'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*80
Dukkan su suna zaune akan dinning table Zarah ta kalle su tace,
" a gaskiya ya kamata muje mu gano Hamza da Muktar fa,
fuska Zaid da Khamal suka b'ata batare da sunce komai ba,
Fateeha da Lubnah suka ce gaskiya kam ya kamata,
kunga nan ma sai muyi umara,
Basma tace " eh Allah dan nima ina san ganin Hamza da Muktar ido da ido,
Neaseer yace " gaskiya ya kamata mu gansu kam,
haka dai sukayi ta tattaunawa amma daga Zaid har Khamal babu wanda yake k'ala,
ganin haka yasa sukayi banza dasu,
Abraham da Abdul suka kira pillot,
wanda jet d'in su ke hannunsa, suka sanar masa ya shirya jibi zai kai su Saudi Arabia,
washe gari suka je prison dake Holland domin ganin Muktar,
yadda suka ganshi yayi bala'in basu tausayi,
dan zai da duk suka toshe hancin su ,
saboda tsananin warin dayake,
acan gefe daga k'arshen gidan yarin aka kaishi,
dan warinsa yana iya halaka mutane da dama,
ko magana baya iyawa, sai ido daya k'urawa Zaid da Abraham yana kallan su k'uri,
a hankali ya kalli Lubnah, dake hawaye, kafin yabi sauran da kallo,
cike da takaicin rayuwarsa da nadama,
yayiwa su Zaid alama da hannunsa,
da su yafe masa, murmushi Zaid yayi yana jin tsananin tausayin sa,
yace " ni ai na dad'e da yafe maka Mukhtar,
kuma Abraham dasu Abba ma sun yafe maka,
da kyar ya d'aga kai alamar ya gode.Washe gari jirginsu ya d'aga zuwa k'asa mai tsarki su duka har yaransu,
a madina suka fara sauka sukayi ziyarce-ziyarce,
kafin su k'arasa makka suyi umara,
daga nan sukayi Jidda zuwa gidan yarin da Hamza ke zaune,
basu b'ata lokaci ba Hamza ya k'araso cikin electric walk chair,
yadda suka ganshi sunyi tsannain mamaki,
dan kamala da nutsuwa gami da annuri sunyi bala'in bayyana a tattare dashi,
sosai Hamza yaji dad'in ziyarar da d'an uwansa yayi masa,
ga yaran su nan masu kyau gwani ban sha'awa,
shima Khamal duk zafin da zuciyarsa keyi masa sai yaji ya gushe,
ya k'urawa Hamza ido kamar bazai d'auke ba,
kafin daga bisani suka gaisa sosai,
daga Saudia Nigeria suka yi, domin gaida iyayen su da 'yan uwa,
aiko duk sunyi farin cikin ganin su,
gidan su Zaid suka fara isa, sosai Ammi da Abba sukayi farin cikin ganin yaran nasu,
dama dangin kowa yasan kowa,
dan haka babu wani bak'unta ko kara, duk gidan su wanda aka je d'aya ne, yadda suka ga dama haka suke yi,
daga nan su kaje gidan su Fahad,
sai gidan su Lubnah da Kausar, sai gidan su Yasmeen,
daga nan sai gidan su Naseer wajen Momy da Dady,
har gidan su Abban Zarah da Alhaji Abdullahi ma sunje sun kai gaisuwa,
kafin daga k'arshe suka zube a gidan Zainab da Mannir,
acan sukaci abinci,
ranar Abdul yasha kuka kamar ransa zai fita kasancewar bashi da kowa a duniya bashi da wanda zai kira da nasa,
dakyar suka iya shawo kansa,
dama lokuta da dama hakan tana faruwa dashi idan ya tuna abin.Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na shud'ewa,
yayinda SIX STAR'S ke k'ara samun d'auka,
daga wajen al'umma har zuwa ga kan cimpanies d'insu,
dan yanzu duk Nigeria da Holland babu cimpanies d'in da ake ji da su kamar SIX STARS,
sun d'aukaka sosai a fad'in duniya,
sunan su babu inda bai je ba, sun tara dukiya mai tarin yawan da su kan su basu san yawan ta ba,
idan za'a kashe su basu san iyakacin abinda suka mallaka a duniya ba,
shiyasa suke taimakon al'umma,
duk inda sukaje ana neman taimako da gaggawa suke kaiwa tun kan a rok'e su,
suna da tarin gidajen marayu,
masallatai, rijiyoyi da bohol, da asibitoci,
suna shiga k'auyuka suna kai taimako,
suna yin hanyoyi, makarantun boko dana islamiyya a gurare da dama,
Allah yayi su da tsananin tausayi da jin k'ai,
shiyasa a kullum Allah yake k'ara d'aukaka su.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...