33

5.6K 279 12
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
             *~(UMMU AMAN)~*

33

Had'i da sambatun dad'i, itako Lubnah ta lafe a jikinsa tana ta zuba masa shagwab'a daga tace nan na mata ciwo sai tace nan na mata ciwo, duk ya rud'e ya rasa inda zai saka kansa, a hankali ya mik'e tare da ita a jikinsa ya nufi bathroom, runwan wanka mai zafi ya had'a mata, sannan ya saka ta cikin runwan wankan ya sab'e ta sol ya gasa mata k'asanta sosai, daga k'arshe suka gabatar da wankan tsarki tare, sai da ya shirya ta tsaf sannan ya rungumo ta jikinsa suka tsunduma duniyar bacci, tun daga wannan rana soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Lubnah da Zaid, muguwar kulawa suke bawa junansu kowa yana gudun b'acin ran kowa.

Rayuwa su Zaid sukayi a wannan gidan har na tsawon wata d'aya rayuwar mai cike da jin dad'i had'i da walwala da kwanciyar hankali,mai tsawa a rai wanda bazasu tab'a mantawa ba,  sai da suka gama Honeymoon d'in su sannan suka koma gida cike da kwanciyar hankali, lokacin da su Zaid ke Honeymoon komai hannun Abraham ya dawo shike gudanar da duk wata harkar Business d'in su, dan ya nutsu sosai ya zama kamili nutsatstsen mutum, duk wannan abu dake faruwa Zaid manta da maganar da Mukhtar ya fad'a masa ta cewar Abraham ba d'an Ammi da Abba bane dan sosai maganar ta tsaya masa a rai, dan haka suna dawowa cikin gari ya shiga bincike mai zurfi ba tare daya sanarwa da kowa ba, direct babban gidan marayu ya nufa.

Sai da yayi bincike sosai na tsawon lokaci sannan ya gano gaskiya amma duk da haka bai gama yarda ba, har sai ya ji daga bakin Ammi da Abba tunda ya fara binciken ya shiga matsananciyar damuwa kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin tashin hankali, sosai hankalin Lubnah yayi mugun tashi, ta rasa inda zata saka kanta gashi tayi masa tambayar duniya amma kullum maganarsa d'aya ce babu komai, ko abinci ma sai ta matsa masa sannan yake ci kad'an, ranar Friday kamar yadda suka saba direct daga masalcin juma'a gidan su Ammi suke wucewa, bayan sun idar da sallar juma'a Zaid ya kalli Abraham yace " wai ya naga kana ta zuba sauri haka ina zaka ne, " wallahi mantuwa nayi a office na wasu takardu ne, kaje gida ka jira ni nan da 30 minutes zan dawo "ok yace dan shi hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba dan zai samu damar yin magana da su Abba.

Zaid ya shiga motarsa ya nufi gidan su, shima Abraham ya shiga tashi motar ya nufi company, Abraham na gaf da isa wayarsa ta fara ruri ganin sunan secretaria sane yasa shi d'aukar wayar bayan ta gaidashi tace masa ta kwashe takardun daya bari ta tafi gida dasu amma gobe zata kawo mishi su office ganin masu mahimmanci ne takardun shiyasa tayi haka, "ok baduwa nagode kawai ce had'i da kashe wayar, kan motarsa ya kanya ya nufi gida, Zaid nayi parking a harabar gidan ya fito da sauri dan Allah Allah yake suyi maganar kafin Abraham ya dawo,yana shiga gidan ya iske su a main parlor gidan na k'asa, cikin ladabi da biyayya ya durk'usa har k'asa ya gaida iyayen nashi.

A  hankali Ammi ta zubawa tilon d'an nata ido ganin yayi muguwar rama gashi daga ganinsa zaka san yana cikin muguwar damuwa abinda keyi shi Abba ma keyi dan sosai dan shima yaga ramar da Zaid d'in yayi, Abba ya mik'e had'i da kallan Zaid yace " ka same ni a sama na ina son magana dakai, ya juya ya kalli Ammi yace " tashi muje sama, magana anan batayiyo ba saboda 'yan aiki dake giftawa akai-kai, cikin mutuwar jiki Ammi da Zaid suka mik'e sukayi saman gaba d'ayansu, Abraham na shigowa shima yayi parking a indaZaid yayi, a hankali ya fito ya nufi parlor ganin duk basa k'asa ya sashi hawan saman, bayan Abba da Ammi sun zauna ne ya kalli Zaid yace " meke damunka, meye damuwarka ko tun abinda Mukhtar yayi maka ne yake tab'a har yanzu bai bar zuciyarka?

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now