'''GADAR ZARE!!!'''
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO**BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
*~(UMMU AMAN)~*25
Wani gigitaccen ihu Abraham ya saki had'i da buga tsalle ya fad'a gadon, Zaid ma a gigice ya nufi Abba, cikin tashin hankali suka shiga jijjiga shi suka kiran "Abba! Abba!! Ido d'aya Abban ya kanne musu had'i da sakar musu murmushi yana rungumo su jikinsa, nannauyar ajiyar zuciya Zaid da Abraham suka sauke suna k'ara shigewa jikin Abba,dariya Abba yayi cikin k'arfin hali ya kalli Abraham yace "ashe dai kana so na, dan gashi ka nuna kafi so na fiye da gadon, ajiyar zuciya Abraham ya k'ara saukewa bai ce komai ba, a hankali Abba ya d'ago su daga jikinsa suna fuskartar juna yace " kun d'auka na amsa kiran mahalicci na ko?
Duk sukayi shiru babu wanda ya amsa saboda jikinsu daya gama mutuwa, murmushi Abba ya kuma yi yace " ban tafi ba tukunna inanan tare daku in sha Allah sai naga 'ya'yanku, duk da dai ita mutuwa tana wuyan kowa haka dukkan mu zaman jiranta muke, a koyaushe tana iya zuwa ta d'auke mu, dan bata kwankwasa k'ofa dan haka ake so ka kyautata alak'arka da mahaliccinka dan akoyaushe kana iya amsa kiransa, a hankali Ammi ta tako har bakin gadon cikin sanyin jiki ta zauna a kusa dashi ta rik'o hannun Abba k'ura masa ido ta kasa magana, murmushi yayi mata yace" yadai? irin wannan kallo haka, ajiyar zuciya ta sauke har a lokacin idonta yana kansa, ganin haka yasa Abba kallon Zaid da Abraham yace " gud 9t my child.
Murmushi dukkan su sukayi sannan suka mik'e had'i dayi musu sallama suka fice, Abba da Ammi suka bi bayan su da kallo, suna fita Ammi ta rik'o hannun Abba cikin nata a hankali Abba yace " ya Allah ka had'e min kan yaran nan, murmushi Ammi tayi had'i da cewa "Amin tana me kwantar da kanta a k'irjinsa yasa hannu ya k'ara rungume ta sosai.
Zaid da wata irin matsananciyar yunwa ya koma gida, yana shiga parlor ya kwanta a kan 3 sitter ya d'aga kansa sama yana kallon celling saboda duk jikinsa a mace yake ya kai 30mnts a haka sannan ya mik'e ya nufi bedroom d'in Teemah kwance ya iske ta tana ta sharar bacci abinta, a ransa yace " inaga ko sallah bata yi ba, bai san sanda yaja dogon tsaki ba ya fice direct d'akinsa ya nufa, yadda ya tafi yabar d'akin haka ya dawo ya same shi, tsaki ya kuma yi, kayan sa cire ya bathroom wanka yayi had'i da d'auko alwala dan har 9:00 bayyi sallar isha'i lotion ya shafa had'i da feshe jikinsa da turare, ya zira jallabiya ya tada sallah, yana idar da sallar yaji yunwarsa ta k'aru, shiru yayi yana tunanin abinda.
Tsaida shawararsa yayi akan yaje part d'in Lubnah, bako tantamar komai ya mik'e ya nufi part d'inta tun daga step yaji wani sihirtaccen k'anshi yana dukan kancinsa, a parlor ya iske ta sanye da gajeran wandon jeans mai kama da pant da wata matsiyaciyar riga wacce da ita gwara babu, a hankali take bin wak'ar Shakira had'i da bin rawar wak'ar, k'amewa Zaid yayi a tsayi yana kallon yadda jikinta ke shaking ga ko bra babu duk yadda ta motsa sai duk ilahirin jikinta ya motsa, wata muguwar sha'awa yaji ta taso masa, take wutar sha'awarta ta fara ruruwa a duk wata gab'a ta jikinsa, take jijiyarsa ta harba yayinda da jikinsa ya d'auki rawa, tako bama tasan da mutum a wajen ba balle tasan halin dayake ciki, wak'ar ce ta k'are dan haka ta tsaya cak da rawarta had'i da juyowa dan ta Lubnah wata, tsaye ta ganshi k'em ya hard'e hannuwansa a k'irjinsa yana kallonta da idanunsa wad'anda suka gama riniwwa.
YOU ARE READING
GADAR ZARE
RomanceA firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu...