16

4.1K 189 17
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

16

Ya fara k'ok'arin ball da ita, da sauri Momy ta rik'e shi, cikin b'acin rai tace " karka soma dukan min 'ya akan wani katon banza, kai a ganinka Abban Ja'afar zai iya marin d'ansa ne koda kai ya mara? 

shima a fusace yace " wallahi Zainab ki fita daga ido na inba haka ba, ranki zaiyi masifar b'aci, "wani kallo Momy tayi masa murya ta a  matuk'ar fusace tace " wallahi muddin ina da rai da lafiya a doron k'asa bazan tab'a bari Fateeha ta rayu cikin bak'in ciki ba, koda kuwa hakan na nufin rabuwar mu da kai,  tana karasa fad'ar haka ta kama hannun Fateeha fuuuuuuuuuuuu suka yi ciki,  ranta a b'ace zuciyar ta tamkar zata tarwatse.

Bayansu Dady yabi da wani kallo me cike da alajabi da mamaki a hankali kuma ya maida kallon sa ga Ja'afar dake tsaye yana kallonsu cike da takaici zuciyarsa na masa wani irin tsalle tamkar zata basa masa kirji,
muryar Dady a raunane  yace " kayi hak'uri Ja'afar kasan yadda halin mata yake,  murmushin yak'e Ja'afar yayi domin shi kad'ai yasan yadda yake jin kansa
kana yace " ba komai Dady,  sallama suka yi sannan yabar gidan koda yaje gidansu a matuk'ar haukace  ya shiga gidan kai tsaye part d'insa ya nufa ya sona cire kayan jikin sa ya bud'e washing machine ya zuba ya soma sintiri a d'akin yana had'a abubuwan da Fateeha take masa akan wani banza cima kwanace marar aikin yi jobless me zaman banza sosai ya dad'e yana zarya da saka da warwarar yadda zai salwantar da Khamal daga duniya  kafin daga baya wata idea tazo masa, dariya ya saki , had'i dayin murmurshin mugunta ya ware hannushi duka yana dariyar samun mafuta had'e da shigewa bathroom.

Bayan kwana biyu tafiya takama Dady zuwa Abuja wanda a kalla zai yi kamar sati kafin ya dawo .

Yayin da a hankali kuma tafiyar Khamal Saudia ke k'ara matsowa wanda kwata kwata Fateeha batason tafiyar tashi dan wani lokacin har kuka take masa, ta rasa dalilin dayasa hanklinta yak'i kwanciya akan tafiyar Khamal bayan farin ciki ya kamata yayi, tun  daren jiya sukayi da Khamal zai zo gidan su, ganin mahaifin ta baya gari,
ta shigo dashi har parlour  bak'i, bayan Khamal ya shiga cikin wata rantsantsiyar shadda gizna, zama yayi a d'aya daga cikin kujerun dake falon, ya kafeta da ido, yayinda hannunta ke cikin nashi, maganar tafiyarsa yake son mata amman baya son abinda zai tada hankalin ta,  itama shi take kallo zuciyarta na wani irin bugawa idan akwai abinda tafi so da k'auna a duniya yana bayan Khamal tana yi masa son da ita kanta bata san yadda zata misalta shi ba, a hankali ya bud'e bakinsa  yace " Fateeha  next week In sha Allah zanbar k'asar nan dan angama komai na tafiyata saboda... tun kan  ya k'arasa magnarsa,  hawaye suka cicciko sun fara bin fuskarta,  zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da sauri ya rud'e,
kasa magana yayi illa jikinsa daya rungumo ta tsam, ya shiga rarrashin ta yana shafa bayanta muryasa a matuk'ar sanyaye  yasoma magana " please Fateeha ki natsu ki kwantar da hankalinki wlh kece karfin tafiyar nan tawa ,kusan sbd ke zanyinta domin cigaban rayuwarmu kin dai ji abinda Dad d'inki yake fad'a akaina, ko bakya son cigabanmu ne?
ya k'arasa maganarsa yana sake k'amk'ameta.. muryarta na rawa tace " nifa..nifa bawai tafiyarka ce banaso ba rashin ganinka daba zan dinga yi bane na wani lokaci shine damuwata amman kamin alkwari duk rintse duk wuya bazaka barni ba bazaka juya min baya ba Khamal ina mugun sonka,  rayuwata da komai nawa naka ne mallakinka ne Khamal.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now