Babi Na Talatin Da Bakwai (37).

2.6K 349 50
                                    

JIRWAYE........ The Stained Veil!

An Engausa Story By Haphsertuh

The chapter today is for you AbdulazizAminatu. I'm wishing a prosperous life full of happiness and lots of success plus subhanahu wata'alah's never ending Noor,  khayr and rahma. Have a blast dear!

Babi Na Talatin Da Bakwai.

Zainaba kam tunda maganar auran Mahmoud da Laylah ya iso ta ta rasa sukuni. Duk ta bi ta rasa kwanciyar hankali, ba kadan hankalinta ya tashi ba dun ta san Laylah is a strong competition. Duk abunda take tunanin tana dashi Laylah ta fi ta dashi. Dun haka ita da mahaifiyar ta da kawaye aka ta shige da fice gidan bokaye da malamai, neman asiri har Maiduguri, duk dun a fasa biki amma ina Kullum sai Matsowa kusa time yike, ga shirye shirye ana ta yi ba dare ba rana. Tsohon gidan da suka zauna Mahmoud yayi renovating ya dawo kamar sabo, daidai standard din wanda suke ciki a yanzu, a nan Laylah zata zauna. Unguwar ba nisa da unguwar da zainaba take. Da ka gansa yanzu kaga hutu da kwanciyar hankali, dun kusan Kullum in ya tashi aiki sai ya bi gun Laylah kan ya shiga gida kuma tafi basa kulawa fiye da matar sa da ke gida wanda ba abunda da ta iya daga gulma da kawaye sai kallon zeeworld and telemundo, going from one wedding to another, aikin kenan Kullum. Batawa cikin ta ta ci ba, bata yi wa yaran ta sun ci ba bare wani miji. Koh su yaran suna jin dadi in Baban su yace zai kai su weekend gun auntie dinsu because tana basu full attention dinta, tana bata su sosai. Kan a maida su gida sai ta tabbata an sake musu sabon hair do, an gyara su tas. Hakan nayi wa Mahmoud dadi matuka.

Ita kam zainaba sabon mota ya sake mata ya mata alkawarin kujerar hajj duk wai cikin compensation da ake ba mata in zaa yi fadin kishiya banda kaya da siya mata amma duk wannan didn't calm her down, ita kawai a fasa bikin shine burin ta.

Wata ranar Monday very early, after tayi dropping yara a school kawai tayi zooming off to GRA inda gidansu Laylah yike. Bakin gate ta dinga manna wani mahaukacin honk har sai da security man din ya buda mata gate ta shiga. Bata ma tsaya ta gyara parking ba ta fito daga cikin mota sai ihu take tana approaching main entrance din gida. A makeken living room inda ke downstairs ta tsaya tana ta fuming sai Ummati ta shigo cike da damuwa a fuskar ta tana lafia?.

"Ina take, ina wancan Shegiyar Karuwar take!".

"Subhanallah! Me zan ji haka ni Rabi'atu". Ummati ta fadi tana mamakin wai zainaba ce ke fadin haka.

"Dallah rufe mun baki tsohuwar banza, har da ke ai. Shegiya baqar munafuka! Ni din da kike fadin kin dauke ni tamkar diya shine zaa hada baki dake a cutar da ni dun iya shege. Ban barin gidan nan yau wallahi sai na ci wa wancan Karuwar diyar take mutunci. An je an gama yawon karuwanci an kwaso cuta zaa zo a liqa mun..... inaaa bazan yarda ba". Zainaba ta dinga, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

Shima Abba hayaniyar da ya ji yayi yawa ne yasa yace wa yaron da ke kula dashi in Ummati bata kusa ya tura wheelchair sa zuwa main living room din gidan yaji dalilin wannan hayaniya da sanyin safiya. "Ke Baiwar Allah Meya faru". Ya tambaya a hankula.

"Dallah rufe mun baki, tsohon banza. Shiyasa a haka zaka dawwama akan kujerar guragu. Mutane ne ba abunda kuka sa gaba sai kwadayi da cin amana toh wallahi sama tayi wa yaro nisa. Duk na sha karfin ku, sai ma na hadu da wancan annamimin, baqin munafiki mai halin ýan wuta, sai kace ba da shi aka zo neman aure na ba amma yanzu dun gulma ya dau gwalgwajin kanwar sa ya jonawa mijina, kun rasa yadda zaku yi da ita kawai zaku liqa masa. Waya ce muku shi bola ne da kowa zai iya watsar da sharan sa?". Ta dinga, Ummati dai tana tsaye tana ta kallon ikon Allah.

Laylah kam hayaniyar da ta ji yayi yawa ne ya tashe ta, miqewa tayi ta zauna kan gadon ta ta rasa reason for the noise so early. Da taji shuru noise din sai qaruwa yike kawai ta dau dan karamin hijaab dinta ta sanya ta fito. Koh da ta sauko taga masu aikin gidan sun taru ga iyayenta nan, ga kuma zainaba sai maganganu take fadiwa mahaifiyar ta. Cikin hanzari ta qaraso.

JIRWAYE✔Onde histórias criam vida. Descubra agora