'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*28
Barrister ya kalle ta yace " ya sunanki " Lubnah Muhammad Bature, "meye alak'arki da wanda ake tuhuma? " miji na ne, " ok kiji tsoran Allah ki fad'awa kotu gaskiyar abinda kika sani game da wannan kissan, d'an shiru tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya had'i da share hawayen dake zubo mata a hankali ta kuma kai idonta kan Zaid taga shima ita yake kallo sosai ya kafe ta da idon shi, Barrister yace " kiji tsoran Allah ki dubi girman Allah ki sanar damu gaskiya karki duba alak'arki da wanda ake tuhuma, ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu sannan ta fara magana cikin kuka " a ranar da abin ya faru bayan ya dawo gida yayi wanka ya shigo part d'ina yaci abinci, har muka gama cin abincin amma banga Aunty Teemah ta zo ba alhalin tare muke cin abinci, danaga bata shigo sai na zuba mata nata a food flask nace ya kai mata, da farko kin zuwa yayi sai da na k'ara yi masa magana sannan ya d'auki abincin ya fita dukda ransa bai so ba.
"Ranar kwanki ne? da sauri Zaid ya d'auko kai suka had'a ido, haka nan Lubnah taji kawai bazata iya bayyawa duniya sirrin zamantakewar auren ta ba, dan idan tayi hakan kamar ta nunuwa duniya mijinta ba adali ba bane, babu wanda zayyi masa adalci a take za'ayi masa mummunar fassara, dan haka tace " eh tana kallan fuskarsa da k'arfi Zaid ya sauke ajiyar zuciya game da runtse idonsa, Barrister yace " daga nan fa?
"D'aki na koma na kwanta sama-sama na rink'a jiyo ihunta da sauri na mik'e nayi parlor, a parlon muka ci karo da Teemah ta shigo da gudu a firgice tana kuka ganin yanayin da Teemah ta shigo ne yayi mugun tsora ta ni, da gudu nayi bedroom Teemah ma tabi bayana, daga ni har ita muka koma can k'uryar gado muka b'oye yayinda ni na k'urawa k'ofa ido ina sauraren ganin abinda ya firgita Teemah haka, da sauri naga Zaid ya shigo hannunsa rik'e da wuk'a tsirara, k'ara k'ank'ame ni Teemah tayi tana cewa wallahi kashe ni zayyi Lubnah please ki taimake ni karya kashe ni, shi kuma sai huci yake yana cewa wallahi sai na kashe ki, dakyar na lallab'e shi na bashi hak'uri ya hak'ura ta k'arasa maganar cikin azababben kuka.
Barrister yace " iyakar abinda kika sani kenan?
"Eh cewar Lubnah, "ok koma wajenki ki zauna, tunda Lubnah ta fara magana Zaid ya k'ura mata ido cike da matsanancin mamaki had'i da mummunan tsoro, shi dai a saninsa hakan bata faru ba, iyakar abinda ya sani kawai ya biyo ta parlor kuma hannunsa ba wuk'a, take ya fara yiwa kansa tamayar ya akayi hakan ta kasance, shin meke faruwa dashi, meke damun shi, kodai bashi bane, meke shirin faruwa dashi ne, tabbas yasan akwai wani b'oyayyen al'amari a k'asa.
Barrister yace " da wannan shaidu nake kira da wanna kotu mai adalci data yankewa wanda ake zargi hukunci domin duk wata hujja da ake nema an samu an kuna tabbatar da shine wanda ya kashe matarsa da kansa, da sauri Mukhtar ya mik'e domin tuni jikinsa ya gama yin mugun sanyi shi kansa tsoro da firgici sun shige shi, cikin mutuwar jiki ya fara magana " ina rok'on kotu ta bani dama nayiwa Lubnah, Baba mai aiki, Baba mai gadi tambayoyi, bayan an bashi ya kira su duka gaban kotu ya kalle su yace " ko a cikin ku akwai wanda wata matsala ta tab'a shiga tsakanin shi da Zaid ko Teemah?
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...