4

9K 305 6
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

          ~NA~

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO  UNDER AGES , SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

4

Murmushi Khamal yayi ,sannan  ya kalli Ammar yace " to Bissimillah,shima murmushi yayi yace "ok sannan ya fara

" misalin k'arfe 11:00pm na dare a garin Holland, muna tafiya ni da Matata Basma a mota .
ana tsuga  matsanancin ruwan sama, Basma  tace " Dear kamar hannu naga ana d'aga mana ko?

Ido sosai na k'ara bud'ewa dan ganin ko gaskiya ne, " eh my love kuma kamar mace, " eh macece Basma ta fad'a a dai-dai lokacin da muka k'arasa wajen, mace na gani da tsohon ciki, ga motarta a gaban ta ga dukkan alamu motar ce ta lalace, muna tsayawa Basma ta fito da sautunta ta kama wannan  matar dake takawa da kyar ta shigar da ita 'cikin  mota, ta rufe ta zaga ta shiga gaba, da kyar matar ta iya bud'e baki tace "motatace tayi faci.
sai a lokacin na lura yarinyar ce wacce bazata wuce sa'ar Basma ba.

" a hankali tace " sunana YASMEEN, "oh Basma tace, sannan tace ni kuma Basma, yanzu ina zamu kaiki ko mu wuce gida dake kawai?

"A'a please ku kaini hospital saboda ina d'an jin ciwo, "ok Basma tace, ta kalli Ammar, gira ya d'aga mata yana murmushi , direct a hospital mafi kusa muka wuce, sai da  muka kai 1:00am sannan aka sallame mu Dr ya tabbatar mana da babu wata matsala, daga nan muka wuce gidan mu, da taimakon Basma Yasmeen tayi wanka, ta bata abinci, dai da Yasmeen ta dawo hayyacinta sannan ta fara laliben jakarta.

Kallon ta Basma tayi tace "me kike nema, murmushi tayi tace "jakata, Basma tace " aiko ina tunanin kin barta a mota, " please kozan iya samu aran waya na kira miji na na sanar dashi, inda nake .
dan nasan hankalin sa nacan a matukar tashe, "ok tace had'i da mik'o mata wayarta, kiran Abdul Yasmeen tayi ta shaida masa abinda ya faru, hankalinsa yayi mugun tashi yace " a bashi mai gidan.

Basma ta karb'i wayar ta kaiwa Ammar, da sallama Ammar ya fara magana, cikin tashin hankali Abdul yace " please a wace unguwa kuke?  ina son nazo yanzu.

Murmushi Ammar yayi yace " mu muna liver fool stress, amma idan ba damuwa ka fad'a mana inda gidan yake sai mu kawota, dan naga kamar baka cikin nutsuwa, "ok ina gida,

"Yanzu zamu zo da iznin Allah, da Basma aka tafi kai Yasmeen gida, a harabar gidan suka iske Abdul sai safa da marwa yake, yana ganin motarsu ta shigo tun kafin su k'ara sa parking ya k'ara sa da sauri  wajen.
Yasmeen ta fito da kyar aiko da sauri Abdul ya rungumeta ajikinshi .
  yana sauke naunauyen ajiyar zuciya, gyaran murya Ammar yayi,  sai lokacin Abdul ya tuna ashe fa  basu kadai ne agurin ba .
sakin Yasmeen yayi tare da  nufar inda Ammar yake yana Miko masa sukayi musabaha fuskasa cike da tsansar farinciki taimakon matarsa dasukayi .
sosai yayi masa godiya, sukayi sallama.

Washe gari bayan an gyara motar Ammar yana wajen aiki yayiwa Basma waya yace yanzu bakanike zai kawo mata mota takaiwa Yasmeen, muryarta  cike da  shagwab'a tace " ni idan Kai wa zai dawo dani?

Murmushi yayi kamar tana kallan sa yace " ok to mu had'u a gidan, lokaci d'aya Basma da Ammar suka k'ara gidan, number Abdul da Yasmeen ta kiya ta bawa Ammar ya kira Abdul, aiko da sauri ya fito da fara'a, ya taresu  yana cewa " kwa tsaya daga waje ai ciki zaku shigo, yana maganar yana mik'awa Ammar hannu.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now