ki bamu abunda zaki haifa mu kuma munyi alkawarin kula da ke. Ci, sha, tufafi, karatu da komi. Duk wani abunda kike so na more rayuwa zamuyi miki". Duk yadda Adama ta kai ga rashin son cikin da ke jikinta sai da taji wani iri a zuciyar ta. Ganin yadda fuskar ta ya sanja ya sa Sahar tayi sauri ta kwace maganar daga hannun mijinta.

"Adama ba wai zamu raba ki da abunda zaki haifa bane. Koh kadan, zaki zauna da mu amma yaron zai zama a sunan namu. Babu wanda zai sa ni, kinga a haka asirin ki da na abunda zaki haifa a rufe, ba wanda zai kira yaron ki da sunan shege koh Shegiya. Kuma kulawa da jin dadin rayuwa iya gwargwado duka ku biyu zaku samu, ki Kwantar da hankalin ki kiyi tunani zuwa gobe da safe". Sahar ta fadi tana mata murmushi. Sahar Bata bar Adama a haka ba. Har dakinta ta bi ta ta dinga hure mata kai, tana ta kokarin convincing dinsa. Lady luck smiled upon the helpless couple dan bayan nazari sosai Adama ta ga cewa abunda zata haifa zai fi samun kula da rufin asiri in ta basu, kuma sannan ita kanta zata samu kulawa, zata cika burin ta na neman ilmi. Hakan ya sa ta yarda zata basu abunda ke cikin ta bayan ta haife sa. Ranar kam murna wajen Sahar baa cewa komi. Kan ayi sati duk ýan uwa am bi an fadi musu cewa Sahar ta sama ciki, kowa sai murna ake taya su. Finally after 10 good years Allah ya ansa Addu'ar su. A haka Mumtaz ya kirkiro business trip ya kwashi both Sahar da Adama zuwa can kudu, can port harcourt bayan sunyi Karyar cewa anyi masa transfer ne.

Haka rayuwar su ya cigaba da gudana, kulawa sosai Sahar ke bawa Adama, yadda Kasan kwai haka suke treating dinta. Sosai take jin dadin zama da su dan basu nuna mata tsana koh bambanci, gashi yadda suka dau so da kulawar su suka dora kan abunda ke cikin ta. Ba randa dayan su baya fita be dawo da abun wasa ba koh rigar yara sai dai kash! Kana naka Allah na nasa, safiyar wata ranar lahadi, a lokacin cikin Adama nada wata shidda ta tashi ranar da wani mugun ciwon ciki, har zuwa rana da suka ga ciwo ba sauki aka kaita hospital a nan ne doctor ya fadi musu cewar dan da take dauke dashi ya rasu a ciki kuma dole ayi aiki a cire kan ita ma uwar a rasa ta. Sosai Sahar tayi baqin ciki, dan har ta fi Adama baqin ciki. Kwana da Kwanaki ta dauka tana kuka, gaba daya hopes dinta had just been dashed, they died along with the baby.

Adama na gama jinya Mumtaz ya tattara ya maida su kano a inda tun kan su dawo labari ya zagaya ýan uwa cewa Sahar tayi rashin cikin da take dauke da shi. Sosai aka dinga tausaya mata bayan sun dawo. Haka mutane suka dinga bata baki cewar in no time Allah zai kawo mata wani cikin. Rashin cikin be sa Sahar koh Mumtaz sun sanja towards Adama ba, a Kullum shaquwar ta da Sahar qaruwa yike dan da ka gansu tamkar siblings gashi dama Adama ita ma Allah ya mata matukar kyau, farko da suka dauko ta rashin kulawa ya hana kyaun ta fitowa amma yanzu da ta zauna da su, tana samun adequate care kyaunta ya matukar fitowa, ga figure me kyau da Allah ya bata, irin wanda ke saurin dauke hankalin opposite sex. Ga wani dan dimple da ke fitowa both cheeks dinta in tayi murmushi koh dariya, ga tsawo da Allah ya bata wanda trait ne na mutanen da suka yi originating from Maiduguri. In one sentence, Adama was a woman all women loved to hate saboda irin kyau da Allah ya bata ga baiwar iya magana cikin muryar ta da ke da shegen zaqi (kamar nawa a nan😉). In tsaya describing irin kyaunta ma bata time ne so I'll leave my readers to their imaginations.

JIRWAYE✔Where stories live. Discover now