'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*41
Cikin rawar baki ta nuna Kausar da hannunta tace " wannan ce matar Fahad d'in? cikin mamaki Hajiya Lailah tace " eh ko kin santa ne? murmushin yak'e Hajiya Rabi tayi had'i basarwa tace " kai masha Allah yarinya mai kyau, ita dai Kausar sai nannok'ewa takeyi tana b'oye jikinta, a hankali Hajiya Rabi ta tako gaban ta cikin murmushi ta rik'o hannunta tace " nima Momyn Fahad ce ki saki jikinki da ni kinji ko, kai kawai Kausar ta iya gyad'a mata alamar eh.
Da sallama a bakinsa ya shigo ganin Momy da aminiyarta yasa shi rusuwa har k'asa ya gaida su, cikin fara'a Hajiya Rabi ta amsa had'i da cewa " oh ango kasha k'amshi gashi anyi biki Momynka bata nan ko? Kansa ya shafa yana murmushi batare daya ce komai ba, ganin haka yasa Hajiya Rabi taja hannun Hajiya Lailah suka fita dole badan ranta yaso ba, a hankali ya d'aga kansa ya kalli Kausar dake tsaye tana ta b'oye-b'oyen jiki, d'an murmushi yayi sannan ya mik'e yace " ki shiga ciki yara zasu shigo da kayan abinci, kamar jira take ta juya ta fara takawa a hankali yayinda duk ilahirin jikinta motsawa yake musamman hips & boom boom d'inta take Fahad yaji wani abu ya tsarga masa a hankali ya lumshe idonsa had'i da furta "ya salam.
Duk wani kayan masarufi na girki an kawo mata part d'inta tun daga kan shinkafa, taliya, macaroni, couscous, indomie, kwai, cahamus, kifi, nama, kaji, kanta, kayan ciki, bushashshan kifi, da kayan vegetables, fruits duk an kawo saboda ya yanke kansa bazata sake shiga part d'in su Momy ba sai dai idan zata shiga gaida iyayensa shima tare zasu je su dawo tare ayi komai akan idansa, bayan an gama shigo da kayan an shirya su tsaf a store ya shiga d'akinta ya iske ta, hamshin dadd'an turaren wutar ya shak'a, a hankali ya mayar da kallansa kanta yace " ga kayan abinci nan kawo kije ki duba duk abinda babu sai ki rubuta min, har kayan miya da kayan tie an kawo daga yau zaki fara girki a part d'inki, sannan karki kuma shiga part d'in su matsawar bana gida, na kuma gaya miki idan zaki fita ko k'ofar parlor ki saka hijab kinga dai abinda ya faru ganin idanki, a hankali tace " to in sha Allah zan kiyaye, sanyi yaji har cikin ranshi.
Mik'ewa yayi yana niyyar fita, har ya kai bakin k'ofa ya juya karaf suka had'a ido da sauri ta mayar da kanta k'asa, murmushi ya kuma yace " sannan ki rink'a sakawa k'ofar parlor key koda ina gida ta yadda duk wanda zai shigo sai yayi miki nocking, kinga babu wanda zai rink'a shigawa kai tsaye, murmushi tayi masa batare dace komai ba, dan ta fahimci inda ya dosa, shima murmushin ya kuma yayi mata sannan ta ya fita.
Dauriya kawai Hajiya Rabi keyi dan iya tashin hankali ta shigeshi, ko sallm bata iya tsayawa tayiwa Hajiya Lailah ba tayi tafiyarta, tana shiga gidanta tayi cilli da hand bag da mayafinta ta shiga safa da marwa tana neman fita, " ashe shiyasa Boka Jimrau yace na fara zuwa gidanta mean yasan komai, to me hakan yake nufi, mace dake mugun so ita aminiyata ke yiwa mahaukacin so, macen dake da burin yin lez da ita, ita aminiyata ta makance akanta, cikin mugun tashi hankali, firgitaccen tsoro da fargaba, matsanancin bak'in ciki tace " wallahi bazan tab'a iya hak'ura da Kausar ba.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...