2

7.6K 278 2
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

          ~NA~

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

  بسم الله الرحمن الرحيم

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO  UNDER AGES , SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

2

Bayan sun gama biyan buk'atar junansu gaba d'aya suka zube akan  gadon kowannesu yana mai da numfashi, ahankali ahankali hannun shi yakai bayan ta yana shafawa tare da lumshe idanunshi, ya matso jikinta sosai  ya rungumeta yana sake shafa bayan ta da sumar  kanta, cikin wata irin kasalalliyar muryarsa  yace " buk'ata ta biya ko?

Kanta ta d'ago suka had'a ido, suna kallon kwayar idanun junansu ta lumshe masa kyawawan idanunta masu  tattare da tsansar alamun gajiya.
  murmushi yayi mata tare da  kashe mata idonsa  d'aya, kanta ta cusa cikin k'irjinsa,tana shakar daddaden kashin turarensa  a hankali ya mik'e tare da ita,a jikinsa  yayi bathroom da ita, wanka sukayi suka fito tare, bayan sun gama duk wani abu wanda yazama na al'adarsu yayin kwanciya bacci, ta rungume mijinta suka kwanta, shi kuma yaja musu husky  blanket ya rufe su, asuba ta gari,Zarah & Naseer.

A b'angarin Kausar da Fahad ma haka abin ya kasance suna komawa gida, Kausar tun a parlor ta had'e bakin ta dana Fahad, shi mamaki ma abin ya bashi duk ta haukace masa, lokaci d'aya da rawar jiki take tsotsar bakinsa shiko yayi sororo, bakinta ta cire daga cikin nashi ta d'an kalle shi, ganin shima itan yake kallo yasata turo baki ta sake shi,
ya gane fushi tayi dan haka yayi saurin rik'ota, zatayi magana ya had'e bakinsu

Washe gari da safe kowacce ta gama shirya mijinta tsaf, tun kafin Abdul ya gama shan tea yaji horn murmushi yayi ya aje cup d'in hannushi  ya mik'e tsaye.
da ido Yasmeen ta bishi tace " ka gama mana, kallonta yayi had'i da rungumo ta jikinsa, yayi mata kiss yace " sorry dear bazan iya barin su a waje suna jira na ba kuma kin san ba shigowa zasuyi ba.

Har bakin mota ta raka shi, rungume a jikinsa, Zaid yace " chew gum ai ki kyale shi ko, dariya tayi ta gaida su, suka amsa dukansu d'auke da murmushi a face d'in su, ya shiga mota suka nufi office.

Da gudu mai gadi ya hangame get, suka shigo, suna shigowa ne Ammar yaga wani matashin saurayi rakub'e a waje, bayan sun fito daga motocin su, saurayin ya mik'e da sauri  ya shigo da gudu kafin mai gadi ya rude get, din aiko cikin zafin nama, wani soldiers,  da sauran jami'an tsaro sukayo kanshi, sun 200 suka zagayeshi da bindiga.

Murya saurayin ya d'aga yace " please ku taimake ni, kuban aron 5mnt kawai dan girman Allah, kallon mai gadi Ammar yayi yace " waye shi?

jikin Baba mai gadi na rawa yace " wallahi ban san shi ba, amma yakai sati biyu kullum yana zuwa tun asuba har ku tashi daga office wai yana san ganin ku, ni dai na hanashi shiga.

Kallan kallo suka farayi a tsakanin su,sannan a hankali Fahad ya d'aga musu hannu alamar su kyale shi ya k'araso,   duk da Fahad ya bada umarnin a kyale shi ya shiga sai da security suka caje shi tsaf, da gudu ya k'araso inda suke  ya zube a gaban su, yace" dan girman Allah alfarma nake nema a wajenku.

Babu wanda yayi magana da ido kawai suke binshi, dashi yaci gaba da mgn muryarsa na rawa  " na had'a ku da girman Allah ku taimake ni, nayi hira da ku a gidan TV na, tsaki Abdul yaja yace " u are fool, saurayin yace " yes Sir, wallahi ogana nayiwa laifi yace idan ban nemo labarin dazai k'ayatar da al'umma da girgiza ZUCIYAR jama'a ba zai kore ni daga aiki, gaba d'aya suka juya suka nufi office, Khamal yace " idan ya koreka kazo zamu baka aiki yayi maganar suna ci gaba da tafiya.

Saurayin yace " no Sir tun ina yaro nake da burin zama cikkekken d'an jarida, mahaifiyata tasha fama da wahala matuk'a dan ganin cikar burina, please ku taimake ni, kada  burina ya ruguje...yakarasa fadar Haka tamkar zai yi kuka sosai ya marairaice musu yana rokonsu  .. please kodan k'anwata guda d'aya tak data rage min, idan aka korini gurin nan bansan yadda rayuwarta zata kasance  ba. Ni kadai gareta duk duniya batada kowa sannan bazan iya jurar yin wani aiki ba byn wannan danake yi  .nasha jin yadda tausayi da karamacinku yake Ga al'umar  garin nan narokeku dan Allah Ku tallafawa rayuwarmu ni da kanwata  nacigaba da aikin nan domin taimakawa rayuwar  kanwata datayi min saura a duniya ....yakarasa mgnr hawaye nabin kuncinsa ..

Tun sanda kyakyawn saurayin nan ya fara mgn suka tsaya Cak gaba d'ayan su, suna kallonsa da jin wani irin tausayinsa dukan su suka k'urawa Naseer ido suna kallonsa , ga mamakin su.
sai sukaji Naseer yace " kayi sanarwa ko ina, kace ranar Friday zuwa Sunday zamu bada labarin kana iya gaiyato 'yan gidajen TV, radio, ku same mu a babban hall d'in 6's STAR HOTEL, daga 12:00pm zuwa 4:00pm, yana kaiwa nan ya juya ahankali  ya shige office dinsa  sauran 'yan uwansa suka take masa baya, suna shiga ciki gaba d'ayan su suka rungume juna cike da murna.

Sosai Abdul yake kuka dan gaba d'aya d'an jaridan ya tuna masa da baya.
, hankalin 6's STARS gaba d'aya a tashe yake,da ganin yanayinsa dukkan su, kukan Abdul ya sasu kuka, sosai km ya taba ransu tare da karya, musu  zuciyarsu .
ranar dai haka suka yini jikinsu a sanyaye Babu dad'i.

Koda kowannen su ya koma gida, haka matan su suka gansu sukuku, dan Abdul ko abinci kasa  ci yayi.
ya rufe kanshi a d'akinsa yana ta faman aikin kuka,da tuno da rayuwarsa ta baya .
Bbu  yadda Yasmeen batayi ba amma Sam  yak'i  yarda ya bud'e mata k'ofa, sai da tace idan bai bud'e ba zata kira 'yan uwansa, da k'arfi cikin muryar kuka yace " No please karki kira su zaki tada musu hankali zan bud'e miki, " ok to bud'e, a hankali ya bud'e mata k'ofar, yadda ta ganshi ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba, cikin rawar murya tace " waye ya tuna maka da bayanka?

Shiru kawai yayi ya kasa furta daidai da kalma daya jikinta a matukar sanyaye tarasa inda madaidaicin fridge dinsa yake    ruwan me sanyi ta d'auko ta bashi yasha, sannan ta shiga aikin lallashi .

Duk gari jama'a an d'auka 6's STARS zasu bada labarin su, duk inda ka duba sai maganar ake, makarantun boko dana islamiyya, majalissar yara da manya, kai harta tsofaffi, dai-dai da yara k'ana sai kaji suna maganar, kowa ya d'okanta ranar tazo, musamman samari da 'yan mata, kowanne gidan TV ko radio maganar  kawai akeyi.

*FRIDAY 12:00PM*

Kowanne ya taho da matar sa, da kuma yaran sa, dubbun jama'ar dake bakin get suka d'auki ihu da ganin motocin su, cikin takun isa da tak'ama mai cike sa izza suka fara takawa zuwa cikin hall din, kallon jama'ar da suka taru dan su sukayi take gaba d'ayan suka ji kwalla, a zuciyoyin su sukeyiwa Allah godiya abisa baiwar dayayi musu ta jama'a domin mutum rahama ne.

Bayan sun shiga cikin hall d'in mai d'auke da 'yan jarida, gidan TV, radio, da sauran masu d'aukar labarai, dan an hana kowa shigowa hall d'in daga su sai 'yan masu d'aukar labarai, da securities  d'insu, Zaid ya kalli 'yan jarida yace " sun shirya, saurayin mai suna Al'amin yayi gyaran murya yace " please Sir ko zaki bawa duniya labarin asalin had'uwar ku?

Murmushi Khamal yayi sannan ya fara magana.......

*MOMYN ZARAH*

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now