'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*17
D'aya daga cikin 'yan sandan ne ya danna wata 'yar k'ararrawa, ba'afi 2 minutes ba saiga dan dazon motocin police sun zo wajen, kama Khamal sukayi suka danna shi cikin mota, sai da sukayi tafiya takai ta 8hrs sannan suka k'araso Shimesi prison, baban gidan yarin dake k'asar saudiyya kenan, nan aka kai Khamal wanda duk wanda ya aikata babban laifi can ake kaishi.
Sosai Khamal ke kukan mutuwa yana ihu kamar ransa zai fita, yace " haba bros bai kamata kayi min haka ba, bai kamata ka nemi hallaka ni akan mace ba, kai d'an uwana ne na jini, kai kad'ai gare ni, duk duniya bani da kowa sama da kai idan dan Fateeha ce meyasa baka sanar dani ba?
" me yasa baka sanar dani itace wacce kake so ba?
"haba my only blood bros, why Hamza?
ya k'ara fashewa da wani irin mahaukacin kuka mai cin rai da tab'a zuciya.
Hamza ko cikin farin ciki ya kashe wayar ya juya fuskarsa d'auke da murmushi, yana juyawa yayi arba da Hajiya wacce tunda ya fara waya da Khamal take tsaye akanshi tana sauraran sa, babu abinda jikinta keyi sai kerrma, gumi ya gama jik'a mata duk ilarin jiki, kamar wacce akayiwa wanka da ruwa, cikin tsoro da firgice take nuna Hamza da yatsan hannunta bakin ta na rawa tace " Ham...za Ham..za.. kai ne kuwa?
" Kai ne ka yiwa d'an uwan ka uwa d'aya uba d'aya haka, Hamza meka fara sha, ?
"mai ya sameka, meke damun Rayuwarka akan mace Hamza?
, kai ta fara girgizawa cikin tashin hankali tana "' a'a wannan bakai bane Hamza , bakaine ainahin Hamza na ba.
, "Hamzan dana sani na rik'a da hannuna jikana ba haka yake ba, murmushi yayi ya tako a hankali har gabanta ya tsaya ya zuba mata ido kana yace " Ok kinji abinda nace kenan?
, cikin tsawa yace " amma duk da kinji kika tsaya a gaba na kina yimin tamboyin banza da wofi tare da surutan iska cikin kuka Hajiya ta rufe shi da duka tace " Allah ya isa tsakani na dakai, bazan tab'a yafe maka ba, dan ba irin wannan tarbiyyar na baka ba.Dariya yayi yace " da kinji nace ki yafe min ne, Hajiya tace" kaci amanar mu Hamza, ka yaudare mu, ka munafurce mu, kai mugu ne mai fuska biyu mai mugun nufi a zuciyarsa, azzalumi, in sha Allahu amanar mu daka ci bata ta tab'a barinka ka rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba.
"kuma alfarmar Ubangiji ko Khamal yana raye ko baya raye baza ka tab'a mallakar Fateeha ba, matuk'ar ina raye in sha Allah bazan tab'a bari Fateeha ta zama matarka ba.A zuciye Hamza yayo kanta ya shak'e mata wuya yana gurnani yace" aiko lalle zaki mutu, kinyi ganganci Hajiya, dan duk wanda ya nemi yimin katanga wajen cikar buri na, to zan kawar dashi, daga doron k'asa batare da shakka ko tsoro ba.
Hajiya ta shiga haure-haure da shure-shure tana kokuwa da Hamza amma ina, bai sake ta ba sai da yaga ta daina motsi da numfashi alamar rai ya fita.Gaba d'aya Idonta duk sun firfito waje,sunyi tulu tulu alamun shan wahala numfashin ta ya d'auke, ya wurgar da ita gefe, ya tsugunna a gabanta yana dariyar mugunta yace " sai ki hana ni mallakarta, shima yana hanyar biyo ki, gawarta ya d'auka yakai kan gadonta ya kwantar da ita, ya ja mata bargo ya lullub'e ta kamar mai bacci, shi kuma ya nufi d'akisa ya kwanta yana tunanin abinyi.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...