'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*62
Photos suka zubo, jikin Naseer na matsanancin kerrrma had'i da rawa ya durk'usa cikin mutuwar jiki yasa hannunsa dake karkarwa ya d'auki photos din yana dubawa,
take jikin Naseer gaba d'aya yayi collapsing had'e da weak,
ganin picture d'in sa wanda sukayi da Zarah tun kan suyi aure,
jikinsa na tsananin kerrrma yaci gaba da duba pictures din,pictures d'in Na'eem ya gani lokacin yana jariri dai-dai lokacin da Zarah ta mutu,
sai pictures d'in Ikram, Zainab da Mannir.Jikinsa na muguwar tsuma ya bud'e diary din ya fara karantawa kamar haka....Da fari dai sunana ZARAH MUHAMMAD DAURA,
ni haifaffiyar garin kano ce,ina da yaro d'aya sunansa NA'EEM,,
sai kuma ubana kuma uwata domin shi tamkar mahaifi na dauke shi
ya wuce miji kad'ai a gare ni shi gaba d'aya rayuwa ta ne,
shi kad'ai keda zuciyar Zarah,
NASEER MUSTAPHA!!!Ai tsayuwar gagarar Naseer tayi, take yaji gwiwoyinsa sun saki,,
k'afafuwansa kuwa kasa d'aukar sa sukayi balle su iya ci gaba da tsayawar saboda tsananin kerrrma da sukeyi,,,
cikin mutuwar jiki Naseer ya zube wanwar a k'asa,,
take numfashinsa ya fara nan d'aukewa,
yayinda Idanuwansa suke neman rufewa dan tuni sun fara gani dishi-dishi,,
lokaci d'aya jin sa ya d'auke kunnensa ya dod'e baya iya jin komai sai shhhhhhhhhhhh,,,
da sauri yasa hannuwansa ya toshe kunnensa dake ta faman yimasa amsa kuwa a cikin dodon kunnensa.Zube gaba d'aya kayan yayi a k'asa yana bin su da kallon tsoro kamar yaga aljani,,
da sauri ya fara ja da baya yana daga zaunen har yakai ga bango,,
kwata-kwata Naseer baya cikin hankali da nutsuwarsa ya gama fita fit daga hayyacinsa,,
take ya fara tunanin ta yadda akayi hakan ta faru, hannayensa ya d'ago yana kallansa had'i da furta,,
"da wad'annan hannayen na saka ta acikin kabari,
a gaba na akayi mata sutura had'i dayi mata sallah,
ta ya hakan ta faru?Yayiwa kansa da kansa tambayar,,
shi da kansa ya bawa kansa amsa da cewa lalle akwai wani b'oyayyen abu a k'asa,,
a zabure cikin rashin nutsuwa da hankali Naseer ya mik'e ya dinga neman evidence,,
ko dalilin dayasa Zarah tayi haka,
yana birkita d'akin yana mahaukacin kuka had'i da sambatu shi kad'ai,,
duk yabi d'akin ya hargitsa ya birkita komai,,
had'i da yin jifa da duk abinda yazo hannunsa a matuk'ar haukace Naseer yake yin komai had'i da kukan matuwa kamar za'a zare masa ruhinsa daga gangar jikinsa,,Gaba d'aya Naseer ya haukace ya zama tantirin mahauci tuburan,,
ya zage ya rink'a tik'ar hauka haik'an,,
ganin ya birkice komai da ko'ina na d'akin amma ya rasa wata hujjar komai yasa Naseer zubewa bisa gwiwoyinsa had'i da sakin uban ihuuuuuuuu da duk gidan sai da ya amsa kuwwa,,
dafe kansa yayi da hannu bibbiyu yana kukan mutuwa tuburan muraran,,
had'i da tsananin mamakin wannan birkitaccen al'amari,,
shi yanzu babban burinsa na farko yana so ya fara gano dalilin dayasa Zarah tayi haka,,
tayi masa wannan mummunan hukuncin akan laifin wasu, laifin daba shi ya aikata ba,,
laifin da kwata-kwata bai kamata ya samu hukuci akansa ba,,
ya rasa dalilin da yasa Zarah tayi masa wannan mugun butulcin.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...