27

4.7K 202 0
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
             *~(UMMU AMAN)~*

27

Da k'arfi ya rungume ta a k'irjinsa tare da sakin mahaukacin kuka mai rikitar da ma'abocin sauraro, " i love you Teemah, wallahi ina mugun sanki duk abinda kika ga ina yi miki ina yi ne dan ki gyaru, ke ce rayuwata wallahi koda zan mutu bazan tab'a barin wanda ya kashe ki ya rayu cikin farin cikin rayuwa da walwala ba, ya k'arasa maganar yana k'ara sakin mahaucin kuka, zama police d'in yayi ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallonsa tare da sakin gutun murmushi, yakai 10mnt a haka sannan ya kalli Zaid yace " I arrest you for killing ur wife a razane Zaid ya d'ago kai yana kallon sa, ya kalli yaran sa yace " oya arrest him, da sauri suka nufi Zaid dake rungume da Teemah yana sakin kuka, dakyar suka b'anb'are shi daga jikinta suka saka mishi ankwa tare da tusa k'eyarsa zuwa harabar gidan inda suka yi parking motocinsu,  police d'in ya kuma bada umarnin a fito da gawar Teemah harabar gidan.

Jin magana k'asa-k'asa yasa Lubnah surar zumbulelen hijabinta tayi waje turus Lubnah tayi dan ganin dandazon 'yan sanda a hankali takai idonta inda mijinta ke zaune hannayensa sanye da ankwa yana kuka, cikin sanyi idonta ya sauka akan gawar Teemah dake rufe da farin yadi, da sauri ta k'ara wajen ta durk'usa agaban gawar Teemah tana kuka marar sauti hannunta na rawa tasa bud'e fuskar Teemah da sauri ta kawar da kanta gefe, cikin dakewar zuciya ta mik'e ta nufi inda Zaid yake ta tsaya a gabansa tana kallonshi ido cikin ido cikin kuka ta fara magana " yanzu duk irin hak'urin da muka baka ni da ma'aikatan gidan nan ashe daman baka hak'ura ba.

"sai da ka kashe ta Zaid wacce irin zuciya Allah yayi maka kai wanne irin mutum ne marar yafiya, mai yasa ka kasance mai taurin kan tsira, da k'arfi  taci kwalar rigarsa " haba Zaid mai yasa zaka aikata laifin da kai kanka kasan makomarka wallahi nayi danasanin aurenka nayi nadamar kasancewa ta matarka kai mugu ne azzalumi, mai tayi maka haka dazaka kashe ta a hankali ta sake shi ta zube a gaban k'afafuwansa tana ci gaba da kukan ta "mai yasa Zaid mai yasa kayi haka mai yasa bakayi tunanin halin da Ammi da Abba zasu shiga ba, kasan halin da Abba fa yake ci ta k'asara maganar tana fashe da mahaukacin kuka, cikin rashin fahimta Zaid yake kallan Lubnah ya bud'e baki zayyi magana yaga Baba mai gadi ya rugu da gudu yana salati da sauri Baba mai gadi yace " ya kashe ta ko?

Baba mai aiki ma ta fita daga d'akinta had'i da d'ora hannu aka ta fasa kuka had'i kallon Zaid " kai yanzu yaron nan duk rok'onka da mukayi amma sai da ka kashe ta, Baba mai gadi ya share hawayen dake zubo masa yace " wallahi dama sai da tace bazata koma cikin gidan ba idan ta koma kashe ta zayyi, har nan waje na ta gudu Ya biyo ta wuk'a, sai da muka rok'oshi muka bashi hak'uri ya nuna ya kyale ta, ashe kwanton b'auna yayi, shiru police d'in yayi yana binsu da kallo fuskarshi d'auke da murmushi, Zaid ko komawa yayi kamar mutum mutumi binsu kawai yake da kallo yayinda da mamaki ya gama ciki masa rai da zuciyar sa take yaji tsoro da fargaba sunyi masa dirar mikiya, nan take yaji ya fara zargin kansa, ya shiga tunanin bayan baya biyo Teemah daga d'aki mai ya faru amma ya kasa tunawa, yana cikin wannan mummunan hali yaji police sunce " kai shiga mota had'i da hankad'a shi cikin motar.

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now