74

3.7K 202 3
                                    

'''GADAR ZARE!!!'''

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

           ~NA~

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_
                     

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

'''MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA'''

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
'''ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA'''
             *~(UMMU AMAN)~*




74



Cikin matsanancin kuka yace " please.... sai kuma yayi shiru, ya kasa cewa komai,
sosai Dady ya hasala, cikin b'acin rai Dady ya daka mishi tsawa had'iwa cewa " Mannir karka kuma bari na kuma yin magana,
bai kalli inda Dady yake ba, ya kalli Zarah cikin ido na kamar seconds 15 sannan ya duk'ar da kansa k'asa,
ita dai Zarah shiru tayi tana kallansa batare data ce komai ba, duk ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari,
k'asa da kai Mannir ya k'ara,sannan  cikin rawar muryar yace " nasan duk wad'an nan abubuwan da suke samu na a rayuwa yana da nasaba da abinda nayi miki ne,
na tabbatar iftila'in da suke fad'a min, ni da iyali nasaboda ke ne Zarah,
dan nasan babu wani abu da nayi marar kyau a rayuwata da Allah zai azabtar dani,
azabtarwa mai tsanani face abinda nayi miki, kuma wallahi nasan kad'an na gani, ban ga komai ba,  matuk'ar ban rok'ek'i yafiya ba,
wannan ya tabbatar min da yanzu tun a duniya ake yin hisabi ba sai anje ko'ina ba (lahira),
idan kayi abin alkhairi tun a duniya zaka gani, haka ma idan kayi sharran,
saboda abinda ni kad'ai nayi miki, iyalai na sai had'uwa suke da iftila,
a gaban ido na akayiwa matata da 'yata fyad'e, kuma duk suka d'auki ciki,
Ikram ta haifi shege kamar yadda kema kika haifa,saboda kema 'yar wani ce, kuma matar wani ce, k'anwar wani ce,
yayar wani ce, sannan mahaifiyar wani ce,
sannan daga k'arshe ta mutu kamar yadda na buk'ata akan ki,
tabbas zancen Allah baya tashi dayace " duk wanda yayi ZINA da 'yar wani, sai shima anyi da 'yarsa
idan kuma bashi da 'ya ayi da matarsa,
idan bashi da mata ayi da mahaifiyarsa,
idan bashi da mahaifiya sai anyi da k'anwarsa,
saboda itama wacce yayi da ita matar wani ce, 'yar wani ce, mahaifiyar wani ce, sannan k'anwar wani ce.

Cikin rawar muryar Zainab tace " Mannir me... me.... ka...ke....nu...fi?

Tayi maganar idanta tarrr akansa,
murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo, kai da ganin murmushin kasan na tsananin b'akin ciki ne,
mai cike da tsantsar nadamar rayuwa,
Zainab ta bud'e baki zata kuma yin magana yayi saurin cewa " please Zainab kiyi shiru, har in kai inda nake san na kai, nasan idan nakai inda k'arshen magana ta zaki fahimci abinda nake nufi,
cikin sanyin murya Zainab tace " amma.....  bai bari ta k'arasa ba ya d'aga mata hannu had'i da cewa " please Zainab yau rana ce ta jin kunya a gare ni, rana ce ta wulank'anta!, tozarta sannan ta k'ank'anta,
da in bari naji kunyar lahira, na kuma ci gaba da tsintar abinda na shuka gwara na fad'a koda duk duniya zasu k'i ni,
su kuma juya min baya, Zainab kiyi hak'uri nasan nayi miki laifi mai girman gaske wanda nasan da matuk'ar wuya ki yafe min,
cikin sanyin murya yace " na aikata laifi mai girma, mai matuk'ar munin gaske.

A tsorace Dady yace " what Mannir, me ka aikata haka?

K'ara k'ask'antar da kansa yayi a gaban Zarah yana kuka yace " please Zarah ki dubi girman Allah ki yafe min,
ki tuna ko Allah ma muna yi masa laifi amma ya yafe mana,
Zarah idan baki yafe min ba, wallahi na shiga uku na rink'a ganin bala'i kala-kala kenan har k'arshen rayuwa ta,
cikin tsawa Dady yace " wai uban me ka aikata mata da kake rok'onta yafiya?

GADAR ZAREWhere stories live. Discover now