'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*29
Gaban Zaid yaci gaba da fad'uwa yana dukan uku-uku tsoro da fargaba lokaci d'aya suka shige shi, babu abinda jikinsa keyi sai kerrma da tsoma yadda kasan wanda aka tsamo daga deep freezer cikin tashin hankali yake kallon Mukhtar da Teemah baki na rawa yace " Friend ban gane ba dama Teemah na raye?
" not friend call me your enemy, a fusace Zaid yayi kan Mukhtar, cikin zafin nama Mukhtar ya zaro bindiga daga aljihunsa ya d'aga ya saita kan Zaid yace " ka sake ka k'ara taku d'aya daga inda kake wallahi saina fasa kanka da wannan bindigar sakarai kawai, ka ja baya sosai a tsakani na dakai ka bada tazarar taku 30 a hankali Zaid ya ja baya, bindigar na saitin kan Zaid, Mukhtar ya fara magana.
" ni d'an mai gadin gidan ku ne, amma ka d'auke ni a matsayin d'an uwa, kuma masoyi, na taso ne a cikin talauci da k'uncin rayuwa hakan ne yasa tun ina yaro na tsani masu arziki na kuma mayar da masu kud'i a bokanan adawa ta, tun mahaifi na yana matashi yake yiwa mahaifinka bauta amma babu wani abu da kuka tsinana masa gai kyautar gidan zama da kayan abinci duk wata sai kuma kudin makarantar yara, dalilin dayasa kenan na fara tunanin naimarwa kaima mafita, tunanin dana fara yi shine yadda zan shiga jikin ku sosai.
"Hakan ne yasa ni shiga jikinka na kuma k'ank'antar da kai, na zama mage mai kwanciyar d'aukar rai, na kwantar da kai na, na shiga jikinku sosai na gama nasanin sirrinku, duk wasu halaye na daga sani masu kyau to ba nawa bane na Abraham ne haka ma duk wasu halayen Abraham daka sani marasa kyau to nawa ne, a zahiri shine d'an iska, amma a fad'iri nina ainahin mugun, nine na mayarda Abraham d'an iska, mazinaci, d'an shaye-shaye, saboda na kawar da hankalinku daga gano ainahin wanene ni.
"Ni na sanya k'iyayya mai k'arfi a tsakanin ku, dan matuk'ar kuna shiri kanku na had'e to ni bazan tab'a samun yadda nake so ba, take maganar Abba ta dawowa Zaid _" ku had'e kanku, ku zama tsintsiya mad'aurinku d'aya, dan idan kanku yana had'e babu wani mak'iyinku da zai samu nasara akanku"_, Mukhtar yaci gaba " rashin lafiyar da Abba yakeyi nine nayi mata poison injection nayi mamakin da har yanzu bai wula ba, sannan duk labarin da Teemah ta baka gaskiya ne, kuma nine MB d'in cikin labarin ta, MB yana nufin Mukhtar Barrister, sannan turai datace maka mun tafi tare shima da gaske ne, lokacin da mukaje Dubai ne, na tafi da ita, sannan karkayi mamakin jin acikin labarin ta tace MB matashin mai kud'i ne, haka ne dan duk satar da akeyi a gida ana zargin Abraham to ni ne.
"Kar in cika ka da surutu da yawa bari na baka labarin yadda muka tsara komai ni da matar ka kuma mata ta Teemah.
Da farko kamar yadda ka sani Teemah budurwa tace, kuma nine wanda ya kai ta wannan party, ni ne na kashe wutar hall d'in, kuma Teemah ce ta rungume ka bakai ka rungume ta ba, sanin irin zuciyar ka da kuma tsananin kishinka shiyasa mukayi amfani da wannan damar muka saka maka zargin Teemah a ranka, muka sanya ka kayi kanka da kanka mummunan furuci a bainar jama'a, sannan nasan har yanzu kana mamakin yadda duk ma'aikatan gidan had'i da matarka suka bada shaidar akanka ko?
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...