'''GADAR ZARE!!!'''
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
بسم الله الرحمن الرحيم
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*3
Filin wasan kwallon k'afa dake garin Holland cike yake tap da d'unbun jama'a, iri iri babu k'abilar bil Adama da babu, ciki wannan filli wasa wanda ya tattara kan bak'aken fata 'yan Africa koma ince in Nigeria,da sauran kasashen duniya. ihun mutane daban daban dake zaune wajen ya cika filin wasan kwallon Yayinda wasu daga 'cikin mutane gurin ke sanye rigar matches rike da flags suna Dagawa sama suna zabga matsanancin ihu alamun Yan team dinsu ne suka samu nasarar cinyewa..
Kyakykyawan saurayin dake gefe zaune ya b'ata rai, in banda tsaki babu abinda yake faman yi,cikin fushi ya cutsa laulausar tafin hannushi 'cikin sumar kansa dake kama data Fulanin asali yana shafawa , cikin harshen Hausa yace " aikin banza kawai sun b'atawa mutane lokaci a banza ashe babu abinda zasu iya.
" wani dake gefen zaune ya lalleshi fuska d'auke da murmushi yace " Assalamu Alaikum, wanda ke zaune rai b'ace ya juyo ahankali ya tsurawa wanda keyi masa sallamar idanu yana kallonsa , had'i da amsa masa sallamar.D'ayan yace " naji kayi Hausa ne, shine nace bari nayi maka magana d'an uwa, murmushi yayi yace " lalle ko, wani can daga gefe shima yayi dariya yace " sannunku, nima naga 'yan uwa, dariya sukayi su duka,uku d'ayan dake gefe ya taso ahankali cike da takun isa ya mik'a musu hannu yace " am KHAMAL by name , dariya d'ayan yayi yace " ni kuma NASEER, hannu shima d'ayan ya mik'o musu yace " ni kuma ABDUL.
Take Kowanesu yagabatar da kansa, da dan'uwansa wani matsanancin ihun da aka kuma yi ne ya dawo da hanakalin su wajen filin wasan,sosai tsaki still NASEER ya kuma yi ya furzar da iska me zafi Daga bakinsa kana yace "aikin banza, aikin wofi ashe duk dakikai akatara anan dabasu iya koma kawai ana sa mutun bata lokacinsa .
dariya Khamal yayi tare da cewa " haba ai Chelsea k'arshe ce wajen wasa,kwallon duniya Abdul yace " haba dai Chelsea Malam.
kasan dai Amman idan ana maganar manya kwallon wasan duniya Barcelona ba'a mana ko itace kan gaba ?Naseer dake zaune ya dan zamo kadan Daga kujerarsa yana me juyowa saitin da Abdul yake ya kalleshi yana lumshe idanunshi sannan yace " Barcelona me? Suwaye 'yan wasan ta?
Khamal yayi dariya yace "Barcelona cluv pleyers 1 stegen 2 segi roberto 3 pique 4 basquet 5 samul umtiti 6 ivan rikitic 7 usman denbelle 8 Philip coutinho 9 surez 10 leneal messi 11 jodi alba, kallansa Naseer yayi yace " sannunka, gaskiya kai mayen kallon ball ne,na karshe amma ni nafison Real Madrid, saboda tana da manyan 'yan wasa wayanda suke da kwarewa sosai akan fanin wasa .
Dariya Khamal da Abdul sukayi sosai har da dan buga kafafunsu suka ce " suwaye manyan?
Dariya Naseer yayi yace "Real madrid cluv 1 keylo navers 3 cavejal 3 marcelo 4 sergio ramos 5 rafeal varen 6 casmiro 7 Asensio 8 tony krooss 9 karim benzema 10 luca modric 11 grez bell.
Abdul yace "ai gara kace ma Manchester City, suma suka saka masa dariya, hade ranshi yayi sosai yana cin magani kana yace " wallahi tafi duk sauran yan wasan kwallon da kuke.
dan itama tana da manyan 'yan wasa km kwararu da suka shahara acikin duniya Manchester city cluv 1 ederson 2 neuclas otemendi 3, kyle walker 4 fabian delp 5 ilkey gundigon 6 fernsndinho 7 bernado silver 8 rahem sterling 9 sergio aguero 10 leory sane 11 lapote,Nan fa musu me karfi ya shiga tsakaninsu kowanne yana kokarin kawo hujoji da cewa nashi ne babba, har sanda aka tashi daga wasan, har waje suka fito tare suna wasa da dariya, tare da exchanging din numbers junansu suka yi, sannan kowa ya nufi gida.
Washe gari tun wajen k'arfe 12:00pm Naseer ya fita wajen motsa jiki, tun baiyi nisa ba yaji ana kwala masa kira, cak ya tsaya ya juyo, dariya yayi yace " Khamal ka fito kenan?
" eh na fito, tare suka ci gaba da tafiya, Khamal ya kalli Nasser yace " halan kaima anan kake ba nisa?
"Eh daga can baya gida na yake, number 12,dariya Naseer yayi yace " kace bamu da nisa, ni ina layin baya number 27,ina nan da matata d'aya da yara 4 mata 2 maza 2, Khamal yace " nima da iyalina mata ta 1 yara 3 biyu maza 1 mace,
Suna hira har suka k'arasa wajen, Abdul suka hango ya dage yana ta motsa jiki, dariya sukayi suka nufeshi, cikin dariya Khamal yace " an dage ana ta faman aiki, halan madam ce bata san k'iba, sai a lokacin ya kula dasu.
Dariya yayi yace " ni Madam d'ita babu ruwan ta, kudai da naku suka koro ku, tunda safe, dariya sukayi gaba d'aya, sai wajen 4:00pm sukayi sallama, har zasu rabu, Khamal ya kalli Abdul yace " a ina gidan ka yake?
" a Jon crescent house number 35,dariya sukayi suka ce" lahh dukkan mu ashe unguwar mu d'aya,batare mun sani ba .
nan suma suka fad'a masa inda gidan su yake, murmushi yayi yace " nima ina da mata 1 da yara biyu mace da namiji.Sallama sukayiwa juna suka rabu, wajen k'arfe 8:00pm Abdul ya fita kallan wasan Cricket, yana zuwa ya iske Naseer zaune gaba d'aya hankalinsa ya tafi wajen wasan.
Murmushi Abdul yayi yace " tabb kaga sarkin kallo, ajiyar zuciya Naseer yayi .
ya kalli Abdul dake tsaye hannuwasa duka zube cikin aljihun wandonsa yace " oh kai ma kana kallan wasan Cricket?"Sosai ma, Khamal suka hango can gefe yana ta waya, mik'ewa sukayi gaba d'aya suka nufe shi, yana ganin su ya ajiye wayar ya mik'a musu hannu yana dariya yace " kaga manya a she nan ma kuna lel'owa?
" Sosai ma kuwa inji Naseer dake murmushi,zama sukayi suka maida hankalin su ga wajen wasan
Ba'a tashi ba sai wajen 11:pm, tare suka fito, sallama sukayiwa juna, kowa ya nufi gida.
Ranar asabar da wuri Khamal ya tafi kallon wasan Poly, yana zama saiga Naseer, shima bai dad'e ba saiga Abdul, kallonsu Abdul yayi yace " wai ku ko'ina kuna nan kmr wasu mayyu ?
"Dariya suka kwashe dashi suka ce " ko kuma muce kai ko'ina kana nan kmr wani magnet?
Gabadaya suka kwashe dariya wannan karon tare da tsansar murna sake ganin junansu da hk kawai kowanensu ke jin dan'uwansa 'cikin zuciyarsa .km a duk sanda zasu hadu suna tsintar kanshi 'cikin farinciki.
Bayan an gama wasan Khamal yace " gaskiya ya kamata musan juna fiyye da haka tunda duk Muna tare da matan mu yakama har su mu had'asu domin zumucinmu ya daure .Murmushi Abdul yayi yace " gaskiya dai ya kamata, Naseer yace " to yanzu tunda unguwar mu d'aya, kamata yayi kowa yaje yaga gidan kowa, inyaso gobe sai mu had'u a gida na, shawarar Naseer aka bi.
Washe gari Abdul da Khamal kowa yazo gidan Naseer da Matar sa da yaran sa, cikin fara'a Zarah ta tari Fateeha da Yasmeen, wanda daman tasan da zuwa agurin mijinta hira sukayi sosai, tamkar sun jima da sanin juna sannan aka zauna a dinning aka ci abinci,yayinda yaran su 'cikin farinciki suke wasa da juna wanda hkn ya faranta ran iyayen .
Tun daga wannan ranar wata irin kwakkywar shak'uwa ma k'arfi ta shiga tsakanin Khamal, Abdul, Naseer haka matayensu da yaran su, sun saba sosai, dan bazaka tab'a tantance yaran su ba, d'an kowa na kowa ne.
Har school d'aya suka maida yaransu domin inganta zumuncinsu kyakykyawar fahimta ce mai k'arfi a tsakanin su, kowa bai da get a gidan kowa.
Khamal ya kalli dubbun manya 'yan jaridan da 'yan gidan TV da sauran masu d'aukar labarai, yace " to kunji farkon yadda muka fara had'uwa, da junanmu har Allah ya dai-daita tsakanin mu, har yau Allah baisa mun tab'a samun sab'ani ko rashin fahimta a tsakanin mu ba, haka ma yaran mu, da matan su.
D'aya daga cikin 'yan jaridan ne yace " Sir to ya akayi kuka had'u da Ammar, Fahad, Zaid?
*MOMYN ZARAH*
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...