10

5.4K 247 5
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

          ~NA~

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


*EDITED BY*
*Maryam Ahmad Paki*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO  UNDER AGES , SU KARANTA BA'''


~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

10

Daga wannan page d'in bazan k'ara posting a WhatsApp ba, sai a wattpad duk mai so zai samu a wattpad complete

Kamar mahaukaci ya kalli Sanata Sambo yace "ina zan samu Umar?".

"gaskiya Abdul ban sani ba, Abdul yace "ok zanci gaba da rik'e Haidar har sai randa ka kawo min Umar, sai ka bani shi ni kuma na baka d'anka, yana kaiwa nan ya fice, Haidar na ganin yadda Abdul ke tafiya ya tabbatar da ba lafiya, sai had'a hanya yake ya fice daga hankalinsa, da sauri ya fito daga inda yake b'oye ya rik'e Abdul, cikin sauri ya sakashi cikin  mota yayiwa motar key ya figeta da sauri.

A bukkar su yayi parking, da sauri ya fito ya zagaya ya fito da Abdul, Yasmeen na ganin Abdul ta mik'e da sauri ta rik'e shi tana kallan Haidar cikin tashin hankali tace " lafiya?" haka dai ya fito daga wajen Dad, ni kuma ganin yanayin dayake ciki yasa ban tambaye shi meke faruwa ba, ya k'arasa maganar yana zaunar da Abdul a bukka.

Ruwa Yasmeen ta d'ebo ta bashi a baki ya sha, a gefen sa ta zauna ta mik'e k'afafuwanta, ta kwantar da kansa a saman  cinyar ta, ta shiga shafa masa sumar kansa tana yi masa kalamai masu dad'i da kwantar da hankali, ganin yana sauke ajiyar zuciyata ne ya tabbatar mata da ya fara samun nutsuwa.

Cikin dabara ta fara tambayar sa abinda ya faru, "cikin kuka ya zayyane musu duk abinda ya faru, da sauri ta mik'e tsaye dafe da k'irji tace "UMAR!!!" sosai Haidar ma ya firgita, cikin rawar murya tace "shine kenan wanda ya saida gidan ku?  domin faruwar abin ba dad'ewa aka sai da gidan, Haidar ya kalli Abdul yace meye mafita yanzu?".

Cikin kuka yace "na cewa Dad d'inka idan yana sanka a raye ya kawo umar  in 2 days, ni kuma zan bashi kai, " gud, Haidar ya fad'a sannan yace "ko da yayi waya yace maka kazo ga umar  ba tare zamu je ba, idan munje sai na samu waje na b'uya ka fad'a kamar yadda ka fad'a masa yau.

Da mamaki Abdul ya kalli Haidar yace me yasa!?  "saboda zasu iya had'a baki su cutar dakai" dariya Abdul ya tintsire da ita, sannan ya kalli Haidar yace "   Haidar kenan, yanzu har akwai wata rayuwa da zan so agaba, har akwai wani jin dad'in ko farin ciki da zan k'ara kasancewa a cikin shi, bani da kowa aduniya duk wanda na girma dasu na saba muka shak'u babu ko d'aya, wallahi ko yau na mutu bani da kaico, yanzu abu d'aya ne kawai ya rage min a duniya naga bayan mak'iya na, da sauri Yasmeen ke kallon shi tana girgiza kai tana cewa "a' a hawaye na zuba daga idonta, "haba ya Abdul please karkayi min haka, baka san dan me Allah ya  barka a raye kai kad'ai a cikin zuri'arku ba, Allah baya tab'a yin abu babu dalili ni nasan akwai dalilin da yasa Allah ya barka a raye Yaya Abdul please karkayiwa Allah butulci, kai fa musulmi ne, ya kamata ka yadda da k'addara mai kyau ko mara kyau, kai fa ya kamata ka rink'a k'aramin k'warin gwiwa, please Yaya Abdul kar kayi mun haka" ta fashe da mahaukacin kuka, jikinshi ya jawo ta ya rungume ta saka kukan shima, Haidar na ganin haka ya tashi ya fita.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now