9

5.6K 251 1
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

          ~NA~

*HAUWA A USMAN*
        _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO  UNDER AGES , SU KARANTA BA'''


~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

9

"Bayan anyi min test aka dawo dani, Doctor ya tabbatarwa da alk'ali ina da tab'in hankali, kwakwalwata ta tab'u wanda hakan ya haifar min da ciwon kai me tsanani ,bayan Dr ya gama yiwa alk'ali bayani sannan ya mik'awa alk'ali takardun .
, alk'ali ya duba sosai kuma ya gamsu, bayanin alk'ali ya gama yan duba dubensa da zaiyi ya yanke min hukunci zama a sabitin mahaukata  dake kurkuku (prison) na tsawon shekara biyu, tare da shaidawa jama'ar dake kotun cewa idan na gama shekara biyun babu wani sauran hukunci a kaina kotu ta sake ni.

Daga kotu kai tsaye (Prison) aka wuce dani, Yasmeen nata kuka, nazo na wuce ta gabanta ko kallan inda take banyi ba sbd bana 'cikin natsuwata da haiyacina , bayan an kaini prison, na samu kulawa sosai ban sha wata muguwar wahala ba can , kasancewar ni a hospital din nake.

Ko a gidan yari  banida da wani aiki sai kuka,  da tunani ahlina dana rasa kona  nay ta ihu ina kiran sunan Mama da Ramlat ko Ja'afar da Umar, sosai wani lokacin idan abin ya fad'o masa ko ya tuna yake hauka tuburan, na rame na koje, tsabar tunani da tashin hankali.
gaba d'aya na fita daga hayyacina Sai sambatu iri iri nake a game taskon rayuwa r dana tsinci kaina ciki .
, Na tara k'asumba da gemo, kwata-kwata bana magana idan zaka shekara akaina aka na yi min  magana bazai kalle ka bama balle na tanka maka, haka wani lokaci zakajini  cikin dare ina ihun Ina buge buge  da kira sunan  Sanata Sambo ....ka cuceni ka zalinceni karabani da ahlina danafi kauna fiyye da komai  ka maidani maraya karfi da yaji mara galihu adoron kasa .

daman Haka fadar gsky zatayi da rayuwata?
Hk son kwatar yanci  zatayi sanadin tabarbarwa duniyata da tarwatsa rayuwata ?

Meyasa...?

meyasa  zaka min hk ?
Sai km ya fashe da wani matsanancin  kuka me tsanani da cin rai tare da taba zuci

BAYAN SHEKARA 2

Cikin ikon Allah Abdul ya fito lafiya lau, ya warke sumul babu abinda ke damunsa, sai matsanancin bak'in ciki da damuwa, da kuma wutar d'aukar fansa dake k'ara ruruwa a zuciyarsa  in every second, koda Abdul ya fito bai bayyanawa kowa da duniya fitowarsa ba, ya b'oye kansa, babu abinda yasa gaba sai bincikin inda zai samo Sanata Sambo.

Tsakiyar 'cikin wata dokar daji Abdul yasamu yayi Buka tare da   kebe kasan Daga shiga 'cikin mutane burinsa bai wuce yaga tagayyara rayuwar Sanata da dansa ba ..cikin wannan mahaukacin daji  yacigaba rayuwasa shikadai .

Shiryawa yayi cikin dare, yayi shiga yadda babu mai gane shi, y nufi unguwarsu, a k'ofar gidan su ya tsaya, gaba d'aya an canjawa gidan tsari an mayar dashi gidan zamani sosai harda bene, gizo Mama, Ramlat, suka fara yi masa sosai yake ganin su a cikin idonsa, Ramlat na ihu cikin kuka take kiran sunansa, muryar Mama ya jiyo ta _"Abdullahi karka zo, karka zo Abdullahi ko kai kad'ai ne ka rayo danka d'aukar mana fansa_.

Sosai Abdul ya kwanta a wajan yana birgima a k'asa yan ihun kuka kamar ransa zai fita, ihu yake sosai yana sambatu kamar mahaukaci, kasancewar tsakar dare ne yasa babu wanda ya ganshi, ko ya gane shi, wani tsoho dake kwance a soron wani gida ya jiyo ihun Abdul,   a hankali ya fito da touch light a hannunsa, har ya zo kan Abdul amma bai sai anzo kansa,b a dafa shi tsohon yayi yace " yaro lafiya?  Kasancewar Abdul ya canja kama kuma ya tara k'asumba yasa tsohon bai gane Abdul ba, sai da tsohon yayi magana sosai sannan Abdul ya jishi, ya kuma dawo hayyacinsa, mik'ewa yayi bai yiwa tsohon magana ba yayi tafiyarsa, tsohon ya bishi da kallo me tattare da tausayawa .

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now